A shekarar 2024 ce za a yi zaben wanda zai maye gurbin Shugaba Akuffo-Addo mai barin gado. Hoto: AP      

Daga Peter Asare-Nuamah

Da yake bayyana takaicinsa a kan irin wahalar da mutanen Ghana suka shiga a shekarar 2023, Shugaban Kasar Ghana Nana Akufo Addo ya bayyana a ranar 26 ga Agustan 2023 cewa, "Ana shan wahala, na san da hakan, amma ina da yakinin cewa mutanen Ghana za su zabi shugaban da ya dace, wanda zai kai kasar ga mataki na gaba."

Babu shakka, akwai kalubale babba a gaban gwamnatin mai shigowa na daura kasar a tafarkin ci-gaba musamman ta fuskar tattalin arziki.

A shekarar 2019, Bankin Duniya ya bayyana Ghana a matsayin kasar da ta fi samun habakar ci-gaban tattalin arziki.

A shekarar 2019, kudin shiga na Ghana ya kai Dalar Amurka biliyan 68.3, sai ya samu ci-gaba da kashi 2.5% a shekarar 2020, har ya kai Dalar Amurka Biliyan 79.16 a shekarar 2021, wanda ke nuna karin kashi 13.01%. Amma a shekarar 2022, sai aka samu koma-baya da kashi 7.98%.

Abubuwan da suka jawo koma-bayar suna da yawa, amma muhimman su ne: basussukan da ke kan gwamnati, da hauhawar farashi da karyewar darajar kudin kasar da rashin aikin yi da sauran abubuwan da suka yi wa kasar katutu suke jan ta baya.

A yanzu, Ghana tana cikin kasashen da suke da wahalar rayuwa. Annobar Covid-19 da yakin Rasha da Ukraine sun taimaka wajen hana kasar ci gaba, tare da ta'azzara wahalar da 'yan kasar suke fuskanta.

Shugaban Kasa Nana Akuffo Addo ya yi alkawarin inganta rayuwar 'yan kasar. Hoto: AFP

Ririta tattalin arzikin Ghana ne zai taimaka wajen ciyar da kasar gaba. Don haka, masu kada kuri'a a zaben na 2024 suke burin ganin sun zabi shugaba wanda zai iya gyara tattalin arzikin kasar.

Wadanda abin ya fi shafa

Basussukan da ke kan gwamnatin kasar yana ta kara girmama, wanda hakan ya sa ake fargabar ci gaban kasar a yanzu da kuma fargabar halin da za ta shiga nan gaba.

Ma'aikatar Kudi da Tsare-Tsaren Tattalin Arzikin kasar a taronta na rubu'i na uku na shekarar 2022, ta bayyana cewa jimillar basussukan da ke kan kasar Ghana ta kai dalar Amurka biliyan 48.87 (Dala biliyan 28.41 na kasashen waje, da dala biliyan 20.46 na cikin gida), wanda ya kai kusan kashi 75.9% na kudin shiga da kasar ke samu, sannan kuma ya nuna karin kashi 12% daga rubu'i na biyu na shekarar 2022.

Duk da cewa ratar da ke tsakanin basussukan kasar da kudin shigarta na karshen shekarar 2022 bai tsallake ka'idar kashi 77, ya nuna akwai matsala a kan kasar wajen iya biyan basussukan da ke kan ta, ballantana ta samu damar inganta tattalin arzikinta.

Duk da kasar ta samu karin lamunin shekara uku daga Asusun Lamuni na Duniya wato IMF, wajen biyan bashin dala biliyan uku, da kyar aka amince da yarjejeniyar saboda yadda masu ba da bashin suka nuna damuwa kan kalubalen da kasar ke fuskanta wajen iya biyan basussukan.

Amma duk da haka, bayan kasar ta karbi kashin farko na Dala miliyan 600 na kudin a Mayun 2023, har yanzu ba a turo mata kashi na biyun ba wanda ya kamata a ce an bayar a Nuwamban 2023 har zuwa wannan wata ma Disamba.

Kasar tana matukar fama da matsalar hauhawar farashi a bana, musamman bayan karyewar darajar kudin kasar wato Cedi. Hoto: Ghana News Agency

Akwai kuma alamar za a cigaba da jan kafa a bana wajen ba ta sauran kudin saboda fargabar da ake yi na iya biyan basussukan kasar na kasashen waje.

Kasancewar zaben kasar a shekarar 2024 za a yi, rashin samun kudin zai nuna gazawar gwamnati wajen cika alkawarinta na inganta tattalin arzikin kasar, wanda kuma zai iya kawo wa zaben cikas.

Haka kuma Ghana ta fuskanci hauhawar farashi da karyewar darajar kudin kasar a bana.

Hauhawar farashin, wanda bai rasa nasaba da hauhawar farashin makamashi da kayayyakin abinci da kuma karyewar darajar kudin kasar wato Cedi, ya kai kashi 10% a shekarar 2021, amma ya karu zuwa kashi 31.5% a shekarar 2022, sannan aka yi hasashen zai kai kashi 44.7% a karshen wannan shekarar.

Safarar kayayyakin abinci

Yadda kasar ke ta'allaka da shigo da abinci da makamashi daga kasashen waje ya kara nuna cewa hauhawar farashi da karyewar darajar kudin kasar zai matukar girgiza aljuhun 'yan kasar, wanda dole hakan zai shafi farashin kayayyakin bukata a kasar.

Misali, a shekara goma da suka gabata, Ghana ta shigo da shinkafa ta kusan Dala biliyan 8, wanda shi ne abinci na biyu da aka fi amfani da shi a kasar.

Duk da cewa masara ce ta farko, kudin da mutanen Ghana ke kashewa wajen sayan shinkafa ya ninka na masara sau kusan hudu, saboda yawancin shinkafa da ake ci a Ghana shigowa da ita ake yi, sannan karyewar darajar kudin kasar ya shafi farashin.

Hauhawar farashi da tsadar kayayyakin da ake shigo da su a Ghana ya matukar taba sayayyar 'yan kasar, wanda ya kara jefa wasu, musamman talakawa cikin yunwa.

Duk da cewa Bankin Raya Kasashen Afirka ya yi hasashen cewa hauhawar farashi a Ghana zai ragu da kashi 20 a shekarar 2024, nauyin zai koma kan sabuwar gwamnati ne wajen jawo masu zuba jari da habaka masana'antun cikin gida da sauransu.

Hakan zai taimaka wajen rage yadda kasar ke rataya da abubuwan da ake shigowa da su, ya inganta samar da abincin kasar sannan ya taimaka wajen rage hauhawar farashi da daga darajar kudin kasar.

Kamar yadda mujallar Ghanaweb ta nuna a 11 ga Disamban 2023, kididiga daga Darakta Janar na Hukumar Tsara Ci-gaban kasar Dokta Kodjo Mensah-Abrampa ta nuna an samu ragowar talauci a shekara 20 da suka gabata a kasar.

Wata kasuwa a Ghana.

Duk da cewa wannan labari ne mai kyau, amma akwai bukatar a gane cewa yanayin talauci ya karu sosai a Ghana a dan lokacin nan, musamman tun daga lokacin annobar Covid-19.

Inganta bangaren noma

An kiyasta cewa kusan mutum miliyan 2.99 na kasar Ghana suna rayuwa ne a kasa Dala daya a kullum a shekarar 2023, sannan mutanen za su karu idan aka yi amfani da kiyasin masu rayuwa a kasa da Dala biyu kullum.

A shekarar 2022, kusan kashi 27 na mutanen Ghana ne suke fama da talauci, wanda ya nuna karin kusan kashi 2.2 daga shekarar 2021. Idan ana so a magance talauci, wanda ya fi kamari a karkara, dole a inganta hanyoyin samun kudin mutanen na karkara.

Sanannen abu ne cewa noma shi ne ginshikin tattalin arzikin Ghana, kuma tushen arzikin talakawan kasar.

Don haka, akwai alaka babba tsakanin noma da kuma yunkurin rage talaucin kasar. A yanzu da ake shirin zaben na badi, mutanen kasar za su bukaci gwamnati mai shigowa ta yaki talauci da rashin aikin yi sosai.

Zuba jari sosai a bangaren noma da kuma inganta harkokin kasuwancin kayayyakin da ake nomawa a kasar za su taimaka matuka wajen rage talauci da samar da aikin yi a kasar.

Mayar da hankali a kan amfani da kimiyya wajen noma zai kara jawo hankalin matasa zuwa gona, wanda hakan zai rage rashin aikin yi a kasar.

Wani abu da shi ma yake da matukar muhummanci shi ne 'yan siyasar su kuduri aniyar yaki da cin hanci na gaskiya saboda yana cikin manyan matsalolin da kasar ke fuskanta.

Marubucin, Dokta Peter Asare-Nuamah malami ne tsangayar Ci-gaba mai dorewa na Jami'ar Environment and Sustainable Development da ke Ghana, sannan babban mai bincike ne a Cibiyar Binciken Ayyukan Ci-gaba da ke Jami'ar Bonn da ke Jamus.

Togaciya: Ba dole ba ne ya zama ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika