Idan aka samar da kudin bai-daya na ECO za a dinga amfani da shi a kasashen Yammacin Afrika. Hoto: OTHERS

Daga Dwomoh-Doyen Benjamin

Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma(ECOWAS) ta daɗe tana jan ragamar tattalin arziki da hadin kan yankin. Ƙasashe mambobinta suna aiki don cimma manufa ɗaya, ECOWAS tana da damar kawo sauyi ta fuskar ƙarfafa al’ummar yankin Afirka ta Yamma.

Sai dai, jan ƙafar da ake samu a baya-bayan nan da kuma koma baya sun daƙushe tabbatar da muhimman manufofin, kamar irin su samar da kuɗin bai-ɗaya, wato ECO.

Lokaci ya yi da ECOWAS za ta farfaɗo da waɗannan tsare-tsaren tare da ɗaukar matakan gandagarki wajen ciyar da Afirka gaba.

Akwai kyakkyawan fatan cewa kuɗin ECO, wanda aka gabatar don ya maye gurbin kuɗaɗe daban-daban da ake amfani da su a yankin, zai kawo ci gaba sosai da ɗorewar bunƙasar tattalin arziki.

Sai dai kuma, wannan aiki ya dakata saboda wasu damuwa da kalubale da dama. Ya zama wajibi ECOWAS ta sake zage damtse ga wannan shiri, su magance matsalolin da ake fuskanta tare da aiki don tabbatar da nasarar aiwatar da shirin.

Samar da kudin bai daya zai saukaka kasuwanci a tsakanin kasashen Yammacin Afirka, hakan zai janyo masu zuba jari da kawo cigaban tattalin arziki, wanda zai kai ga inganta yanayin rayuwar jama'a a Yammacin Afirka.

Ƙididdiga mai cike da ruɗani

A 2021, kasuwanci a tsakanin kasashen Afirka ya kama kaso 15 cikin 100 na dukkan kasuwancin da ake yi a nahiyar, wanda a 2022 ya karu zuwa kaso 20 sakamakon wasu shirye-shirye irin su Yarjejeniyar Kasuwanci ta AfCTA.

Har yanzu wadannan alkaluman ba su da yawa sosai idan aka kwatanta da suaran yankuna kamar Tarayyar Turai, inda kasuwanci a tsakanin kasashen nahiyar yake kaso 60 na dukkan kasuwancin da suke yi da sauran kasashe.

ECOWAS da ke da kasashe da dama mabambanta, na da wata dama ta musamman don kara yawan wadannan alkaluma, karfafa tattalin arziki da rage talauci.

Cin hanci da rashawa na dakile cigaban tatalin arziki, na kuma sanya shakku kan gaskiyar ma'aikatun gwamnati.

Kudin ECO mai inganci zai habaka kasuancin cikin gida na Yammacin Afirka, sannan kuma zai magance matsalar chanjin kudade.

Domin karfafa kasashe mambobin ECOWAS da ƙarfafa dimokuradiyya, dole Kungiyar ta bayar da fifiko wajen aiwatar da matakan wuri za su tabatar da gaskiya, rikin amana da adalci wajen raba arziki.

Wannan tsari ba cin hanci da rashaw akawai zai rage ba, zai kuma dakile yiwuwar samun rikicin siyasa da na zamantakewa.

Cin hanci da rashawa na dakile cigaban tatalin arziki, na kuma sanya shakku kan gaskiyar ma'aikatun gwamnati. Dole ECOWAS ta dauki kwararan matakai na yaki da cin hanci.

Wani mataki mai muhimmanci game da karfafa gwiwa, shi ne ECOWAS ta samar da wani zabi na tallafin tattalin arziki.

Kasashe mambobi kar su dogara ga kudaden bashi na hukumomin kasa da kasa irin su Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) ko Bankin Duniya.

Ya kamata ECOWAS su samar da hanyar warware matsalolin Afirka, su rage dogaro kan hukumomin kasashen ketare su tabbatar da dogaro da kai.

Tare da dala biliyan 734.8 a ma'aunin GDP, ECOWAS na babbar damar kubutar da mambobinta a lokacin da suka fada matsalar tattalin arziki, maimakon su kyale su a hannun masu bayar da rance na kasa da kasa.

Wannan shiri na kubutar da kasashe da ake baiwa ECOWAS shawarar yi, zai sanya kasashe su sanya idanu sosai wajen hana cin hanci da rashawa wanda kafafen yada labarai suke yawan rawaitowa.

Makoma mai kyau

A 2021, bashin da Afirka ta ci a wajen nahiyar ya kai kusan dala biliyan $644, wanda mafi yawan kudaden bashi ne da suka ranto daga hukumomin kasa da kasa.

ECOWAS na da cikakkiyar damar sauya wannan abu ta hanyar karfafar tattalin arzikin kasashe mambobinta, sannan su rage yawan ciwo bashi daga kasashen waje da suke yi.

Dadin dadawa, ya zama wajibi tallafin tattalin arzikin ya haura na taimakon kudi kawai.

Dole ECOWAS su bayar da fifiko wajen zuba jari a bangarorin ilimi, kula da lafiya da kayan more rayuwa, su tabbatar da kasashe mambobin kungiyar na da dukkan kayan da ake bukata don tabbatar da cigaba mai dorewa, tare da magance matsalolin da 'yan kasashensu ke fuskanta.

A yanzu haka yawancin kasashen Afirka renon Faransa na amfani da kudin bai daya ne na CFA. HOto: OTHERS

Wadannan zuba jari za su kirkiri damarmakin ayyuka, za su yaki rashin aikin yi da talauci, wanda hakan zai kai ga samun Yammacin Afirka mai yalwar arziki da wadata.

Samar da ilimi ingantacce da damarmakin ayyuka ba abu ne da wajibi da za a yi wa jama'a ba, har ma da samar da dabarun da za su kai ga amfana da yawan al'umma.

ECOWAS za ta iya jagorantar zuba jarin gina dan adam da samar da kayayyakin more rayuwa, ta kafa tubalin habakar tattalin arziki da samar da ayyukan yi.

Haka zalika, kari kan shirye-shiryen da ake gani karara, ya wajaba ECOWAS ta yi aiki da sauran gwamnatocin yankuna don saka al'umma a al'amuran yanke hukunci kan manufofin cigaban kasa.

Tarukan kara wa juna san a-kai-a-kai, tuntubar jama'a. da hada hannu da kungiyoyin farar hula zai tabbatar da an saurari kalamai da damuwar jama'a.

Cigaba Mai Karfafar Mutane

Yana da matukar muhimmanci a karfafa gwiwar 'yan kasa su shiga harkokin jagoranci, kuma hakan na taimaka wa wajen dabbaka dimokuradiyya.

Wani bincike da kungiyar 'Afrobaremeter' suka gudanar a 2021 ya gano cewa kaso 71 na 'yan Afirka sun aminta da yakamata shugabanni su zama masu gaskiya da sauraron al'umma.

Ta hanyar shigar da mutane wajen samar da manufofi da tuhumar shugabanni, ECOWAS za ta iya tabbatar da duk wasu tsare-tsare da za a kawo sun dace da bukatun al'ummar Yammacin Afirka.

Masana sun ce idan aka koma kudin bai-daya a kasashen Afirka ta Yamma za a samu daidaituwar harkokin tattalin arziki. Photos: Reuters

ECOWAS na da cikakkiyar damar iya zama tubalin kawo sauyi mai kyau a Yammacin Afirka. Domin cimma wannan manufa, dole ta hanzarta tabbatar da fara amfani a kudin ECO, ta karfafi kasashe mambobinta tare da bayar da fifiko ga daukar matakan kar ta kwana, maimakon matakan magance matsalar da ta afku.

Ta hanyar zuba jari ga jin dadi da walwalar 'yan kasa, dabbaka dimokuradiyya ta gaskiya, da rage cin hanci da rashawa, ECOWAS na iya kirkirar yanki mai arziki, mai zaman lafiya da dogaro da kai.

Yanzu lokaci ne na ECOWAS ta yi jagoranci wajen samar da hanyar da za ta kawo mafita a Yammaci Afirka.

Marubucin wannan makala. Dwomoh-Doyen Benjamin, Daraktan Zartarwa a Cibiyar Masu Samar da Kayayyakin Fasaha ta Afirka.

TRT Afrika