Daga Peter Asare-Nuamah
Dabarun shawo kan sauyin yanayi sun samu karin kulawa a zantukan cigaba a fadin duniya.
Wannan abin yabawa ne ganin cewa a baya, dabarun kula da sauyin yanayi, musamman tsarin hukumar Majalisar Dinkin Duniya na "Framework Convention of Climate Change" da sauran shirye-shirye masu alaka da "Conference of Parties (COP)", sun rinjaya kan sabo, maimakon dakile musabbabinsa.
Yarjejeniyar Paris, wadda aka sanya wa hannu a shekarar 2015, ta share fagen babban canji don daukar mataki kan sauyin yanayi. Yarjejeniyar ta yi amanna kan dabarun sabo da sauyin yanayi da rage mummunan tasirinsa.
Babu shakka, dabarun sabo suna da muhimmanci ga tattalin arziki masu tasowa a yankin Kudancin Duniya, sakamakon cewa suna fuskantar illolin sauyin yanayi, bayan su ba sa haifar da kashi 3% na matsalar ta hanyar iskar gas me illata muhalli.
Sai dai kuma, nahiyar tana fama da mafi munin tasirin sauyin yanayi, kamar ambaliya, matsanancin fari, da yaduwar cutukan tare da hauhawar zafi da ruwan sama mara daidaito. Hakan yakan janyo raguwar amfanin gona da wadatar abinci da talauci.
Inganta kwarewa
A hikimance, dabarun suna da alfanu idan tasirin sauyin yanayi ya karanta a yankunan da ke cikin hadari.
Dabara na nufin sauye-sauye a tsarin dan'adam don takaita mummunan tasirin sauyin yanayi na yayin da ake nemo damarmaki.
Ganin yadda hadarin da kananan manoma ke ciki matsayin noma na kawo cigaba a kasashe masu tasowa na Afrika, da yawan dabarun sun mayar da hankali kan kwarewa tsarin noma.
Sassauya abin noma, da shuka iri mai inganci da tsarin amfani da ruwa cikin tattali, duka misalai ne dabarun da kananan manoma za su dauka.
Sauran fannoni kamar shuka bishiya suna da tasiri a matsayin hanyar dakatar da illa. Wadannan sun zama wajibi don nuna ingancin gudunmowar kasashe masu tasowa don shiga tsarin Majalisar Dinkin Duniya na "Framework Convention on Climate Change (UNFCCC)".
Abin da zai iya haifarwa
Ko da dai yana da alfanu wajen shawo kan sauyin yanayi, masana sun ankarar kan tasirin dabarar mai alaka da irin salon.
Hujjar ta nuna cewa dabarar tana iya karfafa hadarin. Amma ta yaya za a dau mataki kan illar? Dabarun sabon ana shirya su da kaddamar da su da burin magance matsalolin sauiyin yanayi.
Sai dai kuma, abin da zai biyo baya zai iya munana hadarin sauyin yanayi. Ga misali, tashar lantarki ta hasken rana masu girma a Kenya sun inganta damar samun makamashi mai tsafta da rage fitar da iska mai illa.
Amma dai kuma, karbar filayen yin tashar lantarki babba tana hana kananan manoma da mutane 'yar gargajiya samun kasar noma, wanda shi ne madogarar rayuwarsu, kamar yadda kungiyar International Work Group for Indigenous Affairs ta bayyana.
A Ghana, gwamnati tana tallafa wa manoma karkashin shirin Shuka don ABinci da Aikin-yi, don samar musu da magungunanr shuka da sauran kayan noma.
Yayin da manoma suke samun magungunan shuka don inganta amfanin gona, rashin amfani da magani tsakanin manoman karkara yana matukar shafar gurbatar ruwa da kashe kananan halittu na kasa da na ruwa.
Rashin nasarar sabo
Raguwar kananan halittu yana da illa kan albarkar kasa, da amfanin gona, ta yadda yake kara maimaituwar matsalar.
Ganin yadda kokarin yake haifar da tasiri mara inganci, yana da alfanu shirin ya auna dabarun gano munanan tasiri da ka iya samuwa.
Sai dai, wani babban kalubale da ke fuskantar jagorori shi ne nemo hanya mafi kyau ta kaucewa mummunan tasirin. Wannan na faruwa ne saboda tarin munanan tasiri kaddamar da shirin.
Kenan, yana da wahala a ce wata dabara daya ita ce ba ta da tata matsalar ta mummunan tasiri. Haka nan, wasu munann tasirin sukan fito ne a hankali bayan tsawon lokaci.
Wani abin ma da ya fi matsala shi ne al'ummomin yanki suna bukatar canja yanayin muhali da tattalin arzikinsu. A Ghana, ala misali, yawan rashin aikin-yi a karkara ya janyo mutane suna shiga aikin hakar zinare ta haramtacciyar hanya, don su iya tsair da rayuwarsu.
Yayin da hakar zinare ta haramtacciyar hanya yana mumunan tasiri ga muhalli da lafiya. Masu aikin sun fi damuwa da abin da za su samu, ba sa duba illar aikinsu kan ruwa da tsirrai da muhalli gabadaya.
Haka ma manoma da ke mayar da hankali kan inganta amfanin gona ta kowace irin hanya ba tare da la'akari da illar hakan ba.
A kaikaice, tasirin dabarun shi ke nuna kyau ko rashin kan dabara.
Wannan wata matsala ce mai ci wa mahukunta tuwo a kwarya saboda dabarun ana shirya su da farko ne don samara da tasiri mai kyau.
Amm kuma, kamar yadda aka bayyana a dabarun ko rashin alfanunsu ya bambanta. Za a iya karkasa dabarar da ba ta yi nasara ba idan tana da mummunan tasiri ga sauyin yanayi.
Saka-ido a-kai-a-kai
A cewar Field Reckien (2023) wanda ya gwada zabukan fahimtar dabarun, suna iya kunsar juriya ko rashin juriya, wanda ke nufin dabara daya tana iya haifar da tasiri mai kyau da mara kyau.
Reckien ya ce dabarun da ke saka ido kan nau'in abinci ko asararsa, da wadatar abinci, da kayan agaji da mutane, duka suna iya samar da tasiri mai kyau ba tare da babban tasiri mara kyau ba.
Sabanin haka, zabin dabaru masu mayar da hankali kan kayayyakin gabar ruwa, da inshrar dukiya da amfani da ruwa suna iya samar da mafi girman tasiri mara kyau. Sai dai, babu wata dabara daya da ba ta da wani tasiri mara kyau ko kadan ne.
Kenan, ba za a iya kaucewa dabara mara kyau gabadaya ba, amma ana iya rage ta matuka. Kuma a kara wayar da kan mahukunta da cibiyoyin cigaba kan tasirin hakan.
Alhaki yana kan cibiyoyin samar da cigaba, da mahukunta su duba batun dabarun da hanyoyin kaddamar da su, kuam su hada kai da mazauna yanki don shiryawa da saka ido don nazarin tasirin dabarun.
Marubucin, Dr. Peter Asare-Nuamah malami ne a Jami'ar Muhalli da Cigaba mai Dorewa, da ke Ghana; kuma Babban Manazarci ne a Cibiyar Binciken Cigaba, ta Jami'ar Bonn, da ke Jamus.
Togaciya: Fahimta da ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar ra'ayoyi ko fahimta ko tsarin editocin TRT Afrika.