Kyawun Derna, al'amari ne da ya sha yabo da wakoki daga mawakan da makadan ƙasar Libya, lamarin da ake alaƙanta shi da tudu da kwarin tsaunuka na musamman. / Hoto: Reuters

Na shiga matuƙar tashin hankali ganin yadda mahaifata ta birnin Derna ba ta taɓa zama sananniya a duniya duk da irin kyawunta da abubuwan tarihi da take ɗauke da su ba, sai a lokacin da wannan bala'i na ambaliyar ruwa ya same ta, sannan aka san ta a duniya.

Wannan kayataccen birni ya sha daukar hankalin masu kawo ziyara, amma an boye wa sauran al'ummar duniya ƙayatuwarsa tsawon zamani.

Kyawun Derna, al'amari ne da ya sha yabo da wakoki daga mawakan da makadan ƙasar Libya, lamarin da ake alaƙanta shi da tudu da kwarin tsaunuka na musamman.

Bayan haka al'amari ne mai matukar wahalar gaske a samu kutsawa cikin tsunukan da ke kai wa ga Bahar Rum, domin tsaunukan da hamada, na tare ne da lambunan Wadi hade da makwararar ruwan da ke gangarowa daga tsaunuka.

Da yake ana magana ne akan Wadi lambun ni'ima, wannan shi ne tsaunin gabar ruwa ko tundurkin kogin da ya keta ta cikin Derna.

Baya ga wurin da Derna yake a saman tekun, in an kwatanta da garuruwan da ke makwaftka da shi, wadanda suka kera shi har tsawonsu ya kai mita 600, wannan lambun ni'imar gabar ruwa (Wadi) ya sanya Derna ke tattare da hadari.

Wannan lambun ni'ima da ke gabar ruwa na Wadi yana da kananan sassansa har bakwai da ke bubbugowa daga gare shi, kuma su ne tushen ambaliyar.

Tsarin hotunan gine-ginen da gidaje da ambaliyar ta ruguza rugu-rugu. Hoto: Reuters

E, ambaliya ba bakon al'amari ba ne a Derna. Al'amari ne da aka saba da shi daukacin tsawon tarihin wannan birni. Domin har cewa suke yi Jaak El Seil ma'ana abin da ka saba ya zo, harshen mazaunan Derna. Ma'ana dai ambaliya ta zo.

Shawarar ankararwa

Sannan, ta yiwu hujja mafi kyau da ke nuni da muhimmancin ambaliya a wannan birni da aka sha kewarsa a cikin waƙe, wanda wani mawaƙi haifaffen Derna ya wallafa, Mustafa Trabelsi, ba da dadewar nan ba dai ta shahara.

Waƙen ya bazu, yana tashen rera kowace saɗara da ke nuni da wannan mummunar musifa da ambaliya ya haifar tamkar dai ta baibaye al'amuran da za su faru nan ba da dadewa ba a Derna.

Abin takaicin dai shi ne, a wancan lokacin Trabelsi ba mummunar ambaliyar kawai ya hango a wakarsa ba, har ma da mutuwarsa, domin abin bakin ciki ya rasu daren da ambaliyar ta auku.

A wannan daren, da kuma kafin ambaliyar ta share tsakiyar birnin Derna sa'oi kadan, Trabelsi yana musayar sakonni da wani kawuna.

Kawuna ya tuna yadda Trabelsi yake nuna damuwarsa game da madatsun ruwan da suka fashe saboda mamakon ruwan sama. Ya bai wa k\wuna shawarar y\ fice daga gidansa da ke dama da Wadi. Grgadinsa ya isa ya ceci kawuna. Shi kansa Trabelsi, ko da yake ya zauna a gidansa.

Mawaki Dan asalin Derna Mustafa Trabelsi ya hango aukuwar ambaliyar ruwan da ya kawo karshen rayuwarsa. Photo: Reuters

Kananan yara a kan ruwa

Yana zaune ne a wani wuri da ke da dan takin kilomitoci kadan a gabar ruwan Wadi. Ta yiwu bai yi tsammanin cewa ruwan zai isa gidansa ba ne; ta yiwu mutuwarsa ta tabbatar da gaskiyar abin da hasashensa ya hango. Trabelsi ya rasu, amma wakensa na nan tare da mu har a yau, sannan ya ceci kawuna da iyalinsa.

Dan'uwana ya dauki Trabelsi a matsayin mutumin da ya yi sa'a domin bai rayu ba, ballantana ya ga wannan musifar mai tayar da hankali a Derna cikin wannan daren, wanda ya kwatanta da mafi munin ranar halaka.

Dan'uwana ya gane wa idanunsa gawarwaki masu yawa na matasa da tsofaffi, har ma da jarirai, wadanda ke ta yawo akan ruwa. Ya ga motoci da wasu da iyalai a cikinsu, wadanda ruwa ya share su zuwa bakin teku.

Ya tuna tashin hankali da ihun wadanda ambaliyar ruwa ta ci su, amma abin da ya fi tashin hankali shi ne, a cewarsa, wadanda ke ta ihun tuni suka yi shiru bayan da rayuwarsu ta gushe suka mutu.

Ya ga yadda tsakiyar birnin Derna inda ake ta hada-hada aka share shi zuwa cikin teku tun daga saman gini shi da iyalinsa suka samu tsira.

A wannan wajen hada-hadar birnin ne ake da kaburburan sahabban Manzon Allah (SAW) 77 da mabiyansu. A nan ne ake da tarihin shekaru 400 na Derna da ta yi a matsayin wani yanki na birnin Andalus, wato Medina (birni) wanda da ke da muhimmanci, inda wasu daga cikin dangina da abokaina ke zaune a wannan daren.

A tsakiyar birnin Derna, inda ake hada-hadar kasuwanci kan manyan tituna, titin Omar Faiek Shennib (wanda aka ya wa lakabin tsohon Ministan tsaron Libya, dan asalin Derna), a nan daya daga cikin 'yan'uwan yake zaune tare da matarsa da ƴaƴansa biyu.

Mai aikin ceto na saurin kan kayan wasa, yayin da yake laluben gawarwaki a cikin burbushin gine-ginen da suka rushe Hoto: Reuters

Iyali sun halaka

Wani limamin masallaci, dan'uwan ya kwanta da wuri wannan daren, don ya farka da wuri, ya ja sallar asuba. Bayan karfe ukun dare, shi da matarsa sai ruwa ya tashe su, inda suka hango ƴaƴansa na yawo a mace akan ruwa.

Ya yi kokarin finciko daya daga cikin ƴaƴansa don ma ya samu ya binne shi. Sai dai lokacin da yake kokarin jawo daya yarinyar sai igiyar ruwa ta fincike shi. Ganin haka shi da matarsa, suka ga ba su da wani zabin da ya rage illa kawai su nemi hanyar tsira, ko kuma makomarsu ta kasance guda da ta ƴaƴansu.

Ba da nisa ba daga wurin, a kan dai wannan titin, wani abokina Yousif ke zaune, wanda muke tare shekara guda da ta gabata, yayin da muka tafi zuwa Ain al-Dabousiya, wani wajen makwararar ruwa daga kan tsauni kore da ke da nisan kilomita 30 daga Yammacin Derna.

Yousif na zaune da iyalansa, wanda suka dawo kan wannan titin bayan da gidansu na farko ya rushe sanadiyyar yakin da aka yi cikin shekarar 2018. Sun kasance makwaftamu zuri'armu na tsawon zamani.

Abin takaici, gidansu ya baje. Sai dai wannan karon, ya hada har da daukacin su bakwai.

Derna birnin jajircewa ne da ya yi fama da dimbin musifu a tsawon tarihinsa. Hoto: Others

Birnin Jajircewa

Don tattaro yadda fasalin garin yake ba tare da an ambaci mace-mace ba, wannan musifa da ta afka wa Derna ta yi muni har ta kai ga daya bisa hudu (1/4) na birnin ya baje a cikin Tekun Bahar Rum.

Mutane da dama da muka sani halin yanzu ba sa raye.

Warin gawarwaki yanzu ya maye gurbin daddadan kamshin furen Yasmine da ke baibaye iskar garin.

Duk da wannan musifa, lafawar al'amura a Derna yayin da rana ta fito, al'amarin da ake iya hangowa daga Tekun Bahar Rum daga kan duwatsu, har yanzu haka yake.

Mutane da dama da muka sani halin yanzu ba sa raye a Derna. Hoto: Reuters

Ƙwararrun masana sun kiyasta yawan ruwan da ya kwarara a Derna da kimanin kubik mita miliyan 30.

Bayan ruwan saman da ya haifar da barkewar madatsun ruwa, al'amarin da ya kuma haifar da mace-mace da rusa gine-gine.

Wanda ya rubuta wannan maƙala, Yahya Habil, wani ɗan jarida ne mai zaman kansa a Libiya da ke haɗa rahitanni kan al'amuran da suka shafi Afirka. A yanzu yana aki da wata cibiyar bincike a Gabas da Tsakiya.

Togaciya: Mahangar da marubucin ya bayyana a nan ba sa wakiltar ra'ayoyi da mahangar iditocin TRT Afrika ba.

TRT Afrika