Daga Ferdinand Mbonihankuye
Masana muhalli na fargabar cewa gandun dajin Rukoko na Burundi da ya kasance wata matattara ta albarkatun tsirrai fiye da 5,793 da suka kunshi nau’o’i 567, yana fuskantar barazana saboda yadda mutane ke fadada wuraren zama ba bisa ka’ida ba da kuma lalata abubuwa ba kakkautawa.
Bishiyoyin giginya a dajin shakatawa na Rusizi a kusa da Bujumbura, babban birnin kasuwancin Burundi, na jin jiki ta yadda ake sare su don samar wa wata makabarta da sauran abubuwa fili.
Wannan bangare na dajin ya fi fadin kadada 10,600 kuma shi ne bangaren da abin ya fi shafa, musamman saboda iyalai 300 da suka zauna a wurin kuma suka share kadada kimanin 1,000 don noma.
Kusan wannan bishiya ta musamman (giginya) da ake cewa "Urukoko" a yaren yankin ta kusa karewa a kan hanyar zuwa Cibitoke, sakamakon fadada makabartar Mpanda da ake yi.
Masani a kan muhalli Emmanuel Niyoyabikoze ya tuna yadda manomi Jean Marie Nduwimana ya nuna bakin ckinsa game da yadda makabartar ke son kashe bishiyoyin giginya.
"Ba mu da wani zabi sai dai mu fadada share dajin domin samun karin kaburbura," in ji mai haka kaburbura Jean Marie Nduwimana a hirarsa da TRT Afrika, yayin da yake tsaye a kusa da itatuwan bishiyoyin giginyar da aka sare.
A shekarar 2014, hukumomi sun hana kiwon dabbobi a gandun dajin Rukoko, wani matakin da alama ta nuna cewar ya fara taimaka wa bishiyoyi farfadowa, kafin shigar mutane yankin ya sake lalata dukkan cigaban da aka samu.
Barazanar bacewar bishiyoyin giginya
Ba matsugunin mutanen ne kawai yake barazana ga bishiyoyin giginya ba. Aikin kafinta da gine-gine da kuma neman gawayi na taka rawa wajen rage yawan bishiyoyi a gandun daji ga kasar da har yanzu tana cikin kasashe masu muhimmanci a fannin muhalli a duniya.
Idan mutum ya je kasuwannin katako, zai gane iya yawan yadda aka sare bishiyoyi.
Générose Havyarimana, wani dan kasuwa ne da ya bayyana katakon da aka yi daga bishiyoyin giginya da sauran bishiyoyin da suke fuskantar barazanar bacewa a matsayin lu’u-lu’u.
"Baya ga Tanzaniya, ba kasafai ake samun irin wadannan ba saboda bacewar bishiyoyi daga tushensu," in ji Générose a hirarsa da TRT Afirka.
Noma ba tare da sa iyaka ba ma na daya daga cikin matsalolin da ke addabar dajin Rukoko. Fadada yawan noman abinci kamar masara da wake da kuma noman kayayyakin masana’antu kamar rake da auduga na barazana ga nau’in bishiyoyin nan, in ji Emmanuel.
Gonar raken Nahum Barankiriza, mallakar kamfanin kasuwancin Tanganyika a halin yanzu yana kan filin da a da dajin bishiyoyin giginya ne a wajen.
Wata babbar matsala
Haka kuma ana dangantaka bacewar giwa ta karshe shekaru shida da suka wuce da janyo karewar bishiyoyin Urkoko a Burundi.
"Ana ganin cin giginyar da giwaye ke yi ya taka rawa wajen yada yawan bishiyoyin cikin gandun dajin, wanda har yau ana ganin shi ne gida daya tilo na wannan nau’in bishiyar," in ji Emmanuel.
Giwa ta fi cin giginya da aka fi sani da suna Urukoko, wadda ke da kwallayen da ba za su iya narkewa ba. "An samu wadannan kwallayen a cikin kashinsu kuma wadannan kwallayen na samar da sabbin bishiyoyi," kamar yadda Emmanuel ya yi bayani.
Saboda haka, a lokacin da wadannan masu ninka yawan bishiyoyin giginya suka sha wahalar rikice-rikicen da kasar ta yi fama da su tun shekarar 1993, shekarar da aka yi juyin mulkin da ya janyo salwantar rayuka kuma ya saka kasar cikin hargitsi, wannan nau’in bishiyar na daga cikin abubawan da aka rasa sakamakon hakan.
Duk da bambance-bambancen abubuwa da ke cikinsa, wannan yanki mai yawan tsaunuka ya kasance wani wuri mai raunin kiyaye albarkatun dajin da ke da muhimmanci ga al’ummar kauyuka da na birane.
Bayan lalata dajin Rukoko, Emmanuel ya yi gargadin cewar hakan kuma zai yi mummunan tasiri ga muhalli nan gaba, kamar rashin iya kebe hayakin da masana’antu ke fitarwa wanda ke janyo sauyin yanayi da lalata kasa da kuma kwararowar hamada.
Nau’ukan tsirrai, irin su gwangwala (Sinarundinaria alpine), wata bishiya dangin dalbejiya (Entandrophragma excelsum) da kuma wata bishiya mai kama da tinya (Faurea saligna) sun kasance bishiyoyin da ake nema wajen aikin kafinta da kuma kera abubuwa.
An yi amfani da waddannan nau’ukan tsirrai sosai ta yadda ba su wuce ‘yan tsiraru ba a wasu kebabbun gandun dajin irin su wajen shakatawa na Kibira (Kibira National Park) da kuma gandun dajin Bururi (Bururi Forest Reserve).
Masana a kan muhalli sun ce akwai bukatar a farfado da wasu nau’ukan tsire-tsire hudu kwarurrukan Kumoso. Wadannan bishiyoyin sun bace sobada yawan amfani da su.
A halin yanzu wadannan albarkatun suna matukar tsada har ana zuwa Tanzaniya nemansu, lamarin da ka iya zama barazana ta ketare ga wadannan nau’ukan tsire-tsiren.
A halin yanzu nau’ukan tsirrai 40 ne ke fuskanatr barazanar bacewa.
Dasa sabbin tsirrai
Duk da tashin hankalin da sare itatuwa ke jawowa, akwai alamar fata na gari nan gaba. A cikin filin Imbo, wasu nau’ukan tsirrai sun kadaitu a kebabbun wurare.
Masana kan harkar muhalli sun ba da shawara cewar a bi dabarar kare nau’ukan tsirrai a wuraren da ba nasu ba a yankunan muhalli uku na kasar inda mutane suka fi neman tsire-tsiren, musamman ma wadanda suke kan tsaunuka.
Za a samar da lambunan tsirrai uku domin manufa ta kimiyya da kare tsirrai, daya a filin Imbo, daya a tsaunukan da ke tsakanin Kogunan Congo da na Nile, na ukun kuma a kwarurrukan Kumoso, domin farfado da tsirrai kasar da ke fuskantar barazanar bacewa saboda yadda ake amfani da su ba kakkautawa.
Domin samun hanya mai dorewa ta amfani da bishiyoyin katako na kasar Burundi daga nan zuwa lokaci mai nisa, ya zama dole a raba ingantaccen murhu (imbabura) da ba ya cin gawayi sosai, idan ba a samu wani tushen makamashi ba.
Rage sare bishiyoyi a dajin gwamnati da na masu zaman kansu, musamman kananan bishiyoyi, wani mataki ne da za a iya dauka.
Zabi mafi sauki kuma wanda ya fi dacewa shi ne a bayar da kwarin gwiwar dasa bishiyoyi ta yadda za a maye gurbin bishiyoyin da aka rasa.