The US is among world's industrialised countries emitting most greenhouse gasses

Bayan kammala Taron Sauyin Yanayi na Afirka da ya wakana a birnin Nairobi na kasar Kenya, da shirye-shiryen na duniya da za a gudanar a Dubai, sai batun sauyin yanayin duniya da yadda lamarin yake shafar Afrika ya sake dawowa, inda mutane da dama suke ta yin ƙarin haske.

Taron Sauyin Yanayin na Afrika ya bayyana cewa ’yan Afrika sun gane muhimmancin samun hadin kai da murya ɗaya tare da yin tsayuwar daka wajen tabbatar da cewa duniya ta daina yin watsi da buƙatun nahiyar a game da sauyin yanayi.

A yunƙurin da suke yi na tabbatar da an yi wa Afrika adalci, taron ya ƙarƙare ne da yin kira ga shugabannin duniya da su bayar da goyon baya a kan biyan harajin sinadarin carbon a kan kamfanonin sufurin jiragen sama da na sufurin ruwa da albarkatun man fetur.

Haka kuma sun bukaci a yi garambawul kan tsarin kudaden duniya, inda ake tilasta wa kasashen Afrika biyan kudaden ruwa masu yawa idan suna neman karin bashi.

Kamar yadda wani rahoto na masu bincike na Our World in Data project and the Energy for Growth Hub ya bayyana, Afrika ce da alhakin kashi 2.73 kawai na sinadaran da suke gurbata muhalli tun bayan da duniya ta samu ci gaban masana’antu.

A yankin tsibirai masu maƙwabtaka da Somalia wato Somalian Penynsula, kusan shekara hudu kenan ba a yi ruwan sama ba, wanda hakan ya jefa sama da mutum miliyan 23 cikin tsanayin yunwa a kasashen yankin na Habasha da Kenya da Somaliya.

Haka kuma Tafkin Chadi, wanda yake samar da hanyoyin cin abinci ga miliyoyin mutane a kasashe daban-daban kamar su Chadi da Nijar da Nijeria da Kamaru ya ja baya da daya bisa goman girmansa a gomman shekarun da suka gabata.

Ambaliyar da ta auku a 11 ga Satumban bara tana cikin alamun sauyin yanayi. Hoto: AFP

Wadannan biyu ne daga cikin manyan kalubale da nahiyar ke fuskanta saboda sauyin yanayi.

Dole kasashen duniya masu arziki su taimaka wa Afrika da isassun tallafi domin yaki da sauyin yanayi, domin kasashen ne suka haifar da wadannan matsalolin na sauyin yanayi ko dai ta hanyar karfin masana’antu ko ta mulkin mallaka.

Neman tallafin dala biliyan 500

A wani rahoto da wata kungiya mai zaman kanta ta Climate Policy Initiative ya nuna, Nahiyar Afrika ta samu kashi 12 ne kawai na kudaden da take bukata domin magance matsalar sauyin yanayi.

Wannan rashin adalcin ne ya sa nahiyar ta yanke shawarar gudanar da taron na Sauyin Yanayi, sannan ta shirya tsaf domin tafiya taron duniya na COP28 da murya daya da kuma karin bukatu.

Lallai taron COP28 wata dama ce ga Nahiyar Afrika na bayyana bukatunta da kuma sake fito da matsalar da take fuskanta na sauyin yanayi fili.

Kevin Kariuki, Mataimakin Shugaban Bankin Bunkasa Yankin Afrika ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa Nahiyar Afrika za ta bukaci karin tallafi daga Babban Bankin Lamuni na Duniya, inda ake sa ran samun damar amfana da biliyan $500 domin yaki da matsalar sauyin yanayi, wanda za a iya amfana kadan-kadan har kaso biyar.

Nahiyar Afrika na tunanin samun karin kudade domin samun damar yaki da sauyin yanayi ta hanyar amfani da makamashin rana wato makamashin da ake yi sabuntawa, wadanda ba su da illa.

Taron Sauyin Yanayi na Afrika na farko da ya wakana a Afrika a watan Satumba. Hoto: Reuters 

Rashin isassun kudade ya tilasta wa kasashen Afrika yin amfani da makamashi wadanda ba a iya sabuntawa wadanda kuma suke da illa wajen samar da wutar lantarki. Amma duk da hakan, kusan kashi 43 na mutanen nahiyar ba sa samun wutar lantarkin.

Babbar matsalar Afrika wajen yaki da matsalar sauyin yanayi shi ne amfani da albarkatun man fetur da iskar gas da kuma hana wasu mutanen Afrika samun wutar lantarki.

A daidai lokacin da ake kiyasta cewa a shekarar 2050 mutanen Afrika za su ninku, sai girman lamarin ya kara fitowa fili. Abin da hakan ke nufi shi ne manyan kasashen duniya ba su da wani zabi face su tabbatar sun fitar da isassun kudade domin yaki da matsalar ta sauyin yanayi a Afrika.

Wannan na nufin ba kasashen Afrika kudade domin su inganta bangaren makamashi mara illa.

Rashin adalcin zai iya zama dan aike

Kasancewar an riga an tabbatar da hakan, sai kasashen Afrika sun riga sun daura damarar neman wasu hanyoyin daukar nauyin fara yaki da matsalar. Wannan ya sa wasu kasashen nahiyar suka fara sayar da damar fitar da sinadarin carbon domin rage shi.

Kasar Kenya, wadda ta dauki nauyin shirya Taron Sauyin Yanayi na Afrika na farko ce kan gaba a wannan dokar, sannan take da burin fitar da wani tsari da zai sauya yanayin kasuwancin Afrika.

A watan Yuni, kasar ta shirya wani taron, inda kasar Saudiyya ta saya damar fitar da tan miliyan 2.2 na sinadarin carbon a kasar.

Don haka, babban burin nahiyar a taron na COP28 shi ne samun isassun kudaden da take bukata domin inganta bangaren makamashi mara illa.

Sai dai abin takaicin shi ne da wahalar gaske wannan rashin adalcin da ake yi wa Afrika ya kawo karshe a taron na COP28.

Amma duk da haka, yana da kyau a fahimci cewa rashin adalcin da ake yi Afrika zai iya zama dan aike, domin zai shafi duniyar baki daya ne a nan gaba.

Marubucin, Yahya Habil dan jarida ne mai zaman kana shi da kasar Laberiya da ya fi mayar da hankali a kan harkokin Afrika. Yanzu haka yana aiki da wata kungiyar kwararru a yankin Larabawa.

Togaciya: ra’ayin marubucin ba dole ba ne ya zama ya yi daidai da ra’ayi da ka’idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika