Laftanal Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba ne ya yi mulkin sama da watanni takwas a matsayin shugaban Burkina Faso. Ya kwaci mulki ta hanyar juyin mulki ga Shugaba Roch Marc Kabore a ranar 24 ga Janaitun 2022, kuma shi ma aka kore shi daga mulkin a ranar 2 ga Oktoba inda Kyaptin Ibrahim Traore ya maye gurbinsa.
Juyin mulki biyu a kasa da shekara guda. Shugabannin kasa goma a cikin shekaru 62 na samun ‘yancin kai, wadanda mafi yawansu sojoji ne! Hakan zai sanya a ce Burkina Faso na shan wahala rashin zaman lafiya a siyasance. Ta yaya za a fahimci yanayin da ake ciki?
Aiyukan ta’addanci da kura-kuran sojoji
A tashin farko, mutum zai iya tambayar ko dalilan da suka samar da rikici ne suka samar da tasiri a Burkina Faso.
Domin kare juyin mulkin da ya yi a ranar 24 ga Janairun 2022 da kifar da gwamnatin Roch Marc Christian Kabore, Laftanal Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba ya bayyana irin gazawar shugaban wajen dakatar da hare-haren ‘yan ta’adda daga kasar Mali mai makotaka da su.
Wannan ne dalilin da shi ma Ibrahim Traore ya bayar a lokacin da ya hambarar da gwamnatin Damiba a ranar 2 gq Oktobn 2022.
Wani batu da dan jaridar Burkina Faso, Lamine Nourridine Konkobo ya mayarwa martani shi ne, wani rubutun zube na Aquino d’Sassa da yake cewa “Roch Marc christian Kabore, shugaban kasa na farar hula, idan aka zo batun dabarun yaki da ‘yan ta’adda, ba ya aiki da kwarewar sojojinsa.”
“Kuma yadda wadannan sojoji da suke yin rashin nasara a fagen daga yayin fuskantar ‘yan ta’adda --- suka shiga fadar gwamnati, suna ganin su za su iya magance ‘yan ta’addar, abu ne kawai na sumbatun kurma”.
An yi amfani da abubuwa da dama, rashin kayan aiki da kwarewa ne suke ci gaba da tabarbarar da yakin da sojojin Burkina Faso ke yi da ‘yan ta’adda. Tsohon Shugaban Kasar Kabore ya kaddamar da wani rahoto don fahimtar Inata, inda aka kashe a kalla sojoji 50 bayan wani hari da ‘yan ta’adda suka kai musu a ranar 4 ga Nuwamban 2021. ya kamata a ce wannan rahoto ya bayyana gazawar sojoji a wurare da dama.
Abun takaici, juyin mulkin 24 ga Janairu ya boye tare da kin fitar da rahoton da aka dade ana saurare, wand da an fitar da shi zai kunyaa sojojin Burkina Faso a idon jama’ar kasa.
Amma kuma kwararru na bayyana cewa “rashin kayan aiki; rashin na’Urori da motocin yaki” ne babbar matsalar sojojin Burkina Faso.
Dadin dadawa, dan jarida a Burkina Faso dake Ouagadougou (Da za a bayyana da Jule don kare shi) ya bayyana cewa, “sojojin sun rabu zuwa gida-gida. Shugabannin sojoji da na kasa da su ba sa magana da yare daya.
Hakan na bayyana, ya kamata a kalli rushewar gwamnatin tsohon Shugaban kasa Blaise Compaore, wanda aka hambarar a 2014, ya raunata rundumar soji da tsarin tsaron kasar. An so sojoji su kare gwamnati tare da hana ta rushewa. Ba wai ta kare jama’ar kasar ba. Hakan na nufin sojojin da ya kamata su kare jamhuriya, sai ya zama su ma sun rarrabu wanda hakan ke durkusar da kasar.
Hukumomi masu sakaci da hidimtawa daidaikun mutane
“Kundin tsarin mulki da dokoki ba su da wani amfani; cin hanci, tsana da gaba, da jan hankali ga samun dukiya a saukake, duk sun bazu a tsakanin al’uma, kamar yadda Lamine Nourridine Konkobo ya bayyana. A Burkina Faso, akwai a kalla bangarori uku a yau: Magoya bayan Compaore, maboya bayan Kabore, da kuma masu ganin sojoji za su warware matsalolin kasar. Kowanne bangare na yiwa dayan mummunan fata da zarar ya shiga fadar gwamnati ta Kosyam. Adawa, girman kai da bcin rai mara misaltuwa dake janyo hayaniya sun zama ba komai ba a yau --- Paul-Henri Damiba ya koyi hakan da wahala.
“Manyan laifukan” Paul-Henri Damiba guda biyu
Batun saukin da ya sanya Paul-Henri Damiba kwace mulki kuma aka zauna kalau shi ne, alkawarin kawo karshen ta’addanci a Burkina Faso.
Ya tasirantu da karfin ikon wasu ‘yan siyasa da suka raine shi, sai nan da nan ya sauka daga kan kayinsa. “Mun ga yadda ya mayar da kai wajen sauya fasalin gudanarwa, da sasanta jama’ar Burkina Faso.”, inji Jules yana mai bayyana takaicinsa.
“Ya rufe kansa a ciki, ya ki sauraren sojoji abokanansa kan yadda tsaro ke tabarbarewa. Hawan Damiba mulki bai hana aiyukan ta’addanci ci gaba ba. Masu jihadi sun mamaye kaso 40 na kasar a yanu haka --- garuruwa irin su Nouna, Solenzo da Goro sun fada hannunsu.”
Wannan wani yanayi ne da ya bakantawa wasu sojoji kamar su Kyaotin Ibrhim Traore wanda ya so ya gana da shugaban kasa amma abun ya ci tura.
Sama da haka, da yawa daga ‘yan Burkina Fas da suka hada da sojoji ba su marabci karbar da aka yi wa Blaise Compaore ba, wanda aka kora daga kasar sakamakon zanga-zangar da aka gudanar, wanda tun wancan lokacin yake gudun hijira a Ivroy Coast. A watan Afrilun 2022 aka yankewa masa hukuncin daurin rai da rai, saboda rawar da ya taka wajen kisan gilla ga Thomas Sankara a ranar 15 ga Oktoban 1987, kuma da yawa sun kalli ziyarar tasa a matsayin “yafiya”, “banzatar da tunawa da Sankara” da “goyon bayan masu laifi”.
Sauyawar shafin…..
Burkina Faso na bukatar taimako da goyon bayan ECOWAS don karfafa hukumominta; tana bukatar kasashen duniya su tallafi rundunar sojinta; sama da haka kuma, tana bukatar ‘yan kasa da suke da ilimi.
Marubuci Wquaino dSassa ya karkare da cewa “Babu wanda zai iya ciyar da kasa gaba ko jagorantar ta da samun juyin mulki a jejjere: abun da ake bukatar shi ne kundin tsarin mulki da kowa zai girmama, sojoji da za su mayar da hankali wajen kare iyakokin jamhuriya, da ma’aikata da ba za a zalunta ba. Saboda baya ga duk haka, yanayin da muke ciki na wakiltar kwakwalenmu da suke bukatar sake ginuwa.”