Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce har yanzu cutar korona tana cikin ajin cututtuka masu barazana ga duniya, duk da cewa ba ta cikin cututtuka masu bukatar agajin gaggawa. / Hoto: TRT World

Daga Toby Green

Kafofin yada labarai a duniya sun samu labarin sabon "nau'in cutar korona" a makon da ya wuce. Ana kiran sabon nau'in da sunan "ERIS" kuma nau'in da ya kamata a "mayar da hankali a kai", kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana a ranar 17 ga watan Agusta.

Washegari, Shugaban Hukumar WHO Dokta Tedros Ghebreyesus ya ce "har yanzu cutar korona tana cikin ajin cututtuka masu barazana ga duniya, duk da cewa ba ta cikin cututtuka masu bukatar agajin gaggawa".

Yawanci an mayar da hankali ne a kan Kasashen Yamma. Rahotanni daga Cibiyar da ke Kula da Cututtuka Masu Yaduwa a Amurka ta ce nau'in korona na ERIS shi ne kaso 17 cikin 100 na sabbin masu kamuwa da korona.

Wasu masana kimiyya a Amurka sun nuna damuwa kan cewa sabon nau'in cutar yana kama da sauran nau'uka na baya.

Kafofin yada labarai a duniya sun samu labarin sabon "nau'in cutar korona" a makon da ya wuce. Hoto: AFP

Wani masanin cututtuka masu yaduwa nau'in Virus ya ce "sabon nau'in yana kama da nau'in Omicron da aka taba samu a baya".

Duk da haka manyan kafafen yada labarai sun ruwaito masana kimiyya na cewa suna da kwarin gwiwa cewa riga-kafin korona da aka bunkasa zai isa kasuwa kuma zai magance sabon nau'in koronar.

Kamar yadda wani kan labari na kafar yada labarai ta CBS ya bayyana "An samu kaso 60 cikin 100 na wadanda ake kwantarwa a asibiti yayin da sabon riga-kafin korona yake gab da isa kasuwa".

Tsari na daban

Har sai bayan Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Amurka (FDA) ta amince da riga-kafin, jaridar Arizona Family ta yi gargadin cewa "mu rika wanke hannu da rufe bakinmu yayin tari [da kuma] bayar da tazara".

Ko da yake wata mujallar kiwon lafiya ta Birtaniya ta wallafa wani labari a makon jiya mai taken "Hukumar FDA ta amince da riga-kafi wacce ba ta nuna wani alfanu ba, amma kuma ta kara hadarin mutuwa", batun nau'in korona na ERIS da maganar samar da sabon riga-kafi ya jawo suka daga wasu bangarori.

A Afirka, yawanci kafafen yada labarai ba su mayar da hankali kan batun ba – ban da a kasar Afirka ta Kudu. Hoto: Getty Images

Duka wannan abubuwa ne da aka saba gani. Ita kuma jaridar Guardian ta shaida wa jama'a cewa "sabon nau'in koronar yana nuni ne da cewa har yanzu annobar korona ba ta tafi ba", kafafen yada labaran Amurka kamar CNN sun nuna damuwa kan wani sabon nazari da ke cewa hannun da aka yi wa mutum riga-kafi yana tasiri kan garkuwar jiki. Amma sauran sassan duniya, abin ba haka ba ne.

A Afirka, yawanci kafafen yada labarai ba su mayar da hankali kan batun ba – ban da a kasar Afirka ta Kudu, saboda a can an samu wasu labarai kan batun kamar yadda aka gani a Amurka, inda suke cewa sabon nau'in cutar ya bulla kuma ake bayar da shawarar riga-kafi a matsayin mafita ga sabuwar nau'in cutar.

Matakai masu cutarwa

Ganin yadda labarin bai karade ko ina ba a nahiyar, hakan yana nuna yadda wannan ya bambanta da yadda aka gani na korona a duniya.

Afirka ta Kudu abin dubawa ce a nan. Kasar ta dauki tsauraran dokokin kulle da matakan takaita yaduwar cutar fiye da ko ina a nahiyar. Duk da haka ita ce kasar da mutanen da suka mutu sanadin korona ya kai kaso 40 cikin 100 adadi mai yawa a nahiyar Afirka.

Ganin yadda labarin bai karade ko ina ba a nahiyar, hakan yana nuna yadda wannan ya bambanta da yadda aka gani na korona a duniya. Hoto AP

Wasu masana suna ganin tsauraran matakan kullen suna da alaka da alkaluman korona: a tsarin zamantakewa a Afirka, rabin iyalai da ke zaune a birane suna rayuwa ne a daki daya, wadda dokar takaita zirga-zirga da dokar kulle ta kara ta'azzara matsalar.

Wannan manuniya ce kan yadda matakan kare yaduwar korona suka kasance a Afirka. A ranar 17 ga watan Afrilun shekarar 2020, wasu masana daga nahiyar Afirka suka sanya hannu kan wata budaddiyar wasika zuwa ga shugabanni a Afirka, inda suke cewa: "Daukar matakan takaita yaduwar cutar a kasashen arewaci – ba tare da la'akari da abubuwan da ke kasa ba – galibin kasashen Afirka sun dauki tsauraran matakai kan mutanensu…"

"A dauka wadannan matakan ba su shafi matsakaitan mutane ba wadanda ba sa rayuwa a wurare masu cinkoso, ga wasu da suke da zabin yin aiki daga gida. Saboda haka matakan sun takura mutanen da rayuwarsu ta dogara ne kan kananan sana'o'i."

"Shekaru uku da suka wuce sun sa wannan tsoron ya zama martanin da ya dace ga wannan annobar. Matsakaiciyar shekara a tsakanin al'ummar Afirka ita ce shekara 19, saboda haka da wuya Afirka ta galabaita sosai daga cutar korona.

Tasirin kullen korona

Wannan yana nufin kenan tsare-tsaren Hukumar Bayar da Lamuni ta Duniya (IMF) da Bankin Duniya na bayar da bashi da tsuke bakin aljihu yana gab da dawowa.

A daidai wannan lokacin, ana ci gaba da samun gibi a shirye-shiryen Hukumar WHO na yaki da manyan cututtuka a kasashe matalauta da matsakaitan kasashe. Hoto: Reuters

Tasirin hakan a kan harkokin yau da kullum da ba su da tsari a hukumance zai karu sosai. Dakatar da harkokin sufuri da rufe makaranta ya jawo rashin daidaiton jinsi da matsalar karancin abinci, saboda haka ya dace shugabanni su sake nazarin dokokin kullen da aka yi a duniya a nan gaba.

Wannan yana da muhimmanci sosai saboda yadda yanzu korona take kara fadada a fannin kiwon lafiyar duniya.

Shugaban Amurka Joe Biden yana shirin kaddamar da sabon tsarin tunkarar annoba a fadin duniya, ta yadda za a iya samar da riga-kafi don yaki da sabbin cututtuka cikin hanzari "a nan gaba".

Wannan yana cikin wani bangare na aikin jin kai ta hanyar amfani da fasahar zamani wajen magance kalubalen kiwon lafiya a nan gaba.

Fuskoki biyu

Sauya tsare-tsaren ya yi daidai da lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) take sauya yadda take kashe kudinta.

A bara, Hukumar WHO ta samar da wani asusun yaki da annoba wanda zai rika ajiye dala biliyan 10 a duk shekara, inda yake bukatar matalautan kasashe da matsakaita da su bayar da gudunmuwarsu don zama cikin shiri tunkarar annoba.

A daidai wannan lokacin, ana ci gaba da samun gibi a shirye-shiryen Hukumar WHO na yaki da manyan cututtuka a kasashe matalauta da matsakaitan kasashe.

An samu karuwar gibi a kudin yaki da Maleriya da dala biliyan 2.6 a shekarar 2019 zuwa dala biliyan 3.8 a shekarar 2021, yayin da kashe kudi a kan cutar Tarin Fuka ya ragu daga dala biliyan 6 a shekarar 2019 zuwa dala biliyan 5.5 a shekarar 2021 (raguwa da kaso 20 cikin 100 kenan).

Yayin da yanzu Hukumar WHO take kashe kudi a fannin fasahar kiwon lafiya kuma ta rage kashe kudi wajen yaki da cututtuka da ke jawo asarar rai sosai, ba abin mamaki ba ne a ce kafafen yada labaran Afirka ba su mayar da hankali a kan nau'in korona na ERIS ba.

Wannan zai iya zama wani mataki ne da aka dauke shi a makare.

Marubucin Toby Green malami ne a Jami'ar King’s College London a kasar Birtaniya.

A kula: Wannan makala ta kunshi ra'ayin marubucin ne, amma ba ra'ayin kafar yada labarai ta TRT Afrika ba.

TRT Afrika