Ratna Pathak Shah (H) and Naseeruddin Shah (TS) waɗanda hotonsu ke sama da aka ɗauka a Bukin Baje Kolin Finafinai na Cannes a watan Mayu 2024, misalai ne guda biyu na jaruman finafinan Indiya da dama da suka saka hannu a kan wata sanarwa da ke kiran a soke bukin baje kolin nuna finafinan isra'ila yayin da ake tsaka da kisan kiyashi a Gaza.(Reuters/Stephane Mahe) Reuters      

Wata alama ta fata. Haka mutane da yawa ke kallon soke wani bukin baje kolin fina-finai na Isra'ila a nan gida.

An shirya gudanar da bukin ne a Ɗakin Ajiye Kayan Tarihin Finafinan Indiya na Ƙasa da ke Mumbai tun da farko a wannan watan, amma Hukumar Bunƙasa Finafinan Ta Ƙasa Ta Indiya (NFDC) ta soke shi saboda suka daga jama'a.

An fitar da wata sanarwar haɗin gwiwa ta taurarin finafinai, da daraktoci, da masu rajin kare haƙƙin bil adama da kuma al'ummar ƙasa sama da mutane 1,000, waɗanda suka nuna adawa da shirya bukin baje kolin finafinai na Isra'ilan, yayin da kisan kiyashin a Gaza ke ci gaba yanzu watannin 11, inda ska kashe mutum 40,000 - har da ƙananan yara sama da 15,000.

Fitattu daga waɗanda suka rattaba hannun har da jaruman finafinan Indiya Nasiruddin Shah da Ratna Pathak Shah, da mai shirya finafinai na zahirin rayuwa Anand Patwardhan, da lauya mai kare haƙƙin bil adama,Mihir Dasai.

A sanarwar, sun ce, ba ko kunya ana gudanar da bukin lokacin da ɗaukacin duniya ke kallon laifukan yaƙi da Isra'ila ke aikatawa (a Gaza)... kisan kiyashin da ake aiwatar kai tsaye, kuma duniya gabaɗayanta na kallon wannan tsagwaron rashin imanin, kamar yadda muke gani a cikin wayoyinmu da akwatinan talabijin.

Me ma ya sa NFDC za ta shirya irin wannan bukin tallata isra'ila, a lokacin da kan duniya ya rabu gida biyu game da batun Falasɗinu, yayin da Falasdinawa ke fuskantar laifuffukan yaki mafi muni?

Amsa mafi sauƙi ita ce saboda da hukuma ce da ke samun goyon bayan gwamnati. Kuma idan aka yi la'akari da ƙarfafa hulɗa tsakanin Indiya da Isra'ila, abu makamancin wannan zai zo daidai da manufofin gwamnatinmu.

A shekarun baya bayan nan, Indiya da Isra'ila sun zama ƙawayen juna masu karfi ta fuskar tattalin arziƙi.

Suna cinikin makamai tun watan Oktoba, Indiya ta amince ta aika da dubban ma'aikata zuwa Isra'ila domin cike giɓin ƙarancin ƴan ƙwadago da suke da shi.

Amma matakin da da NFDC ta yanke na karɓar baƙuntar bukin baje kolin finafinan Isra'ila ya zarci ƙawancen tattalin arziƙi tsakanin Indiya da Isra'ila.

Domin mu yi masa kyakkyawar fahimta, akwai buƙatar mu ƙara sanin sarƙaƙiyar da ke tattare da hukumar finafinan da gwamnati ke tafiyarwa.

Waiwaye

An kafa NFDC da wacce ta gabace ta Hukumar Ɗaukar Nauyin Finafinan (FFC) domin tallafawa silima mai zaman kanta da ke yin suka ga al'umma, al'ada da kuma zama wata kafar kawo sauyi.

Amma hukumar, har wa yau, an ɗora mata alhakin bibiyar siyasar lokacin, ta hanyar bayyana nasarorin gwamnati ko kuma wani lokacin, nema wa shugabannin siyasa mutunci a idon duniya, kamar tsohuwar firaministan Indira Gandhi.

Misali dangane da wannan shi ne fim ɗin 1976, Manthan ko The Churning, game da sauyi a masana'antar madara a Indiya.

Ya bayyana siyasar cigaba ta mahangar gurguzu, da ta yi nuni sosai da nasarar shirye shiryen gwamnati.

A wajen Gandhi, fim ɗin wata dama ce ta wanke kai, samun ƙarin tagomashi a idon jama'a yayin da ta dakatar da dokar ta ɓacin a 1977.

Neman tagomashin ya ci gaba lokacin da Gandhi ta dawo karagar mulki a matsayin Firaminista a 1980, kuma ta umurci gwamnati, ta hannun NFDC, ta bayar da dala miliyan $6.5 domin taimakawa a ɗau nauyin fim ɗin tarihin Gandhi da aka kashe dala miliyan $22 wajen shirya shi, inji masaniyar tarihi Rochanna Majumdar.

"Ba a taɓa samun gwamnatin Indiya ta biya irin wannan maƙudan kuɗin kan fim ɗaya kacal ba", Majumdar ta ƙara da cewa a littafinta, Art Cinema and India's Forgotten Futures - Film and History in the Postcolony.

"Financing Gandhi, sanannen fim a duniya da ya ƙunshi jarumai na ƙasa da ƙasa da kuma shauƙi na jarunta, wani yunƙuri ne na gyara wasu illoli da dokar ta ɓacin nan ta haifar".

Babu buƙatar a ce neman tagomashin siyasa na da nasaba da irin waɗannan matakan kuma NFDC ta yi amanna da hakan.

A wannan mahangar, shirya bukin baje kolin finafinan isra'ila a ƙarshen mako bai zamo banbaraƙwai ba - hasali ma, NFDC a ko da yaushe tana shiga sabgar siyasa, amma a fakaice.

Abin sha'awa shi ne caccakar da ta sha ta zo ne daga wajen farar hula a wannan mawuyacin lokacin, abin da ya tilasta mata har ta soke bukin.

Amma Indiya ba a ko da yaushe ne take mai goyon bayan Isra'ila ba. Indiya - mai goyon bayan Falasɗinu ce ta farko-farko

Kafin ziyarar Firaminista Narendra Modi mai cike da tarihi zuwa isra'ila 2017 ba, indiya ta kasance mai goyon bayan gwagwarmayar Falasɗinawa tun asali kuma a tarihance.

Firaministan Indiya Narendra Modi,(H) ya ziyarci firaministan isra'ila Benjamin Netanyahu (D) a watan Juli 2017, inda ƙasashen biyu suka saka hannu kan jerin yarjeniyoyin kasuwanci.(AP Photo/Sebastian Scheiner)

Jawaharlal Nehru, da jimawa kafin ya zama firaministan Indiya, ya taɓa faɗi a 1936 cewa,"Matsalar Falasɗinu ta kishin ƙasa ce - mutane da ke fafutikar samun ƴancin kai daga hannun ƴan mulkin mallaka da ci da gumin mutane... ba na launin fata ko addini ba ne".

Mahatma Gandhi, jagoran ƴan gwagwarmaya ya na da ra'ayinsa kan Falasɗinu, "Palastinu ta Larabawa ce kamar yadda Ingila ta ƴan Ingila da kuma Faransa ta faransawa ce."

Waɗannan tunaninnikan su suka share hanyar dangantakar Indiya da Falasɗinu.

Yayin da gwagwarmayar neman ƴancinkan Indiya daga wajen ƴan mulkin mallaka na Birtaniya ta yi ƙamari a shekarar 1940, matsayinta a kan Falasɗinu a siyasance sai ƙara ƙarfi kawai yake yi.

Yayin shigar Indiya Majalisar Ɗinkin Duniya a 1949, Nehru ya kaɗa ƙuri'ar ƙin amincewa da karkasa Falasɗinu da Isra'ila. Har zuwa zamanin Indira Gandhi (1966-1977).

Ta ci gaba da bayyana matsayin nuna goyon bayan ƙasar kuma ita ce shugabar ƙasa ta farko da ta yadda da kungiyar neman ƴancin Falasɗinu ta PLO 1974. Har wa yau,ta mayar da ofishin PLO zuwa ofishin jakadanci a New Delhi sannan ta ba shi duk kayayyakin diflomasiyyar da kowane ofishin jakadanci ke da su.

Shugaban PLO Yaser Arafat ya ziyarci Indiya fiye da sau ɗaya zamanin mulkin indira Gandhi. Arafat mai murmushi kodayaushe sanye da ihirami mai launin baƙi da fari, wanda ya sakko ya kwanta kafaɗarsa, da kuma firaministar sanye da kyakkyawar saree ana nuna su a kafofin watsa labarai na ƙasa a duk lokacin da shugabannin suka haɗu.

A 1981, Indiya ta fitar da wani hatimi tunawa na rupee ɗaya ɗauke da ɗan ƙaramin hoton tutocin Indiya da Falasɗinu.

A 1983, shekara ɗaya kafin a kashe Gandhi, Indiya ta karɓi baƙuncin babban taron ƙasashen ƴan ba ruwanmu inda ta ƙara nanata goyon bayanta ga Falasɗinu.

Matsayar Gandhi game da Falasɗinu abu ne da aka yi tunani mai zurfi s kansa a matsayin manufar ƙasashen waje, amma kuma ya nuna cewa cigaba da manufar Nehru ta gurguzu wacce ba ruwanta da addini.

Wannan cigaba da goyon bayan Falasɗinu za a iya ganin shi yau a tsakanin wasu ƴan majalisar dokokin Indiya. A makon Jiya,wata tawaga daga Santanbul ta ziyarce su da fatan karfafa gwamnatin Modi ta sauya matsayarta game da mamayar da Isra'ila ke yi.

Abokin Isra'ila

Matsayin manufofin Indiya na goyon bayan Larabawa ya sauya bayan ta ƙulla hulɗar diflomasiyya da Isra'ila a 1992, ta hanyar buɗe ofishin jakadanci a Tel Aviv.

A lokacin, gwamnatin firaminista Narasimha Rao ta ƙulla wannan alaƙar ce saboda damuwa da suka yi tarayya a kai game da barazanar tsaro, da ta'addaci da kuma muradu na bai-ɗaya kamar ilimi da yawon shakatawa.

A wannan shekarar, aƙidar tsattsauran ra'ayi ƙaruwa a gida zai samu nasararsa ta farko, yayin da a watan Disamba, wani gungun mutane suka rushe masallacin Babri mai cike da tarihi.

Bayan rushe masallacin Babri, fitattun kamfanonin shirya finafinai a Indiya sun duƙufa wajen gina finafinansu kan labaran kishin ƙasa da ba gaskiya ba ne bisa tarihi kamar Bombay (1995) da Sarfarosh (1999), da kuma Refugee (2000).

A shekarun goma masu zuwa nan gaba, dangantakar Indiya da Isra'ila ta ƙara ƙarfi inda Isra'ila ta bai wa Indiya albarusai a yaƙin Karfin - ɗan ƙaramin yaƙi tsakanin Indiya da Pakistan da aka gudanar daga watannin Mayu zuwa Juli na shekarar 1999, a gundumar kargil ta cikin yanki Jammu da Kashmir, kusa da kan iyaka (LoC).

Bayan rushe masallacin Babri, fitattun kamfanonin shirya finafinai a Indiya sun duƙufa wajen gina finafinansu kan labaran kishin ƙasa da ba gaskiya ba ne bisa tarihi kamar Bombay (1995) da Sarfarosh (1999), da kuma Refugee (2000).

Amma NFDC ta ci gaba da yin fim da sanensu, abin da masaniyar tarihi Majumdar ta kira finafinai masu kyau waɗanda babban hadafinsu shi ne ɗaukaka al'ummar Indiya."

Riba kafin sanin ya kamata amma tasirin finafinan sai raguwa yake daɗa yi, da ci gaba da yin nisa daga asalin ƙudurin d aka yi domin shi saboda sauye sauyen siyasa. Saboda haka Indiya ta fito idon duniya.

Finafinan da hukumar ta tallafawa kamar Down (1974) labarin wasu iyalai masu matsakaicin ƙarfi dake fama da matsala, da Garam Hawa (1977) wani labarin abin da ya biyo bayan rabuwar Indiya da Pakistan, da Anatarjali Yatra (1997) duba a kan yadda auren mata fiye da guda ɗaya a tsarin Brahmi yake, da tsarin matsayi a cikin al'umma da kuma haramta wa bazawara sake aure - an taƙaita su ne ga masu kallo na musamman.

Amma fa shi gama-garin mai kallon finafinai ba shi da wata sha'awar kallon waɗannan finafinan ko ma ya damu da cewa ci gaba da kallon finafinai a wurinsa hanya ce ta fahimtar "asalin" Indiya sosai da kuma duk wata sarƙaƙiyar da take tattare da ita.

Har wa yau, NFDC ta fahimci muhimmancin riba sannan ta kaddamar da "Finafinan Indiya" a wani yunƙurin samun kuɗi ta hanyar faɗaɗa kasuwar tsofaffin finafinanta da aka shirya a shekarun 1980.

A wannan lokacin, asalin hadafinta na shirya finafinai masu mayar da hankali kan zamantakewa ya gushe.

Kuma yayin da gwamnatin masu tsananin kishin ƙasa ta BJP ta hau karagar mulki a karo na biyu a 2019, ta sake fasalin duk manyan hukumomin kula da finafinan ƙasar, har da NFDC wacce yanzu ake tafiyar da ita a matsayin mai sa ido kan wasu kananan hukumomi da kungiyoyi dake ƙarƙashinta.

Bayan shuɗewar dokar ta ɓaci, manufofin indira Gandhi masu sauƙin sha'ani da kuma ɗaga ƙafa da aka yi na a dinga shirya finafinai da suke da yancin sukar gwamnati ya yi aiki.

Ko shakka babu, soke bukin baje kolin finafinan isra'ila wata ƴar ƙaramar nasara ce, yayin da Bollywood, masana'antar shirya finafinai ta biyu mafi girma a duniya, ta ci gaba da kau da kai a kan ƙadi'ar Falasɗinawa.

TRT World