Daga Jasmine El-Gamal
A lokacin da muke bukin cika shekara ɗaya da faruwar harin da Hamas ta jagoranci kai wa Isra'ila na 7 ga watan Oktoba da kuma mummunan yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, yankin yana ci gaba da kasancewa cikin ruɗani.
Yaƙin da Isra'ila ta kaddamar kan Gaza da kuma faɗaɗa kai haren zuwa Lebanon ya yi sanadiyar mutuwar dubun dubatar rayuka, ya raba fiye da mutane miliyan 2 da muhallinsu sannan kuma ya jefa yiwuwar zaman lafiya a yankin Gabas Ta Tsakiya, musamman a halin yanzu, cikin rashin tabbas.
Yayin da Isra'ila ke shirin kai wa Iran hari a jerin hare haren taɓa-ni-ka-ga-gayya tsakanin ƙasashen biyu na baya bayan nan, waɗanda ke rayuwa a yankin na fargabar faɗaɗar yaƙin da ba za a iya tsayar da shi ba.
A irin wannan muhimmin lokaci, tambayoyi game da rawar da Amurka ke takawa na ta ƙaruwa. Duk da dai kawo yanzu ya gaza yin tasiri sosai kan matakan da Isra'ila ke ɗauka, shin yanzu shugaban ƙasa Joe Biden zai matsa wa firaministan isra'ila, Benjamin Netanyahu lamba domin hana bazuwar yaƙin?
Tuni Iran ta ƙarfafa lagon ƴan kanzaginta a Lebanon da kuma a yankin da hadafin raunana isra'ila. Ranar 8 ga watan Oktoba na shekarar da ta gabata, dabarar ta fara aiki yayin da Hezbollah, wacce ake kallon ƴar kanzagin Iran mafi ƙarfi da tasiri, ta harba ɗimbin makaman roka cikin arewacin isra'ila.
Wannan matakin ne ya haddasa kai wa juna hare hare na tsawon shekara ɗaya tsakanin Hezbollah da Isra'ila, da farko ya yi sanadiyar raba mutanen Isra'ila da muhallansu a arewaci sannan kuma yanzu mutanen da ke kudancin Lebanon.
A baya bayan nan Isra'ila ta kawar da hankalinta daga Gaza zuwa iyakarta ta arewaci yayin da sojojin suka faɗaɗa rikicin da gangan ta hanyar kashe Babban Sakataren Hezbollah Hassan Nasrullah a Lebanon.
Yanzu da Hamas da Hezbollah suka yi rauni sosai, yanzu isra'ila ta hangi wata dama da za ta yi wa Iran da kanta kwaf-ɗaya.
Rashin tasirin Amurka
A makwannin bayan nan, Netanyahu da sauran ƙusoshin isra'ila, har da tsohon firaminista Naftali Bennett, sun fito fili sun bayyana yiwuwa ko ma bayar da shawara da a kai wa tashoshin nukiliya Iran hari.
Irin wannan matakin ko shakka babu zai jefa yankin cikin mummunan rikici, sannan zai iya haddasa yaƙe yaƙe ta fuskoki da yawa, irin wanda zai jawo Amurka ciki ta wani irin yanayi da har yanzu ba a san irinsa ba.
Idan aka yi la'akari da yiwuwar faruwar yaƙin, sabon yunƙurin Amurka na yayyafa wa rikicin ruwa a yankin yana da matuƙar muhimmanci.
Sai dai, a maimakon yin amfani da dabarun diflomasiyyarta domin cim ma hakan, bisa ga dukkan alamu gwamnatin Biden ta zama mara tasiri, inda jami'an Amurka suka tseguntawa manema labarai cewa gwamnatin tana cigaba da nuna damuwa game da abin da gwamnatin Netanyahu ke faɗa kan sojoji da shirinta na diflomasiyya a yankin.
Biden ka iya ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki ta hanyar bayyana wa Isra'ila cewa Amurka ba za ta tsoma baki ba idan Netanyahu ya zaɓi kai hari kan tashoshin nukiliyar Iran. Hakan zai iya kawo cikas ga shirye shiryen isra'ila, amma babu wata alama a bayyane da ke nuna cewa Biden na duba yiwuwar ɗaukar wannan matakin.
Amurka, babbar aminiyar isra'ila, ta shiga tattaunawar diflomasiyya sosai game da yadda za a tafiyar da abubuwan da yaƙin Gaza ya haifar, amma furuci a hukumance game da hakan sun nuna ba da gaske ake ba idan aka kwatanta da abin da aka aikata.
Yayin da aka ruwaito cewa gwamnatin Biden tana ta buƙatar isra'ila da ta kauce wa faɗaɗa yaƙinta a Gaza da kuma yaƙin da take yi da Hezbollah a tsallake kar komai ya faskara, amma shugaban ƙasar da kansa ya ci gaba da nanatawa a fili cewa Isra'ila tana da ƴancin kare kanta da kuma jaddada cewa Amurka za ta ci gaba da kawo wa Isra'ila ɗauki idan hakan ya wajaba.
Idan yaƙin tsakanin isra'ila da Iran ya bazu, saka hannun Amurka ba zai taƙaita ga kare Isra'ila ba kaɗai. Dalilin haka kuwa shi ne hare haren mayar da martanin Iran kan isra'ila za su iya afkawa dakarun Amurka da aka jibge a yankin.
Gwamnatin ta Biden har wa yau ta bai wa Isra'ila taimakon makamai tun da aka fara ƙazamin yaƙin - kimanin dala biliyan $18 a shekarar da ta gabata - banda lokaci guda da Biden ya dakatar da kai wa Isra'ila makamai a watan Mayu, ya bijirewa kiraye kiraye na ya bayar da umurnin wasu dakatarwar ko ma ya ƙaƙaba mata babban takunkumin makamai.
Aniyar Biden ta ƙin amfani da bayar da taimakon soji a matsayin abin da zai tursasa a ba shi haɗin kai, bai tsaya ga aniyarsa kan tsaron Isra'ila ba kaɗai - yayin jawabinsa kan cika shekara ɗaya da kai harin 7 ga watan Oktoba, ya bayyana cewa shi ne shugaban Amurka na farko da ya ziyarci Isra'ila a lokacin yaƙi - har ma da matsin lamba daga cikin gida a shekarar zaɓe mai muhimmanci sosai.
Bisa ga dukkan alamu Biden ba ya so ya jawo ƙarin suka ko ma kasadar yi wa mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris kasassaɓar ƙuri'u sakamakon matakin da zai ɗauka.
Shugaban ƙasar ya fuskanci babban koma-baya sakamakon dakatar da kai waɗannan makaman a watan Mayu. Bisa ga dukkan alamu bai son ya jawo ƙarin suka ko ma kasadar yi wa mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris kasassaɓar ƙuri'u sakamakon matakin da zai ɗauka.
Rikicin mara ƙarshe
Ƙoƙarin Amurka na samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Lebanon kawo yanzu bai haifar da ɗa mai ido ba, kuma yayin da saura ƙasa da kwanaki 30 a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, da dama a yankin suna nuna damuwar cewa himmar White House wajen samar da yarjejeniyar tsagaita wuta zance ne kawai.
A halin da ake ciki, burin sojin isra'ila, musamman game da gine-ginen soji na Hezbollah da kuma babbar barazana daga Iran, bai cika ba. Kamar yadda Netanyahu ya bayyana a baya bayan nan, "Ba za mu huta ba har sai mutanen ƙasarmu za su iya komawa gidajensu lami lafiya, kuma za mu ci gaba da rusa Hezbollah har sai burinmu ya cika."
Amma kuma nacewa da Netanyahu ya yi kan ci gaba da daukar matakan soja ya haifar da babbar tambaya:Shin akwai wani tsarin wanzar da zaman lafiya na Isra'ila, ko kuwa iƙirarin isra'ila na nasara a kan Hamas da Hezbollah yana share hanyar rikici mara iyaka ne?
Kawo yanzu gwamnatin Biden ba ta iya amsa wannan tambayar ba, kuma ci gaba da ɗaura alhakin yaƙin da ake yi a kan bangare ɗaya, wato Iran da ƴan kanzaginta, bai nuna tana da niyyar zargin isra'ila kan matakinta na faɗaɗa yaƙin ba.
Yayin da babu shugaban Amurka tun George W Bush da ya nemi yaƙi a yankin, wasu a kafofin tsaron ƙasa a Washington da kuma majalisar dokoki, kamar ɗan majalisar dattawa ɗan jam'iyar Republican mai wakiltar Carolina ta Kudu, Lindsay Graham, ya daɗe da bayar da shawarar a kai hari kan shirin nukiliyar Iran.
Yayin da aka rasa shugabancin Amurka a yankin, gami da shagaltuwar Amurka da zaɓuɓɓuka da ke tafe, bisa ga dukkan alamu, bazuwar rikicin babu makawa.
Magaryar tuƙewa
A bayyane take, akwai sauran lokaci da za a iya hana yaƙi gadan-gadan tsakanin isra'ila da Iran da ƴan kanzaginta
Ministan Tsaron isra'ila Yoav Gallant zai ziyarci Washington a wannan makon, bayan ya sanar da Ministan Tsaron Amurka Llyoyd Austin ranar Lahadi da ta gabata cewa har yanzu isra'ila ba ta yanke shawarar ƙarshe game da girma da kuma lokacin mayar da martaninta kan Iran ba.
Ana fatan gwamnatin Biden za ta yi amfani da wannan muhimmiyar damar ta matsa wa Isra'ila lamba fiye da yadda ta yi kawo yanzu, ta gane cewa yaƙi tsakanin isra'ila da Iran zai iya rincaɓewa cikin sauri har ma ya iya ingiza Iran ta yi yunƙurin yin amfani da shirinta na nukiliya.
Yayin da muke duba kan shekarar da ta gabata, a bayyane take cewa yankin ya kai magaryar tuƙewa mai hatsari. Asarar da aka tafka tana da yawan gaske, inda aka samu dubun dubatar rasa rai, miliyoyin mutane suka rasa muhallinsu da kuma alamun yiwuwar gwabza mummunan yaƙi a yankin.
Idan ba a samu takamaiman shiga tsakanin ta fuskar diflomasiyya ba, akwai haɗarin yankin Gabas Ta Tsakiya zai faɗa cikin mummunan bala'i, abin da zai haifar da mummunan sakamako, ba a kan mutanen yankin ba kaɗai, har ma kan tsaron duniya gabaɗaya.
Marubuciyar, Jasmine El-Gamal tsohuwar mai sharhi kan tsaron ƙasa ce kuma tsohuwar mai bayar da shawara kan Gabas Ta Tsakiya a Pentagon. Ita ta assasa kana babbar jami'ar gudanarwa ta Mindwork Strategies, LTD, wata cibiyar tuntuɓa mai hadafin taimaka wa kungiyoyi wajen shata manufofin ƙasashen waje masu alaƙa da tausayi da kuma la'akari da al'ada, sadarwa da kuma lafiyar ƙwaƙwalwa a wurin aiki.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubuciyar ta bayyana ba dole ya zo daidai da ra'ayoyi, fahimta da kuma manufofin editan TRT Afrika ba.