Mariam Khateeb dai tana karatun likitan hakora ne a jami'ar Al-Azhar da ke Gaza kafin harin da Isra'ila ta kai wanda ya lalata cibiyoyin ilimi. (Mariam Khateeb  

Daga Mariam Al Khateeb

A kowane dare bana samun nutsuwa. A tsawon shekarar ɗaya ban samu wani cikakken barci ba. A baya karar fashewar bama-bamai da kuma ihun da ke biyo bayan shi ne ya ke hana ni barci . Amma a yanzu tunanin waɗannan daren da na kasa rufe idanuna a cikin ɗan karamin ɗakina da ke Kafr el- Sheikn mai tazarar kilomita 130 daga arewacin birnin Alkahira na ƙasar Masar.

Tsawon watannin bakwai kenan na ke nan, bai kamata ina nan har tsawon wannan lokaci ba.

Na kasance daya daga cikin “masu sa’a” da suka yi nasarar tsallaka kan iyakar Rafah kafin Isra’ila ta rufe shi a watan Mayu, inda aka ɗaure Falasdinawa, ciki har da iyayena, a sansanin mutuwa.

A duk safiya idan na tashi, sai na ɗauki wani ɗan lokaci kafin na iya gane inda make. Idan na tuna cewa bana kan gadona mai ɗumi a sansanin Nuseirat a Gaza, wani ciwo mai zafi ya kan bugi makogwarona ya gangara zuwa ramin cikina. Ciwon da nake fama da shi kenan na kewar iyayena. ina ji na tamkar na rasa komai.

Gaza tana mutuwa

Idan na haɗu da wasu daga Gaza waɗanda suke gudun hijira a nan (kusan mu 100,000 sun gudu zuwa Masar tun farkon yakin), muna taruwa don tunawa da inda muka fito 'yan 'uwanmu da kuma burinmu na komawa.

Wani wuri mai ban sha'awa a Gaza  da Mariam Khateeb ke yawan tunawa kafin barkewar yakin. (Mariam Khateeb)

Amma bayan shekara guda ana fama da yaƙi, ba ni da wani ƙarfin gwiwa. Gaza tana mutuwa.

Ko da idan 'yan' uwana sun samu damar barin wajen, sun haɗu da ni a Masar, me kuma ya rage? Mun rasa komai. Ina tunanin iyayena. Sun shafe tsawon rayuwarsu suna ƙoƙarin gina gida, su ba mu ilimi ni da 'yan uwana duk da cewa suna rayuwa a inda aka yi musu mamaya - a yanzu ba su da komai kuma dole ne su fara daga babu.

Ta yaya za mu fara kuma? Muna ɗauke da ciwo mai suna Gaza, ciwon da ake kira kisan kare dangi.

Ina ci gaba da tunanin rayuwarmu ta ƙare a watan Satumbar bara. Wannan shi ne karo na ƙarshe da muka ɗauki hotuna, muka yi ciyayya tare da abokanmu.

Daga 7 ga watan Oktoba, komai ya canza.

Ba a daina kai harin bama-bamai ba

Da safiyar ranar Asabar ce. Za a gudanar da wani taro a jami'ar da nake zuwa, kumu na ƙuɗuri aniyyar zuwa tare da ƙawayena.

Wani  ɗinkin zane da Mariam Khateeb take yawan saka wa a cikin jakarta don tuni da Falasdinu Palestine a kusa da ita yayin da take karatu a Masar. (Mariam Khateeb)

Na farka da ji wani kara tashin bama-bamai a gidana da ke Nuseirat, amma wannan ba sabon abu ba ne a Gaza. Kullum muna fuskantar farmaki daga Isra’ila, amma da alama duniya ba ta damu da mu ba sai a bara.

Ina tsammanin harin zai ɗauki 'yan sa'o'i kawai, ko kuma wasu kwanaki.

Amma a maimakon haka sai suka tsananta, kuma sautin bama-bamai ya biyo baya da sautin kururuwa mai raɗaɗi na iyalai ke kukan rasa makusantansu.

Bayan kwana biyu da faruwar haka, sai aka ce mu ƙaura, saboda za a kai harin bam unguwarmu.

Mun bar wurin da ƴan kwanaki kaɗan, da farko zuwa makarantar UNRWA, sannan muka tafi gidan kawuna dake gaba da mu kaɗan kafin mu dawo gidanmu a ranar 12 ga Oktoba. An yi barna sosai, amma har zuwa lokacin gidanmu yana nan.

Amma bayan wasu ƙarin kwanaki, sai umarnin Isara'ila ya biyo baya kan dukka arewacin Gaza. Za ta turo a rusa mana matsugunanmu.

Bayan mun tafi, babu wanda ya taba tunanin za mu yi hijira har na tsawon shekara guda.

Tawala, harshen Larabci ne da ke nufin 'ya yi tsawo', haka kowa ke cewa. An ci gaba da kai hare-haren bama-bamai, mutane na mutuwa kowace rana. Komai ya daina aiki.

Olives picked from orchards were once preserved in the Khateeb household. (Mariam Khateeb)

Yawancin matasa da ke tafiya zuwa makaranta kowace safiya yanzu suna yin layi don karɓan abinci, da ruwan sha, da sauran taimakon jinƙai ga iyalansu.

Teburan gidaje a Gaza da a baya ake baje kayan abinci na Falasdinawa cikin murmushi, sun zama fanko. Gidaje masu ni'ima, ko yaushe suna maraba,a yanzu sun zama tantuna ga waɗanda ke neman mafaka a cikinsu.

Mutane kusan muliyan 1.9 a halin yanzu suna gudun hijira a Gaza, waɗanda yawancinsu an tilasta musu yin ƙaura a lokuta da dama a shekarar bara.

Babu wata kalmar Turanci da ya yi daidai da ta larabci ma'jaat. Kamus na cewa “yunwa,” amma ya fi haka.

Ba wanda zai iya tunanin ma'anar yunwa a shekarar 2024, sannan babu wanda zai taba tunanin cewa yara za su mutu da yunwa kuma za a kashe mutane a yayin da suke neman abinci.

Barin Gaza A ranar 6 ga watan Maris, innata ta ƙira ni da safe. Ta ce an ƙira sunana a cikin jerin mutanen da ke kan iyaka. An bar ni na wuce zuwa Masar don ci gaba da karatun likitancina na hakora.

Ni kaɗai ce daga cikin ɗangina da aka bari na tafi, ƙanina da ƙannena mata biyu sun zauna. Yana da mahimmanci ga iyayena na ci gaba da karatuna, don in yi aiki don cim ma muraɗun rayuwata a gaba.

Amma daga daidai lokacin da na ke ƙoƙarin tsallake iyakar, sai na fahimci cewa na bar ruhi na a baya. Yanzu ina ji kamar ni kaɗai a cikin duniya nan.

Unguwar Fawakhir ya yi suna a birnin Gaza da tukwane. (Mariam Khateeb)

Na shiga cikin damuwa sakamakon bari na Gaza ni kaɗai. Na guje wa yanayi mai haɗari a ƙasata, amma ba na rayuwa mai ƙyau a nan. Eh, na ƙubuta daga hatsari, amma ba ni da wani ɗan'uwa a nan kuma ba na jin daɗi.

Wasu lokutan idan ina tafiya a kan hanya. sai na fara jin jiri, don haka na kira 'yan uwana na shaidawa musu cewa ina ji na kamar na haukace.

Ranar tuni da haihuwata ta kasance mara daɗi. A watan Yuni ne na cika shekara 20, wata uku bayan na bar Gaza. Kafin a fara yaƙin, mahaifiyata ta kan gasa min kek, sannan a kawata gidanmu da kayan ado, da kuma kyaututtuka.

Amma a wannan shekara, sai dai ƙiraye-ƙiraye da na yi ta yi da sauran 'yan uwana da suka tsira suna taya ni murna. Duk da tsananin wahalar da suke ciki, amma suk da haka sai da suka samu hanyar taya ni murna. hakan ya kara min kewarsu sosai.

Ina kewar rayuwata a can, da kuma jami'a ta. Titunan birnin ba su da wani ƙyau sosai, amma Gaza ce. Ban san abin da suke yi a gida ba ko kuma suna da abinci ko ma suna raye.

Ina jin warin mutuwa daga nan. Ina ganin ko dai warin konannun gawarwaki ne da ke tashi a cikin iska, da ya iya ketare iyakoki ba tare da takaddun shaida ba, ko kuma mafarki na ke yi.

A wasu lokutan, ina jin ƙamshin Gaza - (ƙamshi na musamman na mutane gauraye da warin teku.)

Wasu ma'aurata da suka samu nutsuwa a gabar tekun Gaza na daya daga cikin hotunan ƙarshe da Mariam Khateeb ta iya ɗauka kafin ta bar kasarsu. (Mariam Khateeb)

Akwai kuma ƙamshin abinci da sinadaren girki, da ƙamshin tsohon birnin Gaza da suke dawo min a cikin kaina. Wani ƙamshi ne da ba za ka iya kawar da shi ba.

A raina ina bin lungu da sako na birnin ina shakar kamshin abincin da ya shahara da shi, tare da danɗana abincin da ke titin Souq al Zawiya, wanda yake yawan cika da cunkoson jama’a a lokuta kamar watan Ramadan, da hutu da kuma yayin da daliɓai ke shirin tafiya jami'a kana suna sayayyan kayayyaki, za ka iya samun komai a wurin.

Ire-iren waɗannan abubuwa ne suke bani ƙarfin gwiwa, amma bayan yakin ya shekara guda, ina tsoron za mu iya rasa Falasdinu gabaki daya.

Ba ni kaɗai ba ve, tsoro ne da ke cikin zukatan yawancin Falasdinawa.

Yaƙin yana kara yaɗuwa, ya mamaye yankin Yammacin Kogin Jordan da Lebanon. Wannan shi ne abin da ke ba mu tsoro.

Yayin da lokaci ke tafiya, fatan Falasdinawa ya sauya daga komawa gidajen da suka bari a lokacin Nakba (masifa) zuwa komawa gidajensu da suka rasa a Gaza. Fatan komawa can a yanzu haka ya dusashewa.

Ga waɗanda har yanzu suke can, ina jin suna cewa "Mun gwammace mu mutu a ƙarkashin kurar Gaza, da mu fita mu zauna a wata ƙasa." Wannan tsayin dakar ita ce ƙarfinsu.

A halin yanzu ina rayuwa mai cike da ƙunci, wanda nake ji tamkar wani nauyi. A jami'a ina mu'amala da mutane da dama da muke mutunci da su, sana sanya murmushi a fuskata,kamar babu abin da ke faruwa. Amma a duk numfashin da na yi, ina tuna Gaza da shi - dukan 'yan uwa suna can.

Marubuciyar, Mariam Al Khateeb tsohuwar daliba ce a fannin likitanci a Gaza. sannan mamba ce a shirin We Are Not Number , wani shiri na taimaka wa matasa masu tasowa a Gaza damar ba da labarinsu ga ƙasashen duniya da kuma bayyana halin da Falasdinawa suke ciki.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba dole ba ne ya zo daidai da ra'ayi, fahimta da manufofin editan TRT Afrika ba.

TRT World