Daga Mubarak Aliyu
Tare da mayar da hankali kan kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar, ga manyan batutuwa uku kan siyasa da tsaro da za su iya tasiri a 2024 a yankin Sahel.
ECOWAS da hadin kan yanki
A lokacin da aka yi juyin mulki a Nijar, Kungiyar Cigaban Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta dauki matakan da ba a saba gani ba, ta yi barazanar afkawa Nijar, ta yi amfani da karfi wajen dawo da Shugaba Mohamed Bazoum kan mulki.
Rarrabuwar kai tsakanin ECOWAS ya yi tsamari a lokacin da Mali da Burkina Faso da ke karkashin mulkin soji - suka sanar da cewa idan aka dauki matakin soji kan Nijar, to za su yi wa hakan kallon yakar kasashensu ne.
Wannan sanarwa ta fito karara da rarrabuwar kan ECOWAS a tsakanin kasashen da ke gabar teku kasashe uku da ba su da gaba da teku.
Wannan rabuwar kai ya sake bayyana sosai a ranar 16 ga Satumba, shugabannin sojin Mali, Burkina Faso da Nijar suka sanya hannu kan Yarjejeniyar Liptako-Gourma, wadda ta kafa Kawancen Kasashen Sahel (AES).
An kafa AES da manufar habaka tattalin arziki da inganta tsaro a kasashen da suka kulla kawancen su uku.
A yayin da AES ta mayar da hankali kan samar da tsaro a gajeren lokaci, rikicin da ke tsakanin kasashen uku da ECOWAS na kara musu wani karfi a yankin, wanda hakan ya sanya da wahala a iya sulhunta yadda za su koma turbar dimokuradiyya.
Dadin dadawa, takunkuman ECOWAS sun janyo wahalhalu sosai ga Nijar, inda garuruwan da ke makotaka d aNijeriya suka shiga halin ni-'ya-su.
Wannan ya gurgunta tattalin arzikin kan iyakokin Nijar da Nijeriya, ya tasgata jin dadi da walwalar jama'a, ya kara lalata ayyukan jin kai da ake yi, sanna ya jefa manyan ayyuka irin su na shimfida bututun iskar gas da kasuwancin yankin cikin hatsari.
Tabbas, ra'ayin ECOWAS shi e amfani da hanyoyin diplomasiyya don warware rikici da kasashen AES, duba da irin rawar da kasashen na AES suke takawa wajen hana ta'addanci yaduwa a kasashen gabar teku da ke Yammacin Afirka.
Nuna kyama ga Faransa
Wani abu game da yankin Sahel da yankin Yammacin Afirka shi ne duba ga 2024 da yadda kasashe ke daukar matakan hana samun juyin mulkin soji.
Har yanzu dai akwai batutuwan tattalin arziki, tsaro da nuna kyama ga Faransa da aka yi amanna z asu kasance batutuwan kan gaba da suka janyo juyin mulki a yankin a shekaru uku da suka gabata.
Nuna kyama ga Faransa a yankin ya zama abun da ke kan gaba wajen tasirin siyasa da tsaro a nan gaba a yankin.
Kokarin kasashen Yamma don kalubalantar karfin ikon Rasha a yankin Sahel zai zama wani babban batu na manufofin kasashen waje.
Tare da kalubalen tattalin arziki da hauhawar farashi da karancin cimaka a duniya ke janyowa, jami'an soji a wasu kasashe za su iya amfani da halin kuncin da jama'a suke ciki wajen yin juyin mulki.
A yayin da 'yan ta'adda ke ci gaba da kai hare-hare, tsaro yake tabarbarewa, yanayin siyasa a kasashe da dama a yankin zai zama mai rauni.
Halin da Mali ke ciki
Baya ga yaki da ta'addanci, Mali ta shaida sake dawowar 'yan gwagwarmayar a ware daga 'Yan tawayen Azawad, wanda gamayyar 'yan kabilar Tuareg ne da ke yankunan Arewacin kasar.
Mayakan CMA sun fara tawaye a 2012, amma daga baya suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati a 2015.
Sai dai kuma, wutar rikici ta sake ruruwa bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta janye dakarunta na wanzar da zaman lafiya daga wasu garuruwan Mali a watan Yuni bayan kwashe tsawon shekaru.
A ranar 14 ga Nuwamba, sojojin Mali sun sanar da cewa sun kwace iko da garin Kidal mai muhimmanci a yankin Kidal daga hannun mayakan CMA, bayan kazamin rikicin da aka gwabza na kwanaki uku.
Sake kwace garin ya bayyana rushewar yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla, sabod agarin Kidal ne mafi muhimmanci a hannun CMA.
Haka zalika, shugaban rikon kwarya Assimi Goita ya ce ana ci gaba da daukan matakan tsaro.
Batun tsaro da hanyoyin magance shi a Mali na daga batutuwan da za su mamaye al'amuran da za a fuskanta a yankin a shekarar 2024 mai zuwa.
Duk da cewa 2024 ta zama kamar shekarar rashin tabbas ga yankin Sahel, tattaunawa diplomasiyya, musamman hadin kan yankin na da matukar muhimmanci wajen magance kalubalen siyasa da tsaro a yankin, da ma dukkan nahiyar Afirka.
Marubucin wannan makala, Mubarak Aliyu, Mai Bincike da Nazari Kan Al'amuran SIyasa da Hatsarin Tsaro ne, kuma ya fi mayar da hankali kan Yammacin Afirka da Yankin Sahel.
Togaciya: Ba dole ba ne ra’ayin marubucin ya zo daidaida ra’ayi ko ka’idojin aikin jaridar TRT Afrika.