Daga FARAH-SILVANA KANAAN
Akwai ban takaici ganin mutane suna tattaunawa a kafofin sadarwa cikin raha game da yiwuwar za a fadada harin kisan kiyashin da ake yi a wata kasa.
Sai ka ce wani wasan kwallon kafa ne da za a buga da mutum zai yi caca. Halin da mutanen Labenon suke ciki ke nan idan wadannan masu shan jinin suka samu yadda suke so.
Amma duk da barazanar nan da suke ciki a zahiri na fargabar hare-hare- wanda Amurka ke goyon baya - ana cigaba da rayuwa kamar ba komai da ke faruwa. A wani rubutu da wani dan Lebanon mazaunin kasar waje ya yi, wanda ya karade kafofin sadarwa, ya tambaya cewa, "shin mutum zai iya ziyartar Lebanon ba tare da wata matsala ba?"
Amsar da ya samu, duk da cewa kamar cikin raha aka fada, ita ce gaskiya, inda wani ya amsa a twitter cewa a'a. A Instagram kuma aka ce- eh.
Muna kai-komo ne tsakanin duhu da haske da rashin tabbas.
Halin yaki muke ciki
Babbar matsalar ita ce, Israila ta riga ta kaddamar da yaki a Lebanon. Farbagar yan Lebanon da suke zaune a wasu kasashe-da ma wadanda suke zaune a cikin kasar- cewa nan gaba kadan yaki zai iya barkewa a kasar, alhalin mutanen Kudancin kasar kullum suna cikin kugin bama-bamai ne da jiragen yakin Israila ke aikowa, inda akalla mutum 450 suka mutu tun daga 8 ga Oktoban bana ai ya isa ya nuna cewa yakin ake yi.
Kusan mutum 100,000 na Kudancin Lebanon ne suka tsere daga gidajensu. Wannan kadai ai ya isa matsayin yaki.
Duk abin da mutane za su cigaba da fada na cewa mu ne muka jawo wa kanmu halin da ake ciki wai saboda mun goyi bayan kungiyoyin tada kayar baya-shin ba za mu kare martabar kasarmu ba wadda ita Israilar da mutanenta suke neman kwacewa a kullum?
Alamu sun nuna cewa Lebanon ba ta taba kasancewa ba a yanayin yaki da Israila ba. wannan shi ne abin mamakin saboda gwamnatinmu ba ta ma amince da kasar Israilar ba a hukumance.
Israila ta riga ta kaddamar da harinta a manyan birane irin su Saida da Sour da Baabek. Ta kashe jagoran Hamas a Beirut. Suna so kuma mu amince cewa ragargaza Dahiye, wanda wani yanki ne da suka yi raga-raga da shi a 2006 wai saboda laifin goyon bayan Hezbollah ne, kuma wai wani yanki ne daban da Beirut ba, wanda ba haka ba ne.
Yanki daya ne, kusa da inda nake aiki ne, inda mutane da dama da na sani suke rayuwa tare da iyalansu. A wajen ne ake samun shagunan litattafai masu kyau a Beirut.
An jikkita gomman yara kanana a harin da aka kai a wata motar makaranta, an kashe kananan mata a Sour, haka kuma akwai rahotannin an kai farmakin a kan maaikatan fararen hula da yan jarida. Wannan ai a zahiri yaki ake yi. Yakin tunani da zahiri.
Rabuwar kai mai tsanani
Lallai fadadar yakin ba abu ba ne da duk wani mutum mai hankali zai so ganin haka.
Amma wasu (ciki har da ni) muna ta mamakin saboda ganin abubuwan da suka faru a wata 9 din nan da suka gabata, (da kuma wadanda suka faru a shekarar 2021 da 2014 da 2006 da sauran shekaru) cewa: watakila zai fi kyau kawai a fito fili a gwabza yakin idan har hakan ne zai kawo karshen Israila, ya kawo karshen kama wuri zauna, da kuma samar da yancin Falasdinu, babu wanda yake shaawar yaki.
Babu wanda yake so a kashe shi, ko a kashe na kusa da shi. Babu wanda zai so ya ga an ragargaza Lebanon. Kasa ce da take cike da mutane, mai dadadden tarihi. Kasa ce mai mutanen da kashe wasu zai shafi rayuwar wasu da dama.
Kowane mutum yana so ya rayu cikin natsuwa ba tare da fargaba ba, sannan duk yadda masu raayin kafa kasar Yahudawa zalla (da abokansu masu karfi a duniya) suke so su nuna akasin haka, lallai Larabawa mutane ne kamar kowa. Muma mutane ne da babu abin da muke bukata tamkar samun kwanciyar hankali da natsuwa daga fargabar da muka dade a ciki.
Mutanen Labenon suna tunanin, mutanen Labenon suna son kullum masu sharhi da yan jarida da wasu wawayen mutanen a kafofin sadarwa suna so su rika hasashen abin da ke cikin zukatan mutanen Lebanon. Amma duk wanda ya san kasar nan na hakika, ba wanda yake bibiyar kasar domin wata manufa ba, ya san cewa Labanon ba kamar yadda suke nuna take ba.
Kasa ce da take fama da matsalar rabuwar kai. Wasunmu ba za su yi komai ko da suna gani ana yanka yan uwansu a kusa da su, ko kuma ana tarwatsa su, domin ba ma yin komai domin dakatar da aukuwar hakan.
Wasu kuma babu ruwansu da abin da ke faruwa da Falasdinawa, sannan za su yi maraba da maslaha da Israila- hakan zai inganta tattalin arzikinmu, kamar yadda wani ya taba fada min. Ni dai ban taba kallon Israila a matsayin haka ba.
Zaman jira da kallon kallo
Mutane da dama suna godiya tare da amannar cewa Hezbolla za ta iya kare kasar Lebanon baki daya, ba ma Kudancin kasar kadai ba.
Wasu kuma suna zargin Hezbollah da duk wata matsala da kasar take ciki ne, don haka ba za su damu ba idan aka sake mamaye Kudancin kasar maimakon wanzuwar Hezbollah a yankin.
Kai ka ce Kudancin ba mallakin Lebanon ba ne, tamkar wata kasa daban, kamar ba kasarmu ba ce da kuma yankin da ke rike da tarihinmu.
Yankin Kudancin ne ya hada mu da Falasdinu. Asalinmu daya ne. A wajen wasu daga cikinmu, har yanzu daya muke.
Yanzu lokaci ne na bazara, lokacin da manyan mutane suke rububin zuwa Lebanon domi shakatawa a wuraren shakatawa na bakin tekunan kasar masu tsada-ko zuwa wuraren shakatawar yanzu ana nema a ƙwace mana- wadanda kuma ake amfani da su domin cimma wata manufar ce suka zuwa wuraren shakatawa, ana shakatawa, ana kuma yi Beirut dariya, wadanda kuma suke tsaka-tsakiya suna zuwa wuraren shaktawa na birnin Sour wanda kyauta ne duk da barazanar da ake fuskanta a yankin na harin bama-bamai da mutuwa.
Za mu mayar da Beirut kamar yadda take a zamanin jahiliya, inji wasu daga cikinsu. Idan muka ji hakan sai mu rika yin dariya, ba mu da kudi, ba mu da wutar lantarki, babu ruwan sha, ai mu a zamanin jahiliyar muke yanzu,
Wasu na cewa mutanen Labenon ba su da juriya-kar a mana kallon haka-mu mutane ne, da a kullum muke fuskantar barazanar mamaya daga makwabtanmu da suke da niyyar illata kasar baki daya.
Sannan su wane ne suke fatan ganin an kararmu da mu- Za mu mayar da Beirut kamar yadda take a zamanin jahiliya, inji wasu daga cikinsu. Idan muka ji hakan sai mu rika yin dariya, ba mu da kudi, ba mu da wutar lantarki, babu ruwan sha, ai mu a zamanin jahiliyar muke yanzu,
Me za mu iya yi?
Za mu cigaba da zaman jiran tsammani ne. Za mu hadiya bakin cikinmu, mu cigaba da sauraron abubuwan da yan siyasar Yamma da kafafen labaransu suke yadawa a game da mu, da kuma yadda mashaya jinin nan Israila da abokansu suke ta hankoron ganin bayanmu.
A lokacin da muke ta taunanin wai me ya sa duniya ta kasa dakatar da kisan kiyashin da ake wa mutanenmu, a lokacin da muka ta kokarin cigaba da rayuwa kamar babu abin da ke faruwa-alhali mun san cewa abubuwa suna faruwa- inda muke tambayar kanmu yaya kake alhalin dukkanmu mun san amsar tambayar.
Muna ta zaman jira amsa tambayar shin mutum zai iya ziyartar Lebanon lafiya kalau? Daga wadanda suke zaune a kasashen waje-wasunsu tilasta musu aka yi barin kasar- wasu daga cikinsu kuma sukan yanke shawarar zuwa ziyartar 'yan'uwansu duk da barazanar yakin (ko banza mu mutu tare) ko kuma su manta da 'yan'uwansu su rika kallon abin da ke faruwa daga nesa saboda fargabar idan aka jefa bam a filin jirgin, ba za su iya komawa inda suke rayuwa ba, inda suke aiki, su samu yan kudaden da suke turawa gida wanda yan uwansu suke samun na sakawa a bakin salati.
Kullum yanayin kasar a cikin fargaba ake na barazana daga Israila, wadda kamar yadda muka gani, suke aikata laifin tauye hakkin yan Adam mafi muni a tarihi. Sai dai kawai mu yi kuka, mu share hawayenmu.
Sai dai mu yi ta zaman jira. Muna jiran ranar da wutar lantarki za ta dawo, da kuma zaman jiran lokacin da karshen duniya zai zo.
Game da marubuciyar
Farah-Silvana Kanaan yar asalin Lebanon ne mazaunin dan jarida mai zaman kansa a Italiya da Holland na jarida da rediyo da talabijin. Ta yi aiki a matsayin mai kawo rahoto a kan kasuwanci, ta yi editar jaridar The Daily Star a Lebanon, sannan a kwanakin nan ta yi aiki a jaridar Middle East Eye da The New Arab.
Tana yawan kawo rahoto a kan Lebanon a gidan rediyon Lebanon. A matsayinta na yar jarida, tana kokarin zakulo labarai da suka shafi alumma, musamman a game da siyasar Gabas ta Tsakiya da aladunsu.