Kafofin watsa labaran Iran sun ruwaito cewa wani “bam da aka harba daga jirgi” ya faɗa kan gidan da Haniyeh yake zaune Haniyeh ke zaune.

Alamu sun nuna cewa irin kisan gillar da ya kaɗa mutane ta shugaban Hamas Ismail Haniyeh a Tehran babban birnin Iran, ya ƙara sa yaƙin da ake yi a Gabas ta Tsakiya ɗaukar sabon salo.

Wannan kisan gillar – wadda Isra’ila ta yi - na iya zama wani abin da zai ƙara rura wutar rikicin Isra’ila a Gaza kuma hakan na da yiwuwar ƙara faɗaɗa wannan rikicin zuwa wani babban yaƙi.

Idan hakan ta faru, tasirin rikicin za a ji shi a faɗin duniya kai tsaye da kuma ba kai tsaye ba sakamakon yadda farashin man fetur zai taɓu da kuma hanyoyin teku da ake bi domin cinikayya.

Domin haka, duniya da kuma ƙasashe masu ƙarfin faɗa a ji, irin su Amurka dole ne su ɗauki mataki domin daƙile fargabar da ke tasowa daga Gabas ta Tsakiya da kuma ƙara matsa ƙaimi domin kawo ƙarshen yaƙin Isra’ila kan Falasɗinawa Sai dai damar da ake da ita a halin yanzu ta diflomasiyya domin sassauta rikicin ba babba ba ce a wannan lokacin.

An kashe Haniyeh, wanda ake kallo a matsayin tsakatsakin shugaba, da kuma dogarinsa da misalin ƙarfe biyu na dare a wani gida da tsoffin mayaƙa ke zaune a Tehran, kamar yadda kafar watsa labarai ta Iran ta tabbatar.

Kafofin watsa labaran Iran sun ruwaito cewa wani “bam da aka harba daga jirgi” ya faɗa kan gidan da Haniyeh yake zaune Haniyeh ke zaune.

Duk da cewa ya je Iran ɗin ne domin halartar rantsar da shugaban ƙasar na tara Masoud Pezeshkian, ba wai ƙaramin abin kunya bane kawai ga jagorancin Iran, sannan kuma hakan hakan zai rinƙa sawa ana dasa ayar tambaya kan tsarin da suke da shi a ƙasa dangane da batun tsaro ga manyan baƙi irin su Haniyeh.

Irin yadda aka gudanar da kisan gillan da kuma yadda lamarin yake ya saka Iran cikin tsaka mai wuya.

A hannu ɗaya, lamarin zai tilasta wa Iran mayar da martani da wata hanya a daidai lokacin da ƙasar ke ƙoƙarin nuna ƙarfinta a yankin. A ɗayan hannun kuma, ƙara ruruta wutar rikicin na iya ja wa Iran matsala, ganin cewa Isra'ila na samun goyon bayan kasashen yammacin duniya da Amurka ke jagoranta.

Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga Isra’ila kan kisan zuwa yanzu, tuni kafar watsa labaran Iran ta soma nuna yatsa ga Tel Aviv. A bayyane, Isra’ila ba ta ce komai dangane da wannan harin ba a cikin Iran.

Sai dai an alaƙanta ƙasar da kashe wasu masana kimiyyar nukiliya da kwamandojin soji a baya.

Duniya ta shaida yadda Iran ta mayar da martani dangane da hari ta sama da Isra’ila ta kai kan ofishin jakadancinta da ke Damascus, wanda ya yi sanadin mutuwar dakaru bakwai na rundunarta ta Juyin Juya Hali.

Mako biyu bayan harin na Isra’ila, Iran ta mayar da martani bayan ta aiwatar da wani babban harin jirgi maras matuƙi da kuma makamai masu linzami. Sai dai akasarin waɗannan makaman da jiragen marasa matuƙa an daƙile su.

Duk da cewa Isra’ila ba ta mayar da hankali nan take ba ta hanyar buɗe wuta a kan sansanin sojinta na sama, hakan bai ƙara rura wutar rikicin ba.

Sai dai duk da haka, irin waɗannan hare-haren na cewa kule da mayar da martani da cas, ya fito da rikicin da ake yi tsakanin Isra’ila da kuma Iran a fili.

Shin Isra'ila da Iran za su iya shawo kan tashin hankalinsu kamar yadda suka yi a watan Afrilun wannan shekara? Wannan wata tambaya ce da ke da tambayoyi da amsoshi.

Wannan lamarin zai tilasta wa gwamnatocin Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa waɗanda a halin yanzu suke son tsayawa a tsakiya wurin diflomasiyya bayyana matsayarsu musamman idan fargabar da ke tsakanin Iran da Isra’ila ta koma yaƙi.

Ita ma Pakistan hakan zai faru da ita, ƙasar da ke da iyaka ta kilomita 900 daga yammacin Iran.

Tsayawa a tsakiya ta ɓangaren diflomasiyya zai fi sauƙi fiye da aikatawa. Duk ƙaruwar tashin hankali zai jefa ƙasashen Musulmi da dama cikin wani hali inda kuma dole ne su shirya jure wa matsalolin tattalin arziƙi sakamakon faɗaɗar yaƙi a Gabas ta Tsakiya.

Hakan zai zama wani mummunan lamari ga ƙasashe irin su Pakistan waɗanda har yanzu ba su kammala farfaɗowa daga matsalar rikici ba. Ƙaruwar farashin man fetur a ƙasar zai yi matuƙar ƙara musu matsin tattalin arziƙi.

Kuma Iran da Isra'ila sun kasance wani bangare daya kacal na rikicin da ake iya fuskanta, wanda manyan kasashen duniya ke bukatar daƙile shi.

Abin da aka fi mayar da hankali akai shi ne ita kanta Gabas ta Tsakiya da kuma rikicin Isra'ila da Falasdinu da ke ci gaba da jan lokaci. Tuni dai yankin Gabas ta Tsakiya ya yi kaca-kaca saboda yaƙin da Isra'ila ke ci gaba da gwabzawa a Zirin Gaza tun daga watan Oktoban shekarar 2023.

Kisan Haniyeh ya ƙara dagula al'amura tare da zama koma baya ga yunƙurin tsagaita wuta a Gaza wanda Amurka da Qatar da Masar suke shiga tsakani watanni da dama da suka gabata.

Kisan gillar da aka yi wa shugaban siyasar Hamas ya taɓarɓarar da duk zaɓukan da ake da su na samar da zaman lafiya ga ƙungiyar, don a yanzu an biyo hanyar da za a tursasa mata ta mayar da martani duk da cewa a yanzu ƙarfin reshen rundunar dakarunta ya ragu kuma abubuwa sun sha musu kai saboda yaƙin da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa da Isra’ila ke ta yi.

Isra’ila ba ta tsaya ga yaƙinta da Hamas ba kawai, ta kuma buɗe wani sabon babin fito-na-fito da ƙungiyar Hizbullah ta Labanon. Ita ma ƙungiya ce mai alaƙa ta ƙut-da-ƙut da Iran.

A ranar Talata, Isra’ila ta yi ikirrain cewa ta kashe babban kwamandan Hizbullah a wani hari da ta kai birnin Beirtut na Labanon, wanda tuni aka fara ganin yadda ya harzuƙa Hizbullah wajen mayar da martani.

Sannan akwai sauran wasu ƙungiyoyin Falasɗinawan. Kisan gillar da aka yi wa Haniye zai iya jawo martani daga gare su a kan Isra’ila da muradunta, ba a yankin ba kawai har ma a sauran sassan duniya.

Babbar barazanar za ta fito ne daga ƙananan ƙungiyoyin da ba su yi ƙarfi ba sosai da kuma ɗaiɗaikun mutane.

Hakan na nufin akwai yiwuwar a samu harin ramuwar gayya bayan kisan gillar shugaban ɓangaren siyasa na ƙungiyar Hamas.

Kisan Haniyeh ya kuma dasa ayar tambaya game da dalilin aikata wannan aika-aika yayin da ake kallonsa a matsayin mai sassaucin ra'ayi a cikin kungiyar Hamas, wanda ya taka rawar a ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya da nufin samar da tsagaita wuta a Gaza.

Ana kallonsa a matsayin babban abokin hulda da wasu manyan shugabannin Hamas, ciki har da Yahya Sinwar a Gaza.

Kisan gillar biyu da aka yi su a jere - ɗaya na shugaban Hizbullah a Labanon da kuma na shugaban Hamas a Iran – ka iya ta’azzara yanayin da ake ciki da ma rura wutar rikicin.

Sai dai, idan aka yi gaggawar shiga tsakani na diflomasiyya to za a iya dakatar da ta’azzarar yanayin.

Wani Sakataren Tsaro na Amurka Lloyd Austin ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba a ƙasar Philippines cewa ba ya jin idan lallai yanayin ya zama dole sai an yi yaƙi.

"Ina ganin ko da yaushe akwai damarmarkin shiga tsakani na diflomasiyya… Za mu yi duk abin da za mu iya don tabbatar da cewa mun kiyaye al'amura kar su zama wani babban rikici a yankin."

Amma ko gamayyar Ƙasashen Yamma ƙarƙashin jagorancin Amurka da kuma ƙawayensu na Gabas ta Tsakiya za su iya galaba a kan munanan dabarun yaƙin Isra’ila?

Ko za su iya kare rikicin da yake ƙara ta’azzara a baki ɗayan yankin? Kuma ko za su iya kawo zaman lafiya mai ɗorewa a Gabas ta Tsakiya ta hanyar tabbatar da cewa sun gabatar da yarjejeniya mai cike da adalci da za ta bai wa Falasdinawa damar yin rayuwa a cikin aminci da daraja a cikin ƙasarsu?

Waɗannan ne tambayoyi masu muhimmanci da ba su da amsoshi, duba da mummunan tarihin zubar da jini da rikici da aka daɗe ana ciki a Falasɗinu.

Amma a yanzu ba wai Gabas ta Tsakiya ba ne kawai, duniyar ma gaba ɗaya a ankare take saboda kisan gillar Haniye da irin abubuwan da ka iya biyo bayan hakan.

TRT World