Daga Kaddu Sebunya
Afirka na wani bigire mai matuƙar muhimmanci. Shekarun baya bayan nan sun nuna yiwuwar nahiyarmu ta tsara hanyar ci gaba mai tushe cikin ɗorewa da haɗin kai, da sabbin abubuwa.
Akwai alamu masu ƙarfafa gwiwa. A cikin 2024, rabin duk jarin da aka zuba a Afirka sun kasance masu tagomashi, wanda ke nuna ci gaba mai ɗorewa.
Yayin da muke hangen gaba, dole ne mu kasance masu tsari da dabara game da ƙalubale na kurkusa da hangen nesa game da muradu na dogon lokaci.
Dole ne ƙungiyoyin sa-kai masu zaman kansu su ci gaba da aƙidar jagoranci tare da samar da haɗin kai, da bin diddigi da kuma mutuntawa. Kuma dole ne a ƙarfafa shugabannin duniya su yi haka.
Alal misali, zaɓen Ƙungiyar Tarayyar Afirka da ke tafe a cikin watan na Fabrairu, yana ba da damar ƙarfafa irin jagorancin da ake buƙata don ciyar da Afirka gaba.
Ya kamata mu bari wannan shekarar ta kasance shekarar da za mu dauki darasi daga abin da ya faru a baya mu kuma yi amfani da su. Bai isa a fahimci “me yasa” dole ne mu yi aiki ba.
Dole ne a mayar da hankali kan yadda makomar Afirka za ta koma da kuma fahimtar dangantakar da ke tsakanin mutuwar halittu da sauyin yanayi da rashin abinci da kuma lafiyar al'umma.
Sakamakon wani bincike da kungiyar IPBES Nexus ta saki kwanan nan ya nuna muhimmancin dalilin da ya sa dole ne mu yi aiki tuƙuru a yanzu.
Fiye da rabin al'ummar duniya suna zaune a yankunan da ke fama da mafi girman tasiri na raguwar nau'o'in halittu da wadatar ruwa da ingancin rayuwa, da samar da abinci, da karuwar barazanar lafiya da kuma mummunan tasirin sauyin yanayi.
Bugu da ƙari, kudaden da ake kashewa na magance asarar nau'ukan halittu, wanda tuni ke da gagarumin gibi na kudi, zai ninka idan aka jinkirta shi da shekaru goma kuma ya kara kusan dala biliyan 500 a kowace shekara don magance sauyin yanayi.
Damarmakin da ke gaba
A shekarar 2024, an gudanar da zabuka na matakin kasa guda 65 a duniya, wanda hakan ya sa ta zama mafi muhimmancin a shekarun zabe a tarihi.
Wannan abu ya sa an shiga mataki mai muhimmanci na tunkarar shekaru masu zuwa, inda yake ba da damar
Masu zabe a Afirka sun nuna ƙaruwar son samun shugabanni wadanda ke fifita gaskiya da hadin kai da muradu masu dogon-zango.
A shekarar 2025 ma za a sake wasu zaɓukan 45 a fadin duniya, abin da ke nuna ƙaruwar buƙatar da mutane ke da ita daga shugabanni.
Shugabannin da aka zaba a wannan lokaci mai muhimmanci za su zama na musamman wajen ƙarfafa hadin gwiwa a yankuna da fannoni daban-daban, da tabbatar da tsari na gaskiya masu ƙarfi.
Lallai ana ƙara buƙatar jajirtattun shugabanni waɗanda suke ƙoƙarin samar da ci gaba da tsari mai kyau.
Tasirin waɗannan zaɓukan zai ƙaru a cikin zamanai, yana nuna wajibcin zaɓen ɗaiɗaikun mutane waɗanda za su jagoranci al'ummominsu - da kuma al'ummomin duniya - zuwa ga makomar haɗin kai da samun damarmaki.
A bana, shirin kasuwanci marar shinge na Afirka (AfCFTA) zai fara aiki, da nufin kawar da kashi 90 cikin 100 harajan da ake ƙaƙaba wa kasuwanci da kuma bunƙasa kasuwancin a tsakanin ƙasashen Afirka daga kashi 16 zuwa kashi 52 cikin 100.
Ana hasashen tattalin arzikinmu na intanet zai kai dala biliyan 180, kuma ya ƙaru ne sakamakon ingantuwar intanet da ƙaruwar mutane masu amfani da tsarin fasaha.
Me hakan ke nufi ga mutane da dabbobin dawa?
Hakan na nufin manyan damarmaki don kawo tsare-tsare kan teburin tattaunawa a matsayin jagoran haɓakar tattalin arziƙin ta hanyar kayayyaki da aiki na tushen yanayi da haɓaka mai ɗorewa, da yin amfani da fasaha don ƙarin ƙwararriyar fahimta da yanke shawara mafi kyau.
Akwai wani taro mai muhimmanci da za a yi a sabuwar shekarar nan: Afirka ta Kudu za ta zama ƙasar Afirka ta farko da za ta karɓi baƙuncin Taron G20.
Taron zai zama wata dama ga Afrika da za ta jaddada samar da tsarin tattalin arzikin duniya na adalci wanda zai ƙunshi ƙarfafan alkawura wajen zuba kudi a fannin makamashi mai tsafta da kasuwanci da zuba jari a kan mutane musamman ma mata da matasa.
Dole ne mu jaddada rawar da Afirka ke takawa wajen magance matsalolin duniya kamar su sauyin yanayi da raguwar halittu da kuma talauci.
A yayin da Gasar Cin Kofin Afirka ta bara, tawagogin ƙasashen Afirka da suka sanya wa kulob dinsu sunayen namun dajin ya nuna irin ƙaunar da muke da ita ga yanayi da muhalli.
Irin wannan alaƙa kamar ta wasanni na haɗa kawunanmu. Suna haɗa kanmu. Don haka mu bari su ƙarfafa mana gwiwa a wannan sabuwar shekarar.
Dole rayuwarmu a 2025 ta zama mai cike da fata da jajircewa da aiki tuƙuru da zai sa mutane su mayar da hankali kan inganta muhalli da dabbobin daji.
Dole ne mu mayar da hankali wajen gano hanyoyin warware matsalolin ƙarewar namun daji don taimakon Afirka - kuma duniya ta fahimci cewa, ɗorewar ayyuka na daga cikin abubuwan da za su sa mu gina wa nahiyarmu makoma mai kyau musamman don jin daɗin mutane da ceto dabbobi.
The author, Kaddu Kiwe Sebunya is the CEO of African Wildlife Foundation (AWF) with a career in conservation spanning over three decades across the USA, Africa, and Europe
Mawallafi maƙalar, Kaddu Kiwe Sebunya, shi ne shugaban Gidauniyar Kula da Namun Daji ta Afirka (AWF) , kuma ya shafe fiye da shekara 30 yana aiki a Amurka da Afirka da Turai.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.