P Firaminista Narendra Modi na tattaunawa da Rahul Gandhim shugaban babbar jam'iyyar adawa ta India CP. / Hoto: AP Archive

Daga Smita Gupta

A ranar 8 ga Yuni za a rantsar da Narendra Modi na India a matsayin Firaminista a karo na uku a tarihi, amma a wannan karon, gwamnatinsa za ta dogara kan jam'iyyu daga yankuna biyu da suke adawa da jam'iyyars ata BJP mai dabbaka manufofin fifita jama'ar Hindu.

Tare da dawowa siyasar hadaka, Modi ba zai samu cikakken karfin zartarwa ba, ko ya iya biris da kundin tsarin mulki da sauran hukumomin dimokuradiyya ba kamar yadda ya yi a shekaru goman da suka gabata.

Surkullen Modi da ya shahara bai yi tasiri a wannan karon ba - surkullen da a baya, ya sanya a yanzu masu jefa kuri'a sun murza gashin baki tare da bayar da nasara ga wadanda ba sa samun ta a baya.

Jam'iyyar MJP ta Modi ta rasa sama da kujeru biyar da ta lashe a 2019, kuma duk da an sake zabar sa daga mazabarsa ta Varanasi, kuri'un da ya samu sun ragu sosai kamar da maki tara.

A fadin kasar, jam'iyyar BJP ta lashe kujeru 240, kasa da adadin da ake bukata na 271 don kafa gwamnati kai kadai, wato tana neman karin kujeru 32 kenan. Tare da kawayenta na jam'iyyar NDA, ta samu kujeru 291, kasa da adadin 400 da ta yi fatan samu.

Kuma wannan zabe ne da Hukumar Zabe ta India ta nuna bangarenci karara a bayyane.

Ba wai iyakacin haka ba, BJP na da kayan aiki sama da dukkan sauran jam'iyyu idan aka hade su waje guda, kuma ta yi amfani da dukkan hukumomi da jam'ian gwamnati wajen kalubalantar 'yan adawa.

Jam'iyyar adawa ta kaancen Indiya, ta lashe kujeru 240, inda ta Congress ta ninda adadin da ta samu a 2019 inda a yanzu ta lashe 99 a majalisar dokokin.

Wadannan alkaluma na nuni da cewa za a samu daidaito wajen tunkarar juna a majalisar dokoki a wannan karon sabanin yadda ta kasance a baya inda NDA da BJP ke wa jagoranci take da gagrumin rinjaye.

A yanzu da wahala BJP ta kawo wata doka ko tsari a majalisa da zai tsannata wa wasu al'ummu a kasar.

Modi ba zai iya samun damar tattake abokan aikinsa na majalisar ministoci, 'yan jam'iyya da ma 'yan adawa.

Ya zamar masa dole ne ya nemi tsarin tafiya tare da kowa cikin adalci, sannan kuma ba zai samu damar nada wanda yake so a wani mukami na wata ma'aikata ko hukuma ta gwamnati ba, kamar irin su hukumomin bincike, bangaren shari'a da Hukumar Zabe.

Sannan ya zanarwa Modi dole ya amince a bukatun kawayensa na jam'iyyuna TDP, Janata Dal-United, da bangaren d akansa ya rabu na Shiv Sena da NCP, wanda su ma sun hada kai da NDA.

Tabbas, a ranar biyar ga Yuni, kasa da awanni 24 bayan sakamako ya zo, rahoton bayan zabe na farko na jam'iyyar NDA ya yi nuni da cewa kawayen da za a kafa gwamnati da su sun mika wa Modi jerin bukatunsu - adadin ministocin da suke so tare da mukamai a sauran hukumomi.

Haka zalika, jam'iyyar TDP ta bukaci mukamin shugaban majalisar Lok Sabha, babban mukami a kundin tsarin mulki da aka dora wa alhakin kafa karamar majalisar dokoki.

Idan wannan bukata ta karshe ta karbu tare da tabbata, to za a samu gagarumin sauyi wajen tafiyar da harkokin karamar majalisa, saboda BJP ba ta isa ta hana 'yan adawa magana ba.

Ya kuma zamarwa Modi dole ya sasanta da Rashtriya Swayamsewak Sangh, wanda daga nan suka samu nasu tsari da tunanin.

Mambobinta sun yi wa BJP aiki a lokacin zab, amma a wannan karon, rahotanni sun bayyana cewa sun janye hannayensu a wurare da dama.

Shugaban BJP, JP Nadda ya kara munana yanayin a lokacinda ya yi wata gana wa da 'yan jaridu inda ya ce"Da fari, da mun zama karayayyu, raunana masu bukatar taimakon RSS. A yau, mun girma kuma karfinmu ya kai. BJP na takara ita kadai."

Ga jam'iyyar Cpngress wadda bayan jagorantar kafa gwamnatin kawancen UPA a tsakanin 2004-2014 - ta karye inda ta amu kujeru 44 kacal a majalisar dokoki a 2019 kuma ta samu 52, a wannan karon kuma ta lashe kujeru 99, alamun dake nuni da tana farfadowa.

A lokacin da zabe ya karato, jam'iyyar Congress ta Rahul Gandhi ta dinga kokarin fadada a dukkan kasar a cikin shekaru biyu.

Wannan ya taimaka sosai wajen farfadowar jam'iyyar tun daga tushe a matsayinta na wadda ta kusa ruhe wa inda ta baiwa Gandhi damar mika sakonni ga dubunnan mutane.

A yanayin hakan, ya ci gaba da samun shuhura da karbuwa. Wannan shaida ne a irin nasarar da ya samu a kujerun da ya tsaya takara - Rae Bareli a Uttar Pradesh da Wayanad a Kerala.

Tabbas, ya samu tagomashi a wannan zaben, a yanzu ya samu matsayin shugaba a matakin kasa.

Jam'iyyar Congress da sauran jam'iyyun yankuna da suka hada da kawancen Indiya sun yi yakin neman zabe da manufofi da dama; sun yi amfani da matsalar tattalin arziki, da ya janyo rashin ayyukan yi da hauhawar farashi, sannan rikicin bangaren noma; a lokaci guda kuma sun ginga nuna cewa idan BJP da kawayenta suka samu kuri'u 400, kamar yadda jam'iyyar ta yi alkawarin sauya kundin tsarin mulki da kawo karshen tsarin raba mukamai da ayyuka tsakanin yaruka da sauran jama'aun kasar.

A karshe, sun yi bayani kan hatsarin mulkin kama karya, kalaman nuna tsana da zaluntar 'yan tsiraru.

Duk da rashin hadin kan jam'iyyun, amma sun yi kokarin jan ra'ayin jama'a, duk da ba a ko'ina ba, amma an ga hakan a Maharashtra, Rajasthan, Uttar Pradesh da West Bengal, wanda dukkan su suke da kujeru 195 daga 542 da ake da su a majalisa.

Babban abinda ya girgiza BJP ya zo a Uttar Pradesh inda ta sa ran samun nasara sama da ta 2019 d ata samu kujeru 64 daga cikin 80; maimakon haka karkare da kujeru 33.

Kawancen jam'yyun Congress da Samajwadi sun taka rawa wajen lashe kujeru 42. Ana yawan yi wa SP kallon jam'iyyar da ta samu karfi da goyon baya daga jama'ar Musulmai da al'umun da suke ci baya a yankin Yadavs, a yanzu ta samu babban sauyi, shugabanta ya yi duba na tsanaki wajen tsayar da 'yan takara inda ya zabi wadanda suka dace.

Kwalliya ta biya kudin sabulu inda SP ta lashe kujeru 37, inda ta zama jam'iyya ta uku mafi girma a majalisar dokoki.

Sakon 2024 a bayyane yake karara: Za a iya karya duk wani kudirin Modi. Adadin zai fi amfanar NDA da MJP ke wa jagoranci.

Gogayyar siyasa ta dawo, kuma BJP ba za ta iya ƙwace 'yancin hukumomin dimokuradiyya ba.

Smita Gupta, 'yar jarida da ta lashe gasa da dama kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, har zuwa baya-bayan Babbar Jami'a ce a Cibiyar Nazarin Siyasa ta Hindu, kuma kafin sannan ta rike mukamin Babbar Edita a jaridar The Hindu. Ta kuma yi a jaridu da dama da suka hada da Hindustan Times, Indian Express da The Times of India.

TRT Afrika