Falasdinawa a garin Nablus sun yi tattaki don girmama 'Yar Turkiyya-Amurka mai fafutuka Aysenur Ezgi Eygi. Hoto: Reuters

Daga Ahmet Yusuf Ozdemir

Duk wani da ke bibiyar mamayar Isra'ila ta shekaru 76 a Falasdin, na d amasaniyar me ke afkuwa.

Kan wannan gaba, Falasdin ta haura batun neman goyon bayan kasashe, wanda ake gani ta hanyar shirya zanga-zanga a kan tituna, don tabbatar da kanta a kwakwalen duniya.

Duk wani kalami na da za a yi ba iyakacin tutar Falasdin ko daurin kai na kefiyyah kadai ke kawo wa zukatan mutane ba, har da ma asalin mutane da ayyukan da ke yankin.

Shin hoto mai baki da fari na 'yar gwagwarmayar Falasdin da ke yaki Leila Khaled ne da kefiyyah da aka dora a kanta da kuma bindiga a hannun ta?

Ko kuma tsohon bidiyon shugaban Falasdinawa Yasser Arafat ne da yake yin shahararren jawabinsa a Zauren Majalisar Dinkin Duniya inda ya samu tafi mai karfi, "Yau na zo ina mai rike da reshen bishiyar zaitun da bindigar masu yakin kwatar 'yanci. Kar ku bari wannan reshe ya fado daga hannuna. Ina maimaitawa. Kar ku bari wannan reshe ya fado daga hannuna."

Tirjiya daga tushe

A yayin da tirjiya ga mamayar da Isra'ila ke yi ta zama mai tushe tsawon shekaru tare da koma wa zanga-zanga a kan tituna, ya zama wani bangare na abubuwan da aka saba gani a hotuna da bidiyo na yara kanana na jifan tankunan yaki da duwatsu.

Misali, a lokacin Intifada ta farko da ta dauki tsawon shekaru shida (1987-1993), Ramzi Aburadwan mai shekaru takwas ya zama alamar nuna tirjiya.

A lokacin da tsaka da tattaunawa game da "dabarun nasarar yaki ba tare da fada ba", hotunan matasa, ba wai na shahararru ba, sun zama sabuwar ilhama da karfafa gwiwa ga al'ummu masu zuwa.

A lokacin Intifada ta biyu, wadda aka sani da sunan Al Aqsa Intifada, makomar wasu yara maza biyu, Muhammad al-Durrah da Faris Odeh, ta girgiza duniya. Muhammad da mahaifinsa, Jamal al-Durrah sun tsinci kansu a tsakiyar masu musayar wuta na Isra'ila da masu tirjiya na Falasdin a Gaza.

A yayin da mahaifinsa ke ihu tare da kare dansa daga lamarin, kyamarori sun nuna Muhammad mai shekara 12 na rasa ransa. Haka zalika Faris dan shekara 14 da ya rasa ransa ta hanyar harbin da sojojin Isra'ila suka yi masa saboda jifan su da dutse.

Shekaru da dama wuce bayan afkuwar wadannan al'amura, amma bakin littafin Isra'ila ya kara fadada inda take ci gaba da kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba, tun daga Shireen Abu Akleh sanannen dan jarida mai shekru 51, zuwa Hind Rajab mai shekaru shida, wanda wayar da aka yi da ita ta karshi aka je tana kira da a zo a taimaka mata.

'Yan sandan Isra'ila sun kai kan taron jana'izar Abu Akleh, kuma binciken da aka gudanar ya nuna yadda sojojin Isra'ila suka harba harsashai 335.

Abin takaici, wannan dabbanci bai dakata daga nan ba, kuma ba Falasdinawa kawai suke hara ba, har ma da duk wadanda suka nuna goyon baya gare su.

Fararen hula daga yankuna daban-daban na duniya sun je tare da zama da Falasdinawa. Wasun su sun fada komar dabbancin Isra'ila.

Misali na baya-bayan nan shi ne 'Yar Amurka-Turkiyya mai shekara 26 Aysenur Ezgi Eygi. Mamba ce a Kungiyar Gwagwarmayar Kasa da Kasa (ISM) ce, wadda tun 2001 take ayyuka a Falasdin.

Sojojin Isra'ila sun kashe Eygi a ranar 6 ga Satumban nan a a lokacin da suke zanga-zanga tare da abokan aikinta don nuna adawa ga mamayar Yammacin Kogin Jordan da Isra'ila ke yi.

Ba Eygi kadai ba ce mai fafutukar ISM da sojojin Isra'ila suka kashe a Falasdin. A gefe guda kuma, ISM ta zama a sahun gaba a labaran jaridu shekaru biyu bayan kafa ta a 2003, a lokacin da wata tankar yaki ta kashe mai fafutuka dan Amurka Rachel Corrie mai shekaru 23, a lokacin da take zanga-zangar adawa da rusa gidajen Falasdinawa da Isra'ila ta yi.

Ko akwai wani abu da Isra'ila take yi da "gan-gan"?

Tarihin mamayar shekaru sama da saba'in na mamaya da tirjiya na cike da irin wadannan misalai da dama.

Duk da haka, a yayin da labarai a al'amura ke sauyawa a kowace rana, ana iya manta wa da martanin Isra'ila abubuwan da suka shafi

An ga wannan abu karara sosai bayan kashe Eygi a yayin da sojoji da shugaban Amurka Joe Biden duk suka ce lamarin 'hatsari ne' kuma "an harbe ta bisa kuskukure ko ba da gangan ba".

Wannan na iya baiwa wasu mamaki, amma ya zama manufar Isra'ila dora laifi kan wanda ta kashe da cewar ya je wajen da bai kamata ba.

Domin kaucewa tambayar mamaya da aka tsara yin ta, Isra'ila na yin kokari sosai na kalubalantar irin wadannan bayanai.

Kisan Muhammad al-Durrahh misali ne da za a iya kalla kan wannan batu.

Bayan daukar alhaki da fari, Isra'ila ta yi ikirarin cewar harsashin da Falasdinawa suka harba ne ya kashe al-Durrahh. Sun ma dinga fadin cewar wai mayakan Falasdinawa ne suka janyo rikicin, mai daukar hoto da mahaifin Muhammad.

A batun Rachel Corrie kuma, wannan manufa ta ci gaba.

Mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila ya bayyana masu gwagwarmaya na ISM da "mutanen da ba sa bin ka'ida kuma suke jefa rayuwar kowa cikin hatsari - Falasdinawa, su kansu da dakarunmu - ta hanyar kai kawunansu yankunan da ake yaki a ciki."

Duk da cewar tankar yaki ce ta bi ta kan Corrie, matukinta ya ce shi bai ga hakan ba. Daga baya, wani alkalin kotun Isra'ila bayan iyalan Corrie sun kai kara ya yanke hukuncin cewar ita ce ta kai kanta waje mai hatsari.

A lokutan kisan kiyashi, Isra'ila ba ta sauya wannan manufa.

Harin da ya afku a ranar 17 ga Oktoba a Asibitin Larabawa na Al Ahli ya zama babban batu a lokacin.

Maimakon a bayar da dama ga masu binciken kasa da kasa, Isra'ila da kawayenta sun yi gagawar cewa ba Isra'ila ce ta tayar da bam din ba, Falasdinawa ne ta hanyar nazari kan hotunan.

Isra'ila na son wadanda ke bibiyar al'amuran su yarda da labaran da bangaren Isra'ila ke fada, amma na bangaren Falasdin 'karerayi ne'.

Wannan na barin tambayoyi da dama a baya da aka gaza amsa su, musamman ma irin wadanda suka cancanci a soke su tare da gudanar da bincike kan ko Isra'ila ta aikata wani babban laifi da gangan.

Marubicin wannan makala Ahmet Yusuf Ozdemir, Mataimakin Farfesa ne a Sashen Nazarin Kimiyyar Siyasa da Alakar Kasa da Kasa na Jami'ar Ibn Haldun.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar tunani ko ra'ayoyin tsarin iditocin TRT Afrika ba.

TRT Afrika