Daga Fawaz Turki
A wajen jama'ar Gaza, yau rana ce mai girma a tsakanin ranaku. kisan kiyashi da bala'in da suek ta fuskanta na tsawon kwanaki 470 zai kawo kashe - a kalla a yanzu. Tabbas yanzu kawai.
Sai dai idan ka zama mai saka rai dari bisa dari ko wanda ke da baiwar yaudarar kansa ne za ka yi tunanin cewar saboda wai an tsagaita wuta a ranar Laraba - da aka karya a ranar Alhamis - Isra'ila za ta kawo karshen kisan kiyashin da take yi wa mutanen da ke zaune a dan karamin tsibiri.
A Gaza, mamata - ciki har da dubunnan da ba a gano da da ke karkashin burabugazan gine-ginen da aka rushe ne suka ga karshen yaki.
Rayuwar da za su ci gaba da fuskantar bacin rai da hantara daga Yahudawa, matukar dai sun ci gaba da wanzuwa a matsayin Falasdinawa - matakin nuna adawa da Yahudawa suke da shi tun bayan fara mamayar Falasdin kusan shekaru 80 da suka gabata.
Amma tsagaita wuta sunanta tsagaita wuta, kuma jama'ar Gaza sun yi maraba da ita, haka ma duk wadanda ma suka rasa 'yan uwansu ko aka raba da matsugunansu.
Duk suna nan a ranar Talata, suna bayyana tsagwaron farin ciki da annushuwa, a kan titunansu da ke cike da buraguzan gine-gine sun bayyana tsantsar jin dadinsu.
Amma kuma wannan sauki da farin cikin da suke da shi ba shi da tabbas sosai.
Eh, gaskiya ne, Falasdinawa sun yi maraba da tsagaita wutar, kamar yadda dukkan magoya bayansu na duniya suka yi, duk da sun san wannan ba irin tsagaita wutar 24 ga Nuwamban 1014 ba ce, a lokacin da sojojin Faransa, Ingila da Jamus suka dinga murna a tsawon makonni har zuwa bikin Kirsimeti, suka dinga musayar gaisuwa a tsakaninsu. Sun ba zai taba zama abu irin haka ba.
A ranar Laraba, kwana guda kafin sanya hannu kan yarjejeniyar, kuma kwanaki kafin fara aiki da ita a aikace, sojojin Isra'ila sun kai hare-hare ta sama a tsakiya da arewacin Gaza da ya yi ajalin mutane 123, ciki har da yara kanana 33 da mata 33, wasu sama da 270 kuma sun samu raunuka.
Wannan na bayyanawa karara cewa kasar Yahudawan nan ba wasu cikakkun mutane ba ne. SHin ta yaya za a iya kare kai hare-haren?
Yarjejeniya mai rauni
Idan aka kalli yanayin da ake ciki, ba za a iya cewa yarjejeniyar tsagaita wutar za ta dade har ta shiga bangare na uku tare da kai wa ga janyewar sojojin Isra'ila daga yankin.
An bayar da rahoton cewar yarjejeniyar tsagaita wutar na cike da rudani, kuma masu shiga tsakanin da suka rubuta ta sun yi gaggawa saboda sun zaku ne su kammala don su burge.
Sannan ga kawancen gwamnati marar tabbas, mai kuskure da rashin kan gado a Isra'ila, wanda firaministan yake da tsaurin ra'ayi da kowa ya sani, wanda ayyukansa suke bayyana tsagwaron taurin jama'ar Isra'ila da kazamar siyasar Isra'ila a zamanin yau.
Ba za a iya cewa wadannan mutanen, matukar suna nan a kan kawancensu, ba za su ci gaba da yin barazana ga yarjejeniyar tsagaita wutar a dukkan matakai wuku da ta kunsa ba, wanda kowanne mataki na shi da tabbas.
Matakin farko - musayar fursunoni - shi ne mafi sauki, bangare mafi ma'ana. Sannan sai wana ke da wahalar yiwuwa, kashi na biyu marar fasali da kan gado na batun janyewar sojojin Isra'ila daga Gaza, sannan a baiwa dubunnan daruruwan 'yan Gaza damar dawowa gidajensu.
Ka ce me yanzu? 'yan Gaza su koma gidajensu? Wadanne gidajen?
Babu gidajen da suka rage a Gaza—a yanzu wajen ya zama matattarar bola da tarkace a tarihin yau, wanda ya yi kama da yankin Rumawa na 146 BCE, da Baghdad a lokacin da Mogulawa suka fatattake su a 1258.
Mummunan hali
Wannan mummunan yanayi, kamar yadda Cibiyar Tauraron Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya (UNOSAT) ta yi kiyasi, ya ta'azzara matuka: kuma a takaice an rusa gidaje 257,800 a Gaza, inda kusan kashi 95 na jama'ar yankin su miliyan 2.3 suka rasa matsuguni - wannan baya ga rusa masallatai, makarantu, shaguna, asibitoci da cibiyoyi da gangan, da kuma tayar da bama-bamai a gine-ginen gwamnati, kamar jami'o'i da sauran su.
Bari dai a takaice, idan da a ce za a tattare burbushin gine-ginen, kowanne guda zia kai tudun Giza na Pyramid da ke Masar.
Ko a iya cewa an rusa gine-gine a Gaza sama da ninki uku na gidajen da ke tsibirin Manhattan a New York.
Sannan aikin zubar da wadanan buraguzai kadai zuwa yankin da ke wajen zirin na Gaza ba karami ba ne - an bayyana cewar wannan aiki zai dauki tsawon shekaru 14 ana yin sa - kafin Falasdinawa su samu damar fara sake gina gidajensu, wanda aka yi hasashe a bangare na uku na yarjejeniyar.
A makon da ya gabata, Antony Blinken da ke shirin barin kujerar Ministan Harkokin Wajen Amurka ya yi jawabi - inda ya yi kokarin kitsa ayyukansa a matsayin wanda ya kitsa ta'annatin Isra'ila a Gaza - ga wasu jama'a da suka taru a Majalisar Atlantika, inda ya yi magana kan sake gina yankin da shugabancinsa.
Wanne fata ya rage?
Ko wannan yarjejeniyar mai nauyi za ta zama farkon kawo karshn balahirar Gaza? Abin takaici, amsar ita ce a'a.
A wani waje a Gaza a yau, rana da ake sa ran makamai masu linzami da manyan bama-bamai za su daina sauka kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba, za ku ga akwai yaron da ke gararamba yana fada wa kansa: "Ina jin yunwa. Ni kadai ne. Ba ni da tsaro. Ina jin sanyi."
Ba tare da magance tsananin zaluncin da aka shirya shi tuntuni ba, kullle kofofin habakar tattalin arziki, da mummunan yanayin siyasa da ke bayyana irin rayuwar da ake yi a Gaza, wannan tsagaita wutar na neman zama wata madakatar rikicin da ya gaza zuwa karshe.
Domin tabbatar da wanan tsagaita wuta ta magance farko da karshin bakin cikin Gaza, dole a dauki kwararan matakai. Dole a janye kawanyar da aka yi wa yankin. Dole ne a tuhumi wadanda suka aikata laifukan yaki. Sannan a kawar da musabbabin wannan rikici - mamaya, tsugunarwa da hana kafa kasar Falasdinu. Duk abinda ba wadannan ba, zai sake jefa Gaza cikin tsaka mai wuya.
An haifi marubicin wannan makala, Fawaz Turki a Haifa a shekarar 1940, kuma ya gudu tare iyalinsa zuwa Lebanon bayan rikicin 1948 inda a yanzu ya zama dan jaridar Falasdin-Amurka, malamin jami'a a kuma marubici da ke Washington DC. Rubuce-Rubucen da ya yi sun hada da litattafan 'the autobiography The Disinherited: Journey of Palestinian Exile (1972), Soul in Exile (New York, 1988) da Exile’s Return: The Making of a Palestinian-American (New York, 1995).'
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga, da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.