An ga wakiliyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield a ranar kada da kuri'a kan kudurin Gaza kan a tsagaita wuta nan take a hedkwatar MDD da ke birnin New York, Maris 25, 2024. / Hoto: Reuters  

Daga Assal Rad

Bayan fatali da ta yi da kudurori uku na Majalisar Dinkin Duniya kan neman a tsagaita wuta a Gaza, daga karshe Amurka ta ƙaurace wa kaɗa ƙuri'a a sabon ƙudurin tsagaita wuta wanda zai ba da damar a aiwatar da shi.

Kudurin ya nuna tsayin- dakar Amurka da kuma ta da kayar baya daga Isra'ila karkashin Firaiministan kasar Benjamin Netanyahu wanda ya gaggauta dakatar da wata tawaga da aka shirya zuwanta Amurka bayan da ta kaurace amfani da karfin ikonta a karo na hudu.

Sai dai gwamnatin shugaba Joe Biden ta yi saurin watsi da zargin tana mai ƙasƙantar da muhimmancin ƙudurin.

Sa'o'i kadan bayan zartar da kudurin, mai magana da yawun fadar White House John Kirby ya bayyana cewa kauracewar Amurka "ba ya wakiltar wani sauyi a manufofinmu."

Sannan a wani taron manema labarai da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta shirya bayan zaben Majalisar Dinkin Duniya, mai magana da yawun kasar Matthew Miller ya yi ikirarin cewa "kudirin ba shi da," yana mai bayyana matsayin Amurka a fili tare da ba da shawarar cewa kudurin tsagaita bude wuta zabi ne na Majalisar Dinkin Duniya, maimakon wani muhimmin doka.

A wata muhimmiyar tattaunawa da aka yi da Miller, wakilin kamfanin dillancin labarai na Associated Press Matt Lee ya gabatar masa da wata tambaya da mutane da dama suke son yi game da yakin da Isra'ila ke yi a Gaza: “Mene ne alfanun Majalisar Dinkin Duniya ko Kwamitin Tsaro na Majalisar?

Masana da masu sharhi, irin su tsohon jami'in Majalisar Dinkin Duniya kuma lauyan kare hakkin bil'adama Craig Mokhiber, cikin hanzari suka soki Amurka saboda matsayinta na ƙankastar da ƙudurin, wanda tuni ya bayyana rauni da ke ciki saboda kawai an nemi a "tsagaita wuta a cikin watan Ramadan" wanda ga alamu zai iya kaiwa ga "tsagaita wuta mai ɗorewa."

Mokhiber ya ja hankalin kafofin yada labarai a watan Oktoban 2023 bayan ya yi marabus daga mukaminsa na daraktan Ofishin hukumar kare hakkin dan'adam na MDD a birnin New York, yana mai nuni kan gazawar Majalisar Dinkin Duniya na kawo karshen "batun kisan kiyashi" a Gaza.

Yayin da harshen kudurin ya bukaci sassauci, matakin ya samu yabo daga MDD saboda tsananin bukatar da ake da ita na magance matsalar jinƙai a Gaza, wanda hada da tsananin yunwar da ba a taba gani ba, a cewar shugaban kwamitin ceto ta kasa da kasa David Miliband.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a karara ya bayyana cewa kudurin ba wai sanarwar ba ce kawai ba, "dole ne a aiwatar da shi" kuma rashin yin hakan zai zama "abin da ba za a gafarta ba."

Sai dai da manema labarai suka tambaye shi ko yana ganin kudurin zai sa Isra'ila ta sanar da tsagaita wuta, Miller ya ba da amsa da cewa, "Ban sani ba."

Ko shakka babu zartar da kudurin tsagaita wuta na MDD na da matukar muhimmanci. Zai kara bayyana matsayar shari'a kan Isra'ila game da ayyukanta a Gaza da kuma cancantar shari'a ga zarge-zargen da ake yi wa ƙasashe da ke mara mata baya - kamar Amurka - waɗanda ke ci gaba da ba da makamai da goyon baya ga Isra'ila a "yakinta na kisan kare dangi".

Kamar hukuncin da kotun duniya ta yanke a watan Janairu, ƙudurin tsagaita wuta na MDD ya kara fito da ƙwararan shaidu da wajibcin shari'a kan Isra'ila da masu goyon bayanta na kin dakatar da yaki a Gaza, wanda kawo yanzu ya kashe Falasdinawa sama da 32,000 tare da wasu dubbai da ba a gansu ba kana suna karkashin baraguzai .

Wata Mage ta tunkari wata mata da ke zaman makoki a gaban gawarwakin 'yan uwanta da aka kashe yayin harin bam da Isra'ila ta kai a cikin dare, a asibitin Al Najar da ke Rafah a kudancin Gaza a ranar 26 ga Maris, 2024 (AFP/Mohammed Abed).

A gefe guda kuma, masu suka sun yi daidai da tambaya kan batun muhimmancin wadannan matakai bayan a zahiri abubuwan da suke faruwa ba su sauya ba kan Falastinawa.

Isra'ila ta dade tana watsi da dokokin duniya a tsawon shekaru inda ta ke ci gaba da mamayar Falasdinu da nuna wariyar launin fata da fadada matsugunanta da kuma kwace filaye a Yammacin Gaɓar Kogin Jordan da ta mamaye tare da killace Gaza da kuma kyale tashe-tashen hankula a tsakanin mazauna yankin da aikata laifukan yaki da kuma jerin wasu laifuffuka masu yawa.

A yanzu haka dai, Isra’ila ta matukar raina dokokin duniya da ‘yancin dan Adam, inda harshenta ya yi daidai da ayyukan kisan kare dangi da kuma hana kai agaji da gangan zuwa Gaza lamarin da ya haifar da yunwa mai tsananin.

To, menene manufar Majalisar Dinkin Duniya ko Kwamitin Tsaronta? Wadda aka ƙirƙira bayan yakin duniya na biyu.

Muhimman ƙa'idodin Majalisar Dinkin Duniya dai shine kare al'ummomin da ke tafe daga bala'in yaki da kuma tabbatar da an kare hakkokin ɗan adam a tsakanin dukan al'ummomin duniya.

Yayin da hukumar ta ke da wannan matsayi na kafa dokoki da kuma ba da shawarar matakan da ake bukata, abin da ya rage wa kasashe shi ne su aiwatar da su.

Yayin da ita kanta Isra'ila ta nuna rashin mutunta tsarin dokokin duniya, nauyi ne da ya rataya a wuyan sauran kasashe-musamman masu goyon bayanta- su daura mata alhaki.

The Biden administration’s willingness to isolate the US on the global stage, destroy any vestige of US credibility, and essentially ignore the international community shows a dangerously zealous face of US foreign policy.

Duk da matsayar hukumomin duniya kamar Kwamitin Tsaro na MDD da Hukumar Lafiya ta Duniya, da Kotun Shari'a ta Duniya, da kuma shaidar ƙwararrun MDD, da kuma shaidudaga kungiyoyin agaji da na kare hakkin ɗan'adam kamar Doctors Without Borders da Oxfam International da kuma Human Rights Watch.

Sannan kuma da bayanan shaidu da 'yan jaridu da ma'aikatan agaji a Gaza suka tattaro, Amurka na ci gaba da kare ayyukan Isra'ila tare da musanta aikata ba daidai ba.

Ta hanyar amfani da MDD a matsayin hukumar kare manufofinta na siyasa, maimakon wacce ke samar da dokokin kasa da kasa da adalci, Amurka ta mayar da hukumar mara ma'ana.

Burin gwamnatin Biden na keɓe Amurka a fagen duniya, ya ruguza duk wata kima ta kasar, da kuma yadda ta yi watsi da al'ummar duniya ya nuna hatsarin da ke tattare da manufofin tsarin Amurka, Halin gaskiya a bayyane yake babu shakka.

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.

TRT Afrika