Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi (R) na yin maraba da shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud a fadar Ittihadiya ranar 21 ga watan Janairun shekarar 2024. / Hoto: AFP      

Bisa ga dukkan alamu wani gungun ƙasashen ƙahon Afrika masu adawa da Habasha yana sa wa a ɗan ji dama dama. Masar, wacce tsawon shekaru ke sa-in-sa da Addis Ababa a kan madatsar ruwa ta Grand Ethiopian Renaissance Dam (GERD), tana fakewa da wannan damar ta ci karanta babu babbaka.

Alƙahira, wacce ƙaruwar tasiri da ƙarfin faɗa-a-jin da habasha ke da shi kan madatsar ruwa ta GERD ke ci wa tuwo a ƙwarya, ta zaƙu ta ƙarfafa dangantakarta da ƙasashen Afrika kamar Eritrea, da Sudan da kuma Uganda. Masar na da aniyar karfafa goyon bayan ƙasashen yanki da take samu kan matsayarta game da rikicinta da Addis Ababa kan GERD.

Tun shekarar 2011, Habashawan ke aiki kan katafariyar madatsar ruwan ta GERD mai jawo ce-ce-ku-ce, wacce suke kallo a matsayin muhimmiya ga cigaban ƙasarsu. Kwanan nan Habasha ta kammala aikin mataki na biyar na cike wajen ajiye ruwa a madatsar ruwan ta GERD kuma mahukunta a Addis Ababa na da ƙwarin guiwa game da madatsar ruwan mai samar da wutar lantarki za ta fara aiki sosai a shekarar 2025.

"Yanzu an kusa gama aikin madatsar ruwan," Firaminista Abiy Ahmed ya bayyana a watan da ya gabata. Madatsar Ruwan ta GERD za ta samar da wutar lantarki wa miliyoyin gidaje a Habasha.

Addis Ababa ta ce, Madatsar Ruwan ta GERD, aikin samar da wutar lantarki na dala biliyan $4 da ke da ƙarfin samar da wuta megawat fiye da 6,000 tana da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziƙinta.  [FILE] / Photo: Reuters

Amma Misirawan na kallon GERD a matsayin wata barazana ga rayuwarsu saboda yadda ƙasarsu ta dogara da rafin domin samun ruwa. Masu tsara manufofi a Alƙahira suna nuna damuwa game da tasirin datse ruwan kan gudanarsa, musamman ma idan aka yi fari na tsawon shekaru.

Kulla yarjejeniya

Sakamakon haka, an samu labari a watan da ya gabata cewa, Masar ta bai wa Somalia gudummawar makamai a karon farko a cikin shekaru 40 sannan kuma suka ƙulla yarjejeniyar tsaro ta Alƙahira/Mogadishu.

Sai kuma a ranar 23 ga watan Satumba, wani jirgin ruwan yaƙi na Masar ya ya da zango a tashar jiragen ruwa ta Mogadishu domin jibge makamai irin su atilare da bindugun harbo jiragen sama.

Masar har wa yau ta buƙaci ta bayar da gudunmawar sojoji 10,000 ga sabon shirin kiyaye zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) a Somalia da aka shirya kaddamar wa a 2025.

Labarin miƙa wannan buƙata da Masar ta yi na iya ta'azzara zaman tankiya idan aka yi la'akari da mummunar adawa da Habasha ke yi da duk wata gudunmawa kamar ta tura sojoji da Masar ta yi zuwa Somalia, inda Addis Ababa jigo ce a fuskar tsaro.

A halin da ake ciki, Somalia da Habasha suna da kyakkyawar alaka a shekarun baya bayan nan. Amma a farkon watan Janairun, mahukunta a Addis Ababa sun ɓata wa kakwarorinsu na Mogadishu rai ta hanyar ƙulla yarjejeniya da Somaliland ta ginginar da gaɓar tekun ga Habasha.

Hakan, kamar yadda ake faɗa, ya bai wa ƙasar Afirkan wacce ba ta da teku, damar yin amfani da tekun Red Sea da kuma Gulf of Eden, a musayen cewa Addis Ababa ta yarda da ɓallalliyar jamhuriyar a matsayin ƙasa mai cikakken ƴanci.

A mahangar Mogadishu, yarjejeniyar ta Habasha/ Somaliland ta keta haddin Somalia a matsayin ƙasa mai cikakken ƴanci. Mogadishu ta lashi takwabin kawo wa yarjejeniyar cikas, abin da zai iya sa wa Habashawan su samu tashar jirgin ruwa da kuma sansanin sojoji ruwa a Somaliland.

Ranar 20 ga watan Satumba, mahukunta a Mogadishu sun zargi takwarorinsu na Addis Ababa da keta haddin ƴancin cin gashin kai na Somalia, ta hanyar shigar da makamai babu izini, yankin da ya ayyana kansa a matsayin ƙasar Putland mai cin gashin kai, wacce ke yankin arewa maso gabashin Somalia.

Su ma mahukunta a Alƙahira sun yi adawa da yarjejeniyar ta Habasha/Somaliland, suna mata kallo a matsayin barazana ga muradun ƙasa na Masar.

A ranar 22 ga watan Satumba, ofishin jakadancin Masar a Somalia, yayin da yake bayar da misali da yanayi na rashin tabbas ɗin tsaro, ya yi kira ga ƴan ƙasar Masar da su fice daga Somaliland ba tare da ɓata lokaci ba.

"Masar ta damu ne da da yunkurin Habasha na samun iko da mashigar ruwa ta el-Mandeb, abin da ke nufin za ta yi barazana da mashigun ruwa guda biyu na ƙasar: Mashigun Tekun Nilu da na Suez Canal," a cewar Yusuf Hassan, wani mai sharhi kuma mai bincike da ya ƙware a kan harkokin Afrika da yankin Gabas ta Tsakiya.

Da yake zantawa da TRT world, Hassan ya ce Masar na dafa wa ƙoƙarin Somalia, na ta zama nutsatssiya kuma ƴantacciyar ƙasa, domin ta rage kaifin barazanar da take tunani daga habasha, kuma ta karfafa wa ƙasar ta rungumi tafarkin ƙarin tattaunawa game da lamarin kogin Nilu.

Yanzu Alƙahira ke fahimtar cewa taurin kai da Habasha ke nunawa, a wani sa'in, saboda raunin da ƙasashen Somalia da Sudan suka yi ne, abin da ke bai wa Habasha damar yin abin da ta ga dama ba tare da fuskantar wani ƙwaƙƙwaran hukunci ba.

"Ƙaurace wa siyasar Afirka na tsawon fiye da shekaru 30 da Masar ta yi, musamman bayan yunkurin hallaka (tsohon shugaban ƙasa Hosni) Mubarak a Addis Ababa, wata babbar katoɓara ce, idan aka yi la'akari da muradun tsaron Masar a yankin ƙahon Afrika.

Yanzu Alƙahira ke fahimtar cewa wargin da Habasha ke yi, wani lokaci, saboda raunin da ƙasashen Somalia da Sudan suka yi ne, abin da ke bai wa Habasha damar yin abin da ta ga dama ba tare da fuskantar wani ƙwaƙƙwaran hukunci ba," ya jaddada.

Ita ma Eritrea wata muhimmiyar ɓangare ce a batun. Duk da ta shawo kan tsohuwar gabarta da Habasha a ƴan shekarun baya, ta ƙulla ƴar takaitaciyar kyakkyawar alaƙa, tsohuwar gabar tsakanin Asmara da Addis Ababa na sake farfaɗowa. A wannan gaɓa, masharhanta sun ce yaƙi na iya ɓarkewa tsakanin ƙasashen biyu.

Muhalli Mai Hatsari

Idan aka yi la'akari da zaman tankiya da ke ƙaruwa a yankin, masana sun yi kashedin yiwuwar yanayi mai hatsari da ka iya faruwa yayin da ake cigaba da zamar da Habasha saniyar ware, duk da goyon baya da take samu daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

"Ɓagare mafi jan hankalin shi ne"canji waje" a gogayyyar tsakanin Masar da Habasha," in ji Federico Donelli, mataimakin Farfesa a ɓangaren nazarin dangantakar ƙasa da ƙasa a Jami'ar Trieste.

Da yake zanawa da TRT world, yace "Tsawon shekaru, maƙasudin hamayyar shi ne kogin Nilu, galibi saboda madatsar ruwa ta GERD. Yanzu da aka samu ƙaruwar tsoma bakin Masar a cikin harkokin Somalia, maƙasudin rigimar na komawa kan Bahar Maliya.

Hatsarin shi ne daga Masar ɗin har Habasha ba wanda zai iya magance rikici a waje mai tanga-tangal kamar Somalia. Sakamakon haka, akwai hatsarin cewa abubuwa za su iya rincaɓe musu su biyun.

Da wuya a yi amfani da Diflomasiyya

A yanzu, Masar na sake nazarin manufofinta na ƙasashen waje dangane da yankin ƙahon Afrika, kuma tana amfani da wata dama a Somalia ta matsa wa Addis Ababa lamba yayin da aikin madatsar ruwan ya kusa kammaluwa.

Muhimmin abin da za a sa ido a gani shi ne yadda Addis Ababa za ta mayar da martani kan abin da musamman ta ɗauka takalar faɗa ne Masar ke yi.

Ko ma dai yaya wannan zaman tankiyar zai kasance, za a iya cewa, bayan jerin tattaunawa da yawa da ba su yi nasara ba a baya, yiwuwar samun mafitar diflomasiyya a kan batun madatsar ruwa ta GERD za ta disashe ne kaɗai a irin wannan tirka-tirkar.

Kamar yadda William Davison, edita kuma mamallakin shafin Ethiopia Insight website, ya jaddada cewa ƙaruwar ƙawance tsakanin Masar da Somalia, ko shakka babu, zai sa Habasha ta ga babu buƙatar ta bayar da ƙarin haɗin kai kan batun madatsar ruwa ta GERD da ma duk wani aiki a nan gaba a kogin Nilu fiye da wanda ta cimma da Alƙahira.

Masar dai ta shirya wajen yin amfani da ƙasashen yankin kamar Eritrea da Somalia ta ƙalubalanci Addis Ababa sannan kuma ta yaƙi muradunta.

Yayin da ake fargabar tashin hankali a fakaice tsakanin Masar da Habasha zai ta'azzara zaman tankiya a yankin zuwa wani mataki, babban abin takaici ne a yi tunanin cewa, mayuyacin abu ne Alƙahira da Addis Ababa su iya cimma masalaha.

Marubucin, Giorgio Cafiero shi ne babban jami'in Gulf State Analytics (@GulfStateAnalyt), wata cibiyar tuntuɓa kan kasadar wurare mai mazauni a Washington DC.

Togaciya: Ra'ayoyin da wannan marubucin ya bayyana ba dole ba ne ya zo daidai da ra'ayi, hange da manufofin TRT Afrika ba.

TRT World