Jinjina wa kewar 'Masar da ta haɗa kowa da kowa' ya kai har ga ayyukan fasaha. Hoto: Getty Images

Daga Omar Abdel-Razek

Game da batun dawo da wannan kewar, shahararren fim ɗin nan na Youssef Chahine mai suna Alexandria, Why? (1979) mafi shaharar aikin fasaha da aka ƙirƙira.

Tun Shekaru Goma na ƙarshen ƙarni na Ashirin, kewar tarihin zamanin mulkin mallakanta ya kama Masar a ƙarƙashin laƙabin "Masar da ta haɗa kowa da kowa".

Bisa hangen Chahine, fim ɗin na nuni ne da wani buɗaɗɗen birni wanda a cikinsa Yahudawa da, Italiyawa,da Girkawa da kuma Misrawa suke zaune lafiya da juna a zamanin yaƙe yaƙen duniya na ɗaya da na biyu.

Fim ɗin na nuni da wannan kwaikwayon rayuwar kamar yadda ta fuskanci barazana daga nausawar Jamusawa zuwa cikin 'Hamadar Yammaci' lokacin yaƙin El Alamein (1942) wanda ya tilasta wa mutane dayawa su tsere domin neman tudun- mun-tsira.

Shekaru Talatin daga bisani, an sanya kewa makamanciyar wannan a cikin fim ɗin Haliopolis na shekarar 2009 - wannan karon ta hanyar bayyana irin makomar cikin garin Haliopolis.

Wani hanshaƙin mai sana'ar gine-gine ɗan ƙasar Belgium ɗin nan, Édouard Louis Joseph, ya gina ta a gabashin Alƙahira, anguwar ta 1st Baron Empain Heliopolis an yi niyyar ta zama wata katafariyar anguwar bayan gari ga ƴan bokon Masar, da hanshaƙan Yahudawa da kuma Turawan yamma.

Wannan biki na 'Masar da ta haɗa kowa da kowa' bai taƙaita ga Silima da wasan kwaikwayo ba. Mafi shahara, ta bayyana a littafin Zube mai suna No One Sleeps In Alexandria, wanda marubucin littattafan zube ɗan asalin Alexandria, Ibrahim Abdel Meguid ya rubuta, da kuma ayyukan Marigayin marubucin zube, Edward Al-kharrat, musamman littafin zubensa na 1991, City Of Saffron.

'Ƙagaggiyar Al'ada'

Kewar Masar da ta haɗa kowa da kowa ta ƙara yaɗuwa tsakanin al'ummar Masar tsawon lokaci saboda bunƙasar fasahar zamani cikin hanzari da kuma tasirin yin amfani da intanet.

Hoton wata gada a birnin Alkahira na Masar. / Hoto: Getty Images

Yanzu dai bai taƙaita ga da'irar ƴan boko ba kaɗai, ya kai ga mutane gama-gari ta dandalolin soshiyal midiya, inda suke nuna takaici game da mummunan yanayin da ake ciki yayin da kuma suke kewar rayuwar da mai daɗi.

Shafuka da aka sadaukar wa sarakunan da suka shuɗe da kuma kyawawan titina, da dandaloli, da kuma fadoji da aka ƙawata da shuke shuke, a farkon shekarun ƙarni na Ashirin, manyan alamu ne da ke tunatarwa game da taɓarɓarewar biranen Masar a tsawon lokaci.

Amma dai, ba haka kawai wannan al'amarin ya wakana a ƙarshen shekarun 1970, yayin da Masar ke sauyawa daga asalinta na Balarabiya kuma Ƴar Afrika da Gamel Abdel Nasser da kuma Juyin-juya-halin ranar 23 ga watan Afrilu suka yi daga wani wajen.

A kyakkyawar dangantakarsa da Amurka da kuma rattaba hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila, magajin Naseer, Anwar Sadat, ya zaƙu ya samar da sabuwar al'adar Misirawa - wacce ke kallon Turawan Yamma a matsayin abokanai da kuma Yahudawa a matsayin abokan zama da suke da tunani a al'ummace tare da Misirawa a da can - ko da kuwa gaskiya ta saɓa da wannan ra'ayin.

Turawan Yamma da ba sa wasa da wata dama

Masar ba ita kaɗai ba ce wajen ara a yafa wannan ra'ayin. Galibin ƙasashen Arewacin Afrika da na kudu da Sahara da ke fama da taɓarɓarewar tattalin arziƙi da rashin samun nasara a ayyukan raya ƙasarsu, suna miƙa wuya kan buƙatar yin nazari game da mulkin mallakansu da ya shuɗe - cikin farin ciki.

Amma ra'ayin haɗa kowa da kowa ya bujuro da "al'adar ƙirƙira" da zaɓaɓɓen tunanin wani zamani da bai taɓa wanzuwa ba a Masar ta zamani.

Mutuwar Muhammad Pasha ta buɗe ƙofofi wa Turawa da ba sa wasa wasa da wata dama su tuɗaɗo cikin Masar. Hoto: Getty Images

Ko da mun yarda da cewa haɗa ra'ayin kowa da kowa tsantsarsa yana yi wa mutane kallon su ƴan kowacce ƙasar duniya ne, a maimakon ƴan wata ƙasa ƙwara ɗaya, amma bai taɓa zama daidai da zamantakewar ƙasar da ake siffantawa a rubuce rubucen tsakiyar ƙarni na Goma Sha Tara ba.

Adadin ƴan ƙasashen waje da ke shiga Masar zamanin mulkin Muhammad Ali Posha kaɗan ne - galibinsu ƙwararrun da aka kawo su taimaka wajen zamanantar da ƙasar da kuma bunƙasa tattalin arziƙnta.

Mutuwar Posha ce da kuma raunin magadansa ne suka buɗe ƙofofi wa Turawan yamma da ba sa wasa da wata dama su tuɗaɗo cikin Masar dayawan gaske.

Sun dogara a kan amfanin tsarin dokar ƙasa da ƙasa da ta bai wa ƴan ƙasashen waje kariyar Shari'a da siyasa, da ta bai wa Turawan yamma ikon yin hukunci a kan ƴan ƙasarsu da ke zaune a Masar.

A wannan fuskar, Masar ba ƙasa da ta haɗa kowa da kowa ba ce, face wata al'umma ta al'ummomi da aka ware. Baƙi sun kasance sun can ƙolin matsayi, da ofisoshin jakadancinsu suka kare kuma kotunansu da tsarin shari'arsu ke musu hukunci.

Saɓani tafiya kan Jaki

Ɗaukacin tunanin mutane gama-gari ya ci karo da zaɓaɓɓen tunanin kewar Masar da ta haɗa kowa da kowa. Yaya mutum zai manta cewa an mamayi ƙasarsu na tsawon shekaru Saba'in saboda wani baƙo ya ƙi biyan kuɗin tafiya kan jaki?

Labarin na cewa ranar Goma ga watan Yuni a shekarar 1882, wani ɗan ƙasar Malta ya yi hayar jaki daga wajen wani Bamisre a Alexandria kuma ya buƙaci a kai shi rangadi da tsakar ranar Alexandria mai tsananin zafi.

Babu daɗewa sai taƙaddama ta kaure saboda kuɗin rangadin,sai ɗan ƙasar Maltan ya kashe ɗan Masar ɗin.

Ya tsere yankin Turawa a birnin - yayin da Misirawa suka bi mai laifin a wani ƙoƙarin ɗaukar fansar mutuwar mutumin garin, sai Turawa suka buɗe wuta, suka kashe gwamman mutane.

Jiragen yaƙin Birtaniya da ke jira a Teku Bahar Maliya daura da Alexandria, da ma sun yi barazanar kai mamayar sojoji domin su kare baƙi da ke birnin. Wannan shi ne ainihin abin da ya wakana.

An zamar da Misrawa koma-baya a cikin ƙasarsu. Hoto: Getty Images

A tsarin matsayi a rayuwa, Turawan ne ke gaba, sai Girkawa, da Yahudawan Yammacin Duniya sai kuma Siriyawa kiristoci. Misirawa su ne na can ƙasa.

A bayyane take cewa, a wancan lokacin, dayawan Misirawa ba sa cikin "Ƙasar Masar da ta haɗa kowa da kowa" ɗin kenan da yanzu ake sake bayar da labarin.

Haka kuma gine-ginen alfarma da manyan titunan ba su aka tanadar wa su yi shawagi sanye da Jaallabiyya da Abayarsu ba, tunda an killace su gabaɗaya a cikin unguwanninsu a Alƙahira da Alexandria, ko kuma ma a yankunan karkara na Masar da aka manta da su.

Kishin ƙasar Misirawa

Baƙi a Masar a Shekarun 1940, kamar yadda Edward Said ya bayyana a littafinsa mai suna Out Of Place (2000), suna zaune ne a killatattun tsibirai cikin anguwanni da tsarin rayuwa da ba su da nasaba da galibin Misirawa ta kowacce hanya.

Lokacin gwagwarmayar neman ƴanci a farko farkon ƙarni na Ashirin ya tabbatar da wannan banbancin.

Littafin Naguib Mahfouz mai suna Cairo Trilogy shi ne ko shakka babu littafi da ya fi kowanne bayyana wannan lamarin; ya bayyana gundumar Alƙahira da mazaunanta a matsayin wani gaurayen Misirawa ƴan kasuwa da masu aikin hannu, waɗanda baƙi suka danne, wato ƴan Birtaniya da sojojinsu.

Kuɓutarsu ba a ra'ayin haɗa kowa da kowa ba ne, illa a sabon "kishin ƙasar Masar", cibiya ɗaya mai sassaucin ra'ayi ga waɗanda suka ɗauki kansu Misirawa ba tare da nuni da dokoki ko kotunan da baƙi suka kafa ba.

Tuɓe wa baƙi irin waɗannan alfarmomin shi ne mafarin raguwar baƙi a Masar wanda ya tiƙe da juyin juya halin watan Yuli.

Wani ɓangare ne na matakan ƙwatar ƴancin kai. Ba tarihi ba ne ka ƙirƙiri wani ra'ayi "haɗa kowa da kowa" wanda galibin Misirawa ba su san shi ba a baya.

An fahimci cewa kewa na iya haifar da ƙirƙirar al'ada da take kallon abubuwan da suka gabata a matsayin masu kyau - ko da kuwa sauran bayanan ba masu kyau ba ne.

Marubucin, Omar Abdel-Razek masanin halayyar ɗan adam ne kuma tsohon edita a sashen Larabci na BBC. Yana zama a London Togaciya:

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba dole ba ne su zo daidai da ra'ayoyi da fahimta da kuma manufofin editan TRT Afrika.