Ra'ayi daga Jasmine El-Gamal
Yunƙurin kisan kai tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump a Pennsylvania a ranar Asabar ya rikirkita yaƙin neman zaben da ake gudanarwa na 2024, a lokacin da Jam'iyyar Democrat kuma ta rabu gida biyu kan ko Shugaba Biden zai nemi wa'adi na biyu ko kuwa ya haƙura kawai.
An fara gudanar da Babban Taron Jam'iyyar Republican a Milwaukee, Wisconsin a makon nan. Babban Taron Democrat kuma na nan tafe nan da wata guda. Dukkan 'yan takarar za su nemi a zabe su a kasar da kanta ya rarrabu.
A yayin da Trump yake samun goyon bayan jam'iyyarsa, musamman ma a awanni 48 da suka gabata; tambayar ita ce shin Shugaba Biden ma na iya samun wannan goyon baya daga 'yan Democrat har ta kai shi ga lashe zaben na watan Nuwamba?
Tun bayan rashin taɓuka abin kirki a wajen muhawarar 'yan takarar Shugaban Ƙasa da Biden ya yi, Jam'iyyar Democrat ta shiga rudani.
Katuwar muryarsa da yadda yake jinkiri wajen bayar da amsa da kalaman da ba a fahimta sun ɓata wa 'yan majalisar dokokin Democrat rai, haka ma manyan 'yan jam'iyyar da masu daukar nauyin ayyukanta ba su ji dadi ba, kuma sun yi kira ga Biden da ya janye daga neman sake tsayawa takara.
Amma a yayin da sakamakon jin ra'ayin jama'a ke bayyana, babu wani sabon tasiri game da karbuwar Biden a wajen masu jefa kuri'a, amma idan aka sauya dan takara, to hakan zai cutar da jam'iyyar maimakon amfanar da ita.
Shi kansa Shugaban Ƙasar ya bayyana cewar ba zai hakura da takarar tasa ba, ya nanata haka bayan gudanar da taron NATO a makon da ya gabata. Ya ce "Na taɓa kayar da shi zabe, zan kuma sake kayar da shi a karo na biyu."
Babu ƙarfafa gwiwa
Yadda Biden ya dinga kokarin tabbatarwa da magoya bayansa da abokan siyasarsa bayan muhawarar cewar zai iya ci gaba da takara, ya samu cikas da irin kalaman bayar da kunya da ya dinga yi.
Misali kiran Shugaban Ƙasar Ukraine da 'Shugaba Putin' da ya yi a yayin taron NATO a Washington DC, da kuma kiran mataimakiyar Shugaban Ƙasa Kamala Harris da sunan 'Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Trump'.
A karshen makon nan, kalaman Biden bayan yunkurin kisan Trump ya ba shi damar bayyana wa Amurka cewar zai iya yi kuma yana da ƙarfinsa, ya shirya kuma a tsaye yake da ya shugabanci kasar zuwa wani matsayi na gaba, inda ya yi kira ga kasar da ta yi watsi da rikicin siyasa.
Amma sakon nasa bai samu karbuwa a wajen magoya bayan Trump ba, wadanda ke ɗora laifin lamarin kan Biden da kansa, wanda ya riga ya tsorata da cewar Trump na iya lashe zabe.
A wani bayani da ya fita ga jama'a da ya yi ga masu daukar nauyin jam'iyyarsu, Biden ya bayyana bukatar da ke akwai ta ci gaba da kai hari kan bayanan Trump ta hanyar "bin diddiginsa".
Amma bayanan da ya yi wa kasar ya rage kiran da aka eyi masa, har a cikin jam'iyyarsa na ya janye daga takara.
A yayin da ya rage watanni hudu a gudanar da zaben Shugaban Ƙasar Amurka, kuma 'yan Jam'iyyar Republican suke sake samun karsashin goyon bayan Trump, ci gaba da samun rikici a cikin gidan Democrat zai cutar da jam'iyyar ne tare da illa ga damar sake komawarta mulki a watan Nuwamba.
Lokaci ya ƙure
A maimakon aiki don hade kan kokarin jam'iyya na kalubalantar Trump, batun kira ga Biden ya hakura da takara na bayyana irin raunin da yake da shi, saboda shekaru da raguwar ƙarfin hankali da rashin isasshiyar lafiyar jiki da halayya, ya zama batun da aka dinga tattaunawa a kafafen yada labarai tsawon awanni 24.
Wannan suka da ake yi wa Biden daga 'yan jam'iyyarsa, da kuma daga masu daukar nauyin jam'iyyar, ya kawo damarmaki da yawa ga masu kamfen din a zabi Trump.
Tsohon Shugaban Ƙasar ya bayyana ƙarara yana son Biden kar ya janye daga takararsa, hakan na nufin Trump ya yi amanna shi ke da cikakkiyar damar lashe zaben in dai Biden ya tsaya takara, maimakon wani dan Jam'iyyar Democrat.
Trump ya yi kira gare shi da Biden kan su yi gwajin kwakwalwa "don amfanin kasar".
'Yan kwanaki masu zuwan nan ne za su bayyana irin tasirin da yunkurin kisan gilla ga Trump zai yi ga 'yan takarar biyu a zaben da ke tafe.
A bangarensa, Trump ya ce ya soke shirinsa na jawabi a wajen Babban Taron Jam'iyya, inda ake tsammanin zai mayar da hankali wajen sukar Biden, inda ya mayar da hankali ga neman hadin kan kasa.
Sakamakon yadda kafafen yada labarai suka halarci Banna Taron Republican da yadda aka dinga tausaya wa Trump, akwai yiwuwar tsohon shugaban kasar ya sake samun dama, wanda hakan na iya kara masa ƙaimi a sakamakon da zai fito bayan zaben da zai kalubalanci Biden, (kuri'ar jin ra'ayin jama'a kafin yunkurin kashe Trump ta bayyana su kusan kai da kai).
Haka kuma, kwamitin yakin neman zaben Biden ya soke tallace-tallace da dama da taruka a yayin da shugaban da masu ba shi shawara suka sauya matsayar tunkarar Trump, sakamakon abinda ya faru.
A baya Biden ya mayar da hankali ga sukar Trump, yana mai gargadin wa'adin mulki na biyu ga Trump zai zama babbar barazana ga Amurka.
Salon yakin neman zabe da kalaman Biden za su iya canja wa a yanzu, ana ganin sakonninsa za su mayar da hankali ga hadin kai da adawa da rikicin siyasa.
Salon yakin neman zabe da kalaman Biden za su iya sauyawa a yanzu, ana ganin sakonninsa za su mayar da hankali ga hadin kai da adawa da rikicin siyasa.
Idan ban da kalaman Biden jim kadan bayan harin da aka kai wa Trump, da lamarin ya zama babbar matsala ga yakin neman zaben Biden.
Jam'iyyar Democrat da 'yan majalisar dokokinta da masu daukar nauyinta sun yi gaggawa wajen komawa ga gangamin zaben shugaban don sake samun tagomashi daga gangamin Trump.
Ko hakan na iya zama wata dama ga Trump? Sai dai a saka idon don ganin yadda za ta kaya.
Game da marubuciyar
Jasmine El-Gamal mai sharhi ce kan harkokin tsaron kasa kuma tsohuwar mai ba da shawara kan Gabas ta Tsakiya a Pentagon.
Ita ce ta kafa kuma Shugabar kamfanin Mindwork Strategies, LTD, wanda yake ba da shawara taimaka wa ƙungiyoyin kan hanyoyin jinƙai da hanyoyin al'adu ga manufofin waje da sadarwa da kula da lafiyar kwakwalwar mutane a wurin aiki.