Marubuciyar daga Afirka ta Kudu ta yi imanin cewa za a iya alƙinta harsunan Afirka ta hanyar rubutu da wallafa su. / Hoto: Mashudu Ravele

Daga Mazhun Idris

Ngũgĩ wa Thiong'o, marubuci ɗan asalin Kenya, kana masanin ilimi wanda ya kasance daga cikin ƙwararrun masanan kalmomi a rubutun harshen Turanci waɗanda ba su yi suna sosai ba, kafin daga baya ya rungumi harshensa na asali wajen rubuce-rubuce.

A wani taron lacca na shekarar 2017 da Jami'ar Witwatersrand da ke Johannesburg ta shirya, Thiong'o ya saɗaukar wa mahalarta taron cewa, "idan kun fifita harsunan turai; za ku ƙasƙantar da harsunan Afirka."

A matsayinsa na wanda a yanzu kusan yake rubutu harshensa na asali Gikũyũ kaɗai, Thiong'o ya yarda cewa " an fi samun nutsuwa da kuma hikimar iya wani harshen yaren Afirka.''

Dabarar, in ji shi, ita ce a tabbatar da cewa Afirka na " amfani da Ingilishi maimakon Ingilishi tana amfani da mu", ko da yake bai ba wai yana ba da shawarar marubuta 'yan Afrika su yi watsi da harsunan aka yi gadonsu daga zamanin mulkin mallaka ba ne.

Mashudu Ravele, wata matashiya marubuciya daga gundumar Vhembe a lardin Limpopo a arewa maso gabashin Afirka ta Kudu, na daga cikin marubutan da ke bin wannan salon hanyar ta Thiong'o.

Matashin mai shekaru 22 tana rubutu da kuma wallafa rubuce-rubucenta da harshen Tshivenda, wanda aka fi sani da Venda ko Luvenda kana yana daga cikin gomman harsunan Afirka ta Kudu da aka sansu a hukumance.

"Abin da nake yi shi ne in taimaka wajen alƙinta harshen Tshivenda da barin tarihi da al'ummomin gaba za su yi gado,'' a cewar Mashudu, wadda ta rubuta littattafai biyu ta shaida wa TRT Afrika.

''Marubuta da dama 'yan Afirka sun fi mayar da hankali wajen rubutu da Turanci. Ni kuma na zaɓi yin rubutu da Tshivenda saboda ba na son harshenmu ya mutu," in ji ta.

Mashudu Ravele tana haɗa sha'awarta ta rubuta labarai da kuma son harshenta na asali don ƙarfafa rubutun ta. / Hoto: Mashudu Ravele

Farawa tun daga yarinta

Mashudu, wadda aka haifa kuma ta taso a garin Mbilwi Sibasa, na da shaidar difloma a fannin aikin jarida kuma a halin yanzu tana karatun digiri ɗinta na biyu a fannin kimiyyar sadarwa a jami'ar Afirka ta Kudu.

Rubuce-rubucenta biyu da aka wallafa na daga cikin tarin waƙoƙin baƙa da aka tattara mai suna Tshisima Tsha Dora (Rafin kaiwa ga Ƙishina, 2020) da kuma littafin Ndi Vhudza Nnyi (Wa zan Gaya wa, 2022), wanda ya samu kyautar "littafin harshen Tshivenda mafi kyau" a shirin taron bayar da ƙyaututtuka kan littattafe na Afirka ta Kudu.

Mashudu ta fara rubuce-rubuce ne tun tana makarantar firamare, inda ta wakilci makarantarta a gasa daban-daban kuma ta samu lambobin yabo saboda hazakar ta.

"A lokacin da nake makarantar sakandare, na rubuta gajerun labarai amma ban mayar da hankali wajen wallafa su ba.

"A hankali na fara tunanin wallafa su, kuma a shekara 18 na wallafa littafi na mai suna Tshisima Tsha Dora don buɗe hanyata a matsayin marubuci," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Saboda ƙaunar da take yi wa Tshivenda, Mashudu na alfahari da bayyana kanta a matsayin marubuciya a harshenta.

Sha'awarta ga harshen ƙasarta na ƙara mata ƙwarin gwiwar ba da labari na matsayin matashiyar marubuciya da ke neman samarwa kanta suna.

Ma'aikatar ilimi na Afrika ta Kudu ta sanya ayyukan rubuce-rubucen Mashudu a cikin jerin harsunan karatu a hukumance. Kazalika an baje littattafenta biyu a daƙin karatu na Kwalejin Rosebank da ke ƙasar.

Mashudu Ravele tana haɓaka littattafanta da harshenta ta hanyar tallace-tallace a kafofin soshiyal midiya. / Hoto: Mashudu Ravele

Babbar manufa

Ƙasa da mutane miliyan ɗaya ne suke magana da harshen Tshivenda a faɗin ƙasar Afirka ta Kudu da Mozambique da kuma Zimbabwe.

Mashudu, ta bayyana damuwarta game da yanda harshen ke fuskantar ''koma baya'' har ma a tsakanin masu magana da shi, waɗanda mafi yawanci suka fi zaɓar magana da Turanci a matsayin harshe na farko musamman a yayin rubutu.

"Duk da cewa asalin harshen ya fito ne daga maƙwabciyar ƙasar wato Zimbabwe, asalin masu magana da Tshivenda sun fi yawa ne arewacin lardin yankin Limpopo da wasu tsirarru a Pretoria da Johannesburg.'' a cewar ta.

Duba da yanda take amfani da harshenta wajen isar da labari, Mashudu na haɓaka Tshivenda ta hanyar ƙara wa matasa masu karatu kalaman ƙamus.

Ta yi imanin cewa ƙalubalen da ke cikin rayuwar marubuci, yana kara ƙima a manufar da mutum ya sa a gaba.

"Manufana ita ce in ga 'yan Afirka suna rungumar harsunansu na asali wajen rubuce-rubuce, da kuma karantu da kuma bayyana ra'ayoyinsu - duk saboda al'ummominmu na gaba. Ba dole ba ne kowa ya kasance cikin Turanci," in ji Mashudu.

TRT Afrika