A farkon shekarar nan wasu tsaffin sojojin Senegal sun gana da shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Daga Mazhun Idris

Gwagwarmayar da Afirka ke yi na kwatar kanta daga shakar da sabon salon mulkin mallaka ya ki kawo wa karshe, amma 2025 na iya zuwa da kawo karshen mulkin danniya na Faransa, a lokacin da kasashen Yammacin Afirka renon Faransa ke daukar matakan nisantar Paris.

Babu wani abu da ya kara bayyana faduwa kasa ba nauyin da Faransa ta yi kan wannan al'amari kamar kalaman diflomasiyya na reni na Emmanuel Macron a lokacin da yake mayar da martani ga kasashen Sahel kan cewar sun juya baya ga kasar da ta taba yi musu mulkin mallaka.

"Sauraron godiya saboda dakatar da ayyukan mayakan islama a yankin Sahel," in ji Macron a ranar 6 ga Janairu, inda yake yabon sojojin Faransa a tsawon shekaru suke a yankin Sahel da sunan kare kasashen daga ta'addanci.

Ya ce "Babu wata kasa daya daga cikin su da za ta samu 'yancin gudanar da kanta, da a ce ba a kai sojojin Faransa yankin ba."

Kalaman na reni na Macron sun janyo ka ce na ce da suka a fadin nahiyar, inda Firaministan Senegal Ousmane Sonko ya caccaki Faransa saboda tarihin yadda ta dauki tsawon lokaci tana 'rikita kasashen Afirka'.

Farfesa Patrick Loch Otieno Lumumba, lauya kuma mai fafutuka dan kasar Kenya, ya bayyana Emmanuel Macron a matsayin mai wakiltar "masu sabon salon mulkin mallaka mafiya muni".

Yadda mulkin danniya ke dusashewa a hankali

Rushewar hadin kan soji da tattalin arziki tsakanin Faransa da kasashen Afirka da dama ya zo tare da nuna kyama ga Faransa da rufe sansanonin sojinta tsohuwar 'yar mulkin mallakar a yankin.

Shakiyancin Macron da ya bata wa yankin rai tare da rusa kansa da kansa, karara ya munana wa Faransa.

Shugaban na Faransa bai tsaya ga cin fukar kasashen Sahel na Afirka da wai "sun manta da" alherin da sojojin Faransa suka yi musu.

Ya ma yi gaba-gadin watsa rashin tsaron Faransa a fuskokin manufofin Afirka.

Babu alamun kasashen Afirka musamman na yankin Sahel za su dakata da tisa keyar sojojin Faransa suna barin kasashen.

An tirsasawa sojojin Farana barin Mali, Nijar, da Burkina Faso bayan juyin mulkin da aka yi nasarar yi a kasashen.

A Chadi da Senegal, yanzu ma da Ivory Coast, sojojin Faransa na kan barin kasashen.

Kasashen Sahel da dama sun zabi su kulla alaka mai kyau da wasu manyan kasashen duniya da ke son yin mu'amala ta adalci, girmama juna da cude ni in cude ka.

Turkiyya, Rasha, da China tuni suka danne Faransa a batun diflomasiyya.

A mafi yawancin lokuta, sabbin kawayen na karfafa wa sojojin Afirka don yakar makiya a cikin gida, a yayin da suke kuma kawo tsare-tsare na cigaba don samun'yancin habaka tattalin arziki da mallakar albarkatun kasa a ga kasashen.

"Boren kasashen Sahel wani babban naushi ne kan hakoran Faransa wanda ba ta tsammata ba," Farfesa Lumumba ya fada wa TRT Afrika, yana mai kara wa da cewar rubewar Faransa mai mulkin danniya ya fara ne a zamanin Macron.

Kallo cikin yaudara

A wata sanarwa a hukumance da aka fitar a ranar 7 ga Janairu, Firaministan Senegal ya kawo babbar magana kan me ya sa ikirarin Macron na bayar da taimakon samar da tsaro da zaman lafiya yake ba haka ba.

Da yake kawo Libya a matsayin misali, Sonko ya ce Faransa ba ta da "iko da halasci" wajen samar da tsaro ko 'yancin shugabancin kai a Afirka.

A yayin da Shugaba [project ke fadar sabanin gaskiya, Faransa na ta kokarin kare kanta a Yammacin Afirka, inda sojojinta na sabon salon mulkin mallaka suka gaza tare da rasa kimarsu.

Tun bayan korar sojojin kasashen waje daga iyakokinsu, Mali da Burkina Faso sun sanar da nasarar da sojojinsu suka samu kan 'yan ta'adda da suka dauki tsawon shekaru suna ba su matsala.

Arikana Chihombori, tsohon jakadan Tarayyar Afirka a Amurka, ya tunatar da cewa wanzuwar Faransa a yankin ya haifar da matsaloli da dama maimakon warwre su.

"Ina Burkina Faso a lokacin da wani Janar na soha ya fada min cewa 'Jakada, ga duk sojoji uku, muna da bindiga daya.

"Domin kayan aiki, sai sun rubuta a takarda zuwa ga Faransa. Sau tara cikin goma, za a ki amincewa da wannan bukata. Amma ka canki waye ba shi da matsalar makamai? 'yan ta;addar ne.'"

Chihombori ya ce dalilin da ya sa shugaba Ibrahim Traore ya yi nasarar yakar 'yan ta'adda a kasar shi ne ya rabu da Faransa.

"Faransa ce ke baiwa 'yan ta'addar kudi da makamai," in ji shi.

A lokacin da Faransa ke da dakaru a kasashe irin su Nijar, ba a iya kawo karshen rikici ba tsawon shekaru ba, inda 'yan bindiga da 'yan ta'adda suka yi ta kalibalantar kasashen.

Yadda ake ci gaba da raba hanya da sojojin Faransa da rushe alakar tattalin arziki a Yammacin Afirka da kasar, shaida ce da ke bayyana yadda cikin hanzari Paris ke rasa karfin fada a jin ta a Afirka da take yi wa mulkin mallaka cikin sabon salo.

Wani karin kutufo ga Faransa shi ne yadda Ivory Coast ta fada wa Faransa cewa nan da 25 ga Janairu sojojinta su tattara su bar kasar.

Masu nazari na bayyana wannan matsaki a matsayin wanda ba a tsammata ba kuma babban kutufo daga shugaba Alassane Ouattara, kuma abin mamakin shi ne yadda a baya dakarun Faransa suka taimaka masa wajen hawa mulki bayan rikicin da ya biyo rikitaccen zaben shugaban kasarsa.

Shugaba Ouattara ya yi amfani da jawabin karshen shekarar da ta gabata wajen sanar da matakin da gwamnati ta dauka na sallamar dakarun Faransa daga kasar.

A yanzu faransa ta yi rauni inda ba za ta iya tseren bin guguwar sauyi a Afirka ba, duk da dai tana ta kokarin samun gindin zama a wasu yankunan nahiyar ta hanyar karfafa alaka da kasashe irin su Benin, Togo, Nijeriya da ma Kenya da ke nesa.

Sahel na karfafa hadin kai

Ibrahima Hamidou, mai bayar da shwara kan sadarwa na musamman ga Firaministan Nijar, na jin cewa a wannan karon shugaban Faransa ya wuce gona da iri.

"Macron ya yi amfani da mummunan tunanin 'bauta' don tabbatar da gaskiyarsa duk da rashin nasarar da sabon salon mulkin mallaka a yankin Sahel. Da yana da kunya, da bai yi maganganun banza ga jakadu ba."

Ministan Harkokin Wajen Chadi, Abderaman Koulamallah, ya fada a tashar talabijin ta kasa cewa kalaman Macron na bayyana "kalaman raini ne ga Afirka da 'yan Afirka".

"Dole ne shugabannin Faransa su koyi girmama 'yan Afirka tare da amincewa da darajar sadaukar da suka yi."

Neman mafita mai wahala

A karon farko tun bayan fara Taron Afirka-Faransa a 1973 za a gudanar da Taron Hadin Kai na Shugabannin Afirka ba a Faransa ko kasar Afirka rainon Faransa ba.

Kenya da Faransa sun sanar a wajen Babban Taron Zauren MDD a New York a watan Satumban bara cewa za su hada hannu wajen gudanar da taron n 2026 a Nairobi.

Wannan shaida ce da ke nuna tabbacin rudewar Faransa wajen neman mafi a wajen tsaffin abokanta.

Macron bai boye yunkurin ba ko kadan, ya fara karfafa ayyukan diplomasiyya don rike Shugaba William Ruto.

TRT Afrika