Wani jami'in mulkin mallaka ne ya kai mutum-mutumin Ngonnso kasar Jamus shekara 120 da suka wuce. Hoto:

Daga Sylvia Chebet

Wani dadadden mutum-mutumi da aka sassaka da ice, wanda ake kira Ngonnso, kuma ake girmamawa a kasar Kamaru a matsayin "uwar sarauniyar" al'ummar Nso, ya kasance ajiye a akwatin gilashi a gidan adana tarihi na kasar Jamus, shekaru sama da dari.

An sa ran tsawon lokacin da aka kwashe ana dakon dawowar mutum-mutumin zai zo karshe ne wannan shekara. Amma ina? Tsare-tsare tsakanin hukumomi don dawo da shi sun hana hakan faruwa.

Yayin da jinkirin ke cigaba, akwai alamun damuwa da ya goge farin cikin da ya ginu bayan jin labarin shirin dawo da gunkin na Ngonnso.

Wani mai fafutukar ganin an dawo da kadarorin kasar, Sylvie Vernyuy Njobati ya gaya wa TRT Afrika cewa, "Muna girmama magabatanmu, mutum-mutumin wani tsani ne tsakanin mu rayayyu da kuma kakanninmu. Kuma mukan roki gunkin ya albarkaci kasarmu ta noma."

"A watan Fabrairu, an yi wani babban biki don hada kan mutane domin shirin maraba da dawowar gunkin. Mutane suna ta tunanin yadda za su tarbi gunkin. Wannan ya faru ne saboda bukatar ganin gunkin bai dawo a matsayin wani ice ba, sai dai a matsayin uwa ga al'ummarmu kamar yadda take a baya."

Wannan ya faru ne a watan Yuni na 2022, inda shugabar gidauniyar al'adu a Jamus, ta Prussian Cultural Heritage Foundation, ta bai wa Njobati wata wasika da ta tabbatar da cewa za a dawo wa al'ummar da gunkin na Ngonnso.

A cewar Njobati, alkawarin ya kawo karshen shekaru biyar na fafutukar maido da Ngonnso. Kuma alkawarin ya gaskata imaninsu na cewa wata rana gunkin zai dawo. Sai dai da yawa sun gwada amma hakarsu ba ta cimma ruwa ba har yau.

Fadi-tashi

Tarihin al'ummar Nso da tsananin sonsu ga gunkin na Uwar Sarauniya ya samo asali ne daruruwan shekaru. Bayan mutuwar sarauniyar ta asali, gunkinta ya sami gagarumar kima a al'adance, inda aka gina dakin bautar magabata.

An sace Ngonnso daga fadar sarauta a lardin Nso da ke Kamaru. Hoto:

Gunkin daya ne daga cikin dubban kayan tarihi da aka kwashe daga Afirka lokacin mulkin mallaka. Sama da adadi 500,000 a yanzu suna gidejen tarihi a Turai, da Amurka. Wasu kari kuma suna hannun cibiyoyi masu zaman kansu.

Kadan daga cikin wadannan kayayyaki an dawo da su kasashensu na asali. A watan Fabrairu na 2022, Nijeriya ta karbi biyu daga cikin gumakan tagulla 3,000 na masarautar Benin.

Wadannan nasarori da ba su da yawa sun harzuka Njobati inda ta shiga harkar fina-finai a wannan fanni. Tana fatan nuna tarihin tafiyar gunkin Ngonnso na tsawon kilomita dubu, daga Jamus zuwa Kamaru, a lokacin da abin zai faru.

Jira tsammani

Duk da alkawarin da Jamus ta yi sama da shekara guda, har yanzu babu wata alama na cewa gunkin Ngonnso zai dawo gida a nan kusa.

Al'ummar Nso sun so shirin ya yi sauri, amma tattaunawa tsakanin kasashen biyu ba ta faru ba har yanzu. Wannan ya sa Njobati take da shakku kan batun.

Ta ce, "Ba hikima a ce kasarmu tana tattaunawa da dayar kasar ba tare da sa-bakin wadanda abin ya shafa ba, wato gidajen tarihin da ke cikin al'ummar. Idan ka nunawa jami'an gwamnati abubuwa uku, ka ce su nuna maka Ngonnso a ciki, ba dole su iya fito da ita ba".

Sylvie Vernyuy Njobati yayin zanga-zangar #BringBackNgonnso a Berlin. Hoto : Autres

A wajen Njobati, wannan gwagwarmaya ce kuma sadaukarwa ce. Ta dauki alkawarin ga kakanta cewa za ta yi fafutukar ganin an dawo da uwar sarauniyarsu, zuwa kasarsu ta gado.

A ranar da ta yi zanga-zangar a wajen gidan adana kayan tarihi na birnin Berlin, inda ake ajiye da gunkin na Ngonnso, kakanta ya rasu. Mutuwar ta gigiza ta, daga nan ne ta ci alwashin yin duk abin da za ta iya don dawo wa al'ummarta gunkinsu.

Ta bayyana cewa, "Na yi tafiya mai nisa, sanda na fara wannan batun a shekarar 2021, na fuskanci irin rashin amincewa tattaunawa daga wadanda abin ya shafa. Hukumomin ba su da niyyar sauraren mu."

A wata wsika da ta bayyana cewa gunkin na Ngonnso a yanzu mallakin gidauniyar Prussian Cultural Heritage Foundation ne, bisa doka, kuma ba za a iya mayar da shi ba, wanda hakan ya nuna rashin niyyarsu.

Amma Njobati ta ce, tana “farin ciki kuma ta gamsu", game da yadda tattaunawar ta cigaba tun bayan wancan lokacin.

"Na san cewa abin da bai faru a lokaci guda ba, amma zan iya nuna cigaban da ke da muhimmanci. A yanzu sun amsa cewa tarihin kai gumakan cike yake da rikici da rashin adalci."

Al'ummar Nso suna neman a dawo musu da gunkin Ngonnso da ake ajiye da shi a gidan tarihi a Jamus. Hoto: Others

A yau, an kiyasta cewa akwai kayan tarihi fiye da 40,000 daga kasar Kamaru, da ke ajiye a gidajen tarihi a Jamus. Wani bincike na Atlas of Absence, ya nuna cewa wadannan abubuwa ba a faye nuna su a bainar jama'a ba, saboda suna suto tun lokacin mulkin mallakar Jamus (1886–1916).

A karo na farko, mawallafan sun gano cewa akwai abubuwa kasar Kamaru a gidajen tarihin jamus, a wani rubutu da aka wallafa a shafin arthistoricum.net, wanda kundi ne da ake samun wallafe-wallafe na bincike kan fasaha da tarihi.

Tasawirori masu yawa, da zane-zane da hotuna sun nuna wuraren da kididdigar inda kayayyakin tarihi daga Kamaru suke a Jamus.

Njobati ta ce wasu cibiyoyi biyu na daban a Jamus, sun nuna a shirye suke su dawo da kayayyakin, 28 daga gidan tarihi na Liden Museum, da biyu daga jami'ar University of Minds.

Ta ce, “Sun fara amnicewa cewa wadannan ba karikitai bane na 'yan Afirka, kadarorinmu ne na tarihi. Kuma alamu ne na ruhin al'umominmu. Kuma sun sauya daga "Wa za mu dawo da su ba", zuwa "A shirye muke mu yi aiki da ku", sai kuma "Mun shirya dawowa da su".

  Zanga-zanga a Jamus don neman dawo da da gunkin Ngonnso zuwa Kamaru. Hoto: Others

Tambayoyi game da ko Afirka za ta iya adanawa da kula da kayayyakinta, tana taimakawa wajen tantama kan dawo da kayayyakin.

A littafinta, mai suna Africa’s Struggle for Its Art: History of a Postcolonial Defeat, mawallafiyar nan Bafaranshiya masanar tarihi, Bénédicte Savoy, ta ce damuwar da gidajen tarihi na Turai ke nunawa , wani bangare ne na neman mantawa da bukatarmaidowar ko kashe gwiwar 'yan Afirkan.

Yayin bin diddigin tattaunawa tsakanin jami'an gwamnati da shugabannin gidajen tarihin, Savoy ta gano cewa batun maido da kayan an dade da fara shi amma cin tura ya yi.

Ta rubuta cewa, "Kusan duka tattaunawar kan maido da kayayyakin al'adu zuwa Afirka an taba yin da shekaru 40 da suka wuce",

Tun kafin fara kafa gidajen tarihi, masana tarihi sun ce 'yan Afirka sun rayu kuma sun yi mu'amala da kayayyakinsu na tarihi, tsawon daruruwan shekaru ba tare da sun rasa “kima ko manufa" ba.

Wasu hanyoyin hana lalacewar kayan tarihi ne suke sa kayayyakin suke a halin da suke a yanzu mai kyan gani.

Njobati. ta ce, “Kalubale guda a wannan lokacin shi ne an zuba wa gunkin Ngonnso sinadaran don hana icen lalacewa, kuma watakila dole sai an cigaba da saka sinadaran."

Ta yi hanzarin cewa babu bukatar tayar da hankali. Mafi muhimmanci, a cewarta, wadannan mallakar fadojin masarauta inda aka wawushe su.

Allo mai cewa "a dawo mana da Ngonnso", Sylvie Njobati

Abin da bai bayyana karara ba shi ne tsawon lokacin da Njobati da 'al'ummar Nso za su jira kafin dawowar gunkin Ngonnso, wanda jagoran rauhanansu ne. Amma duk sanda uwar sarauniyar ta dira garin, za a ga gagarumin biki da da budurin nasarar cigaban tarihin al'ummar.

TRT Afrika