Masu mulkin mallaka sun yi tasiri kan sunayen yawancin kasashen Afirka, amma wasu sun kasance bayanai na 'yancin kai. Hoto: Getty Images

Daga Sylvia Chebet

Kudi, kamar yadda ake cewa, shi yake sa duniya ke motsawa. Amma sauyi daga cinikin musaya zuwa amfani da takardun kudi sauyi ne mai cike da kewaye-kewaye, wanda ya bi hanyar sauyin tattalin arziki da siyasa da kuma zamantakewa mabambanta kamar yadda kudaden suka bambanta.

Yayin da da yawa a cikinmu suka tashi a duniya da tsarin takardun kudin da aka alakanta da kasashe, wani dattijon Afirka yana da labari mai ban sha’awa a kan rawar da ya taka wajen samar wa kudin kasarsa suna har zuwa lokacin da kudin ya zama kudin da ake kashewa a kasar.

Tsohon jakadan Eritrea Andebrhan Welde Giorgis jami’in diflomasiyya ne wanda ya kasance dan siyasa kuma masani kan tattalin arziki wanda shi ya jagoranci samar da kudin nakfa a lokacin yana shugaban Babban Bankin Eritrea.

Ya fara aikin ne a yammacin wata rana a shekarar 1994 a lokacin da shi da Shugaba Isaias Afwerki suka karbi bakuncin tawagar Bankin Duniya a karkashin jagorancin Peter Miovich a wani taron cin abinci a da aka yi a wani gidan abinci a Asmara.

Eritrea ba ta dade da gama yakin neman ‘yancin kai da aka kwashe shekara 30 ana yi ba a wancan lokacin da makwabciyarta Ethiopia kuma tana shirin maye gurbin takardar kudin birr din Ethiopia ne da kudinta. Gwamnan, da shugaban kasar da kuma bakinsu daga Bankin Duniya suka tsunduma cikin muhawarar kudin a lokacin da suke cin abincin.

An yi ta ambato sunayen da za a iya saka wa kudin a lokacin tattaunawar a lokacin da Miovich ya shaida wa masu masaukin bakin cewa, "Duba, kun yi wani abu mai ban-mamaki. Babu wanda ya yi tsammanin cewa za ku yi nasara, amma kun bijire wa tunanin kasashen duniya."

Ana kirga takardar kudin "Nakfa" a birnin Asmara. Hoto: Reuters

Giorgis ya bayyana wa TRT Afrika shawarar da Miovich ya bayar a lokacin. "Saboda haka, me ya sa ba za ku ce masa nakfa ba?" in ji shi. "Zai kasance alamar tsayawa tsayin-daka da himma da juriyar mutanen Eritrea a yakin neman ‘yancin kai."

Nakfa ya samo asali ne daga garin da ake kira da wannan sunan a lardin Northern Red Sea na kasar Eritrean wanda ya kasance shelkwatar kungiyar neman ‘yancin kan Eritrea.

Zama takardar kudi

Nakfa daya ne daga cikin takardun kudin Afirka da aka rada wa sunan wurare. Omer Yalcinkaya, mataimakin shugaban kungiyar takardun kudi na duniya, ya fitar da wani bincike mai suna "Tushen sunayen takardun kudin duniya," a shafin intanet na kungiyar inda ya lissafa takardun kudi 215 da ake amfani da su a kasashe 250.

Bincikensa ya bayyana cewa takardar kudin Saliyo, leone, ta samo asali ne daga sunan kasar yayin da kalmar naira ta kasance sauyin kalmar Nigeria ce.

Sauran sunayen takardun kudaden sun hada da kwanza na Angola, wanda ya samo sunansa daga daga kogin Kwanza. Molati na kasar Lesotho ya samo asali ne daga jerin duwatsun mai wannan sunan a Afirka ta Kudu.

Rand na Afirka ta Kudu ya samo sunansa ne daga kalmar yaren mutanen Holland "Witwatersrand", wanda ke nufin "tudun farin ruwa ". Wani yanki ne a arewa maso gabashin kasar da ke da wuraren hakar zinari mafi girma a duniya.

Kamar rand, sunan dollar ya fito ne daga "Joachimsthal" na yaren Jamusawa, wanda yake nufin Joachim's Valley, wani gari a kasar Czech Republic inda ake hakar azurfa a da. Sulallan da aka sarrafa da azurfa a wannan mahakar ma’adinan sun zama "joachimsthaler", wanda aka gajarza zuwa "thaler", kuma ya zama dollar daga baya.

Wasu kasashe a fadin duniya suna da nasu takardar kudin dollar, ciki har da kasar Amurka da Australia da Canada da Fiji da New Zealand da kuma Singapore. A Afirka, kasashe uku – Namibia da Liberia da kuma Zimbabwe — suna da nasu takardar kudin na dollar.

A wani lokaci ma kasar Zimbabwe ta buga triliyon daya na takardar kudin dollar (Z$ 100 trillion ) saboda hauhawar farashi.

Zancen nauyi

Yalcinkaya ya lura cewa wani abu ya fi yawa a bincikensa: "An samo sunayen kudaden farko ne daga nauyinsu."

Sunayen kudaden da suka hada da Pound da Peso da kuma Lira an same su ne daga awu. Photo: Reuters

fam din Birtaniya da lira din Turkiyya da dirham din Larabawa da rouble din Rasha da drachma ta Girka da kuma peseta ta Sifaniya duk suna da alaka da nauyinsu.

Masar da Sudan da kuma Sudan ta Kudu suna da nasu fam din. Ghana ta maye gurbin fama din da cedi na kasar Ghana ("karamar kwasfa " a harshen Akan). Haka ma dalasi na Gambia. Rupee na Seychelles da kuma Mauritia sun maye gurbin fama bayan ‘yan Indiya sun kwarara cikin kasashen.

Wasu kasashe renon Birtaniya suna amfani da shilling, wanda aka samo daga Kalmar tsohon Ingilishi "Scilling", wadda ke nufin "a raba ". fani da shi a Gabashin Afirka.

Tushen kudaden kasashen renon Faransa

A cikin yawancin kasashe renon Faransa, kudin franc — wadda ke nufin sulalla a harshen Faransa— ya zama kudin da ake amfani da shi.

Kasashen takwas a yammacin Afirka suna amfani da CFA Franc — kasashen Benin da Burkina Faso da Côte d'Ivoire da Guinea-Bissau da Mali da Nijar da Sénégal da kuma Togo — da kuma kasashe shida na tsakiyar Afirka wadanda suka hada da Kamaru da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Chadi da Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo da Equatorial Guinea da kuma Gabon. Mauritania ma ta zabi amfani da takardar kudin a shekarar 1973.

Takardar kudin franc ta shiga Rwanda a shekarar 1916, a lokacin da Belgium ta kama kasar da Jamus ke mulka a lokacin. Rwanda ta yi amfani da Franc na Kongo da Belgium ke mulka zuwa shekarar 1960 a lokacin da aka samar da franc din Burundi da na Rwanda. An fara amfani da franc a Djibouti a shekarar 1884 bayan kasar ta koma karkashin mulkin Faransa.

kalmar dinar ta samo suna ne daga kalmar Latin "denarius", sulen azurfa na Rome a da. Hoto: AP

Madagascar ta maye gurbin Malagasy franc da takardar kudin Ariary, yayin da Mauritania ta maye gurbin CFA Franc da ariary. An ce an samu sunan ariary ne daga wani kudin da aka yi amfani da shi kafin mulkin mallaka, wata dala mai azurfa.

An yi da azurfa

Morocco ma ta sauya daga amfani da franc zuwa dirham, wadda ta samo sunanta daga drachma, sulallan Girka da aka yi amfanin da shi kasashen Larabawa kafin zuwan Musulunci.

Makwabciyarta Algeria kuma ta maye gurbin franc da dinar, inda ta bi sahun akalla kasashe goma, ciki har da Libya da Iraki da Jordan da kuma Tunisia. Dinar ya samo asali ne daga Kalmar Latin "denarius", wani sulen azurfa na Roma a da.

Kazalika, takardar kudin birr wadda ke nufin azurfa. An fara amfani da shi ne a kasar Ethiopia a shekarar 1893 kuma ya zama kudin kasar a hukunance a shekarar 1976.

Alamar ‘yanci

Yayin da masu mulkin mallaka suka yi tasiri kan sunayen yawancin kudin nahiyar, wasu bayanin ‘yanci kai ne ya yi tasiri a tushen sunayensu, kamar nakfa.

Kwacha ta Zambiya ta fito ne daga Kalmar harshen Bemba da ke nufin "safiya", wanda ke nuna taken kasar, "Sabuwar Safiyar ‘Yanci." Malawi ma ta zabi kwacha a matsayin kudinta a hukumance.

Daya daga cikin sunayen kudade da suka fi asali, in ji Yalcinkaya, shi ne pula na Botswana. Yana nufin ruwan sama a harshen Setswana, wani harshe a kasar.

Yayin da yawancin kudade suka kasance masu alama mai tarihi, masarautar Eswatini ta zabi ta kira kudinta da suna langeni, Kalmar dake nufin "kudi " a harshen Swati na kasar.

TRT Afrika