Bayan jira cikin tsammani na kusan watanni biyar, lokacin ya zo a ƙarshen watan Janairu: wato damar barin Gaza domin tsere wa mugun yaƙin da Isra'ila ta ƙaddamar a birninmu da ta mamaye.
Don jin daɗin kaina da mijina, wani Bafalasɗine ɗan uwana da ke gudun hijira wanda muke zaune a Rafah ya bayyana cewa a ƙarshe sunana ya bayyana a cikin jerin waɗanda za a kwashe a ranar 26 ga Janairu.
Ni asalin ƴar Masar ce, amma mijina ba ɗan Masar bane.
"Ki shirya, dole ne ki kasance a mashigar Rafah gobe da misalin bakwai na safe," kamar yadda Abu Shaaban ya shaida mata cikin murmushi.
Shi da ni mun jira tsawon lokaci domin zuwa wurin ƴaƴana, waɗanda suka yi ƙoƙarin tserewa zuwa Masar tare da yayata a watan Disamba.
Zuwa watan Janairu, lamarin ya ƙara ƙazancewa a Gaza a daidai lokacin da Isra'ila ta ƙara tura sojojinta kan farar hula inda suka kashe dubban Falasɗinawa.
Yadda tafiyata ta zama zahiri ya samo asali ne bayan ɗana Khaled ya yi ƙoƙarin kirana a waya daga Masar bayan ya yi yunƙurin hakan sau da dama.
Sai dai murna da shauƙi sun lulluɓe ni - duk da ina tunanin tafiya, sai dai na shiga damuwa domin na gano cewa sunan mijina ba ya cikin waɗanda ke shirin tafiya.
Duk da zuciyata ta yi nauyi, amma sai da na tafi na bar shi, inda na yi ta ƙoƙarin neman yadda iyalinmu za su ƙara haɗuwa tattare.
Sai dai na ƙara shiga damuwa bayan na yi tunanin cewa ba lallai ne na rinƙa samunsa yadda nake so a waya a kullum ba.
Tun bayan soma yaƙin Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, hare-haren Isra'ila sun yi mummunan tasiri kan kayayyakin sadarwa na Gaza, wanda hakan ya rinƙa jawo ɗaukewar sabis ɗin waya.
Falasɗinawan da ke Gaza na ci gaba da fama da matsalolin intanet da na wayoyin sadarwa.
Sai dai tafiya ba tare da mijina ba, Ahed, bai kasance lamari mai sauƙi ba; ya karya mani zuciya ya barni cikin fargaba.
Na shafe dare ina ta tunani kan matakin da zan ɗauka, har sai da na yi tunanin tsayawa tare da shi. Duk da damuwar da nake da ita game da ƴaƴana, amma na kasa tunanin barin Ahed a baya domin ya fuskanci abin da ba shi da tabbaci a Gaza shi kaɗai.
Birnin Rafah da ake zargin sojojin Isra'ila sun ayyana shi a matsayin wuri mai aminci ga fararen hula, yana fuskantar barazanar ayyukan sojin Isra'ila a kullum.
"Kada ki yi tunanin wani abu, na ji muku daɗi ke da ƴaƴana, zan kasance cikin aminci, kada ki damu," kamar yadda Ahed ya shaida mani.
Mun rungume juna inda na rinƙa kuka. Cikin dare, na haɗa jakata sannan na yi bacci na tsawon sa'o'i sannan na tashi da misalin biyar na asuba.
Na sha wahala domin ban samu motar tasi wadda za ta kai ni iyakar Rafah ba saboda ƙarancin man fetur.
Makwabcinmu ne wanda yake da mota ya tuƙa mu zuwa can inda muka biya shi shekel 250, kimanin dalar Amurka 68 kenan.
Yayin da muka kama hanya, sai na kalli teku da kuma mutanen da ke kusa da ni. Zuciyata ta yi nauyi domin na ji ba lallai ne na iya komawa Gaza nan kusa ba sakamakon babu wata alamar kawo ƙarshen yaƙin nan kusa.
Yayin da nake bankwana da abubuwan da na sani a gefen teku da tituna, na zura ido kan tantuna da yadda jama'a suka taru. Lokaci ne mai raɗaɗi, wanda ke nuna bankwana na ƙarshe ga yanayin bakin ciki na Gaza.
A daidai lokacin da na kawo mashigar Rafah, sai na ga ɗumin jama'ar da suka taru a wurin, wanda wannan tuni ne kan irin hijirar da ake yi sakamakon zaluncin da Isra'ila ke aikatawa.
"Da alama duka ƴan Gaza na guduwa," kamar yadda na shaida wa kaina. A farko na yi tunanin ba alama ce mai kyau ba, amma a daidai lokacin, amma a gaskiya ya kamata a gudu daga kisan kiyashin da ake aikatawa.
A kusa da mashigar, wasu mutane sun kafa tenti, inda wasu da dama kuma bacci ya ɗauke su a kan kujerunsu, inda suke jiran a kira sunayensu domin su kama hanya.
A daidai lokacin da nake lura da gefena da idanuwana na ƴar jarida, duk wani bayani ya kasance lamari mai ban mamaki a gare ni; mashigar ta yi kama da wani sansani fiye da iyakar da take.
Abin da nake jira ya iso bayan na ji wani ma'aikaci ya kira sunana a mashigar. Bayan na cika da shauƙi, sai na rungume mijina sosai kafin na shiga wurin tafiyar.
Sai na buƙaci Ahed ya jira mu na awa ɗaya, inda nake tunanin zan iya magana da wani jami'i da ke ciki ya bar shi domin mu taho tare, sai dai jami'in ya ƙi amincewa.
"Idan sunansa ba ya kan jerin sunayen, ba zai iya tafiya ba...kuma kar ki ɓata mani lokaci."
Sai na tafi zuciyata cikin nauyi. Bayan an buga mani hatimi kan fasfo ɗina, sai na shiga mota zuwa gefen Masar da ke mashigar Rafah.
An yi wa kowane matafiyi cikakken bincike na tsaro, inda jami'an na Masar suke bin diddiƙin hatimin tafiya da da sunaye a lokacin binciken tare da ɗaukar bidiyon fasinjojin da kemara - wanda lamari ne da ban san da shi ba, amma ya kasance dole ga wannan tafiyar zuwa Masar.
Da muka isa Masar, mun jira a cikin motar bas na kusan sa’a guda kafin a ce mu sauka. Wakilin wata hukumar tafiye-tafiye da ke birnin Alkahira ya raka mu zuwa wani zaure.
Dole ne in ajiye dala 650 don samun damar barin Gaza, wannan ita ce kawai hanyar doka a cikin duk zamba da muka ji game da masu gudanarwa ba bisa ka'ida ba waɗanda suka nemi dubban daloli don fitar da wani daga Gaza.
Tafiya daga Sinai zuwa Alkahira na da sauri da sauki. Na isa Alkahira da karfe 8 na dare, na kwana a wani karamin otal tsawon dare daya.
Da safe, yarana, waɗanda suke zama a gidan wani ɗan uwana, sun zo otal ɗin. Na yi murna matuƙa domin ban yi tsammanin zan sake ganin Khaled da Omar ba. Mun rungume juna mun yi kuka da dariya a lokaci ɗaya.
Da na isa otal ɗin, na yi sauri na wanka —kyakkyawan wankana na farko kenan cikin watanni biyar. Kasancewar shawa mai aiki, samun ruwa mai gudu, da samun haske da intanet a cikin ɗakina na ji kamar da gaske. Ba na buƙatar tafiya mita 2,000 a kowace rana zuwa tanti da ke cikin sansani a cikin ruwan sama don tabbatar da lafiyar yarana; duk abin da nake bukata yanzu na a hannu.
Sai dai ina tunanin Ahed.
Ina tuna irin wahalar da muka sha a tare tun bayan da aka soma wannan yaƙin a Gaza - wanda ya raba mu da muhallinmu sau da dama, tun daga Gaza zuwa Khan Younis zuwa Rafah a yanzu.
Our struggles to secure water, the infrequent showers, the reliance on battery torches due to frequent power cuts, and the exorbitant prices of food items are etched in my memory. Life during wartime is undeniably challenging, but in Gaza, it's nothing short of horrific and harrowing.
Gwagwarmayar da muke yi na tabbatar da ruwa, ruwan wanka da ba mu cika samu ba, dogaro da da fitilar batiri saboda ɗauke wutar lantarki, da tsadar kayan abinci da tsadar kayan masarufi, duka sun zama tarih. Rayuwa a lokacin yaƙi babu shakka ƙalubale ne, amma a Gaza, babban abin tsoro ne.
The morning after I arrived in Cairo, I visited the headquarters of the travel and tourism company that helped me get out of Gaza.
As an Egyptian, I had to pay $650. For non-Egyptians, the price was $1500. I had to get my husband out, but we could not afford it yet. My goal was to save money and bring my husband back to our family.
However, that morning, I was dismayed to find out that they had increased the fees for Palestinians, making it unaffordable for me at $5000.
Disheartened, I left in tears, feeling frustrated and uncertain about the future. I cling to hope, praying for my husband's safety and our eventual reunion.
Kwana guda bayan na isa birnin Alkahira, sai na shiga hedikwatar kamfanin tafiye-tafiyen da ya taimaka mani na bar Gaza.
A matsayina na ƴar Masar, sai da na biya dala 650. Ga wadanda ba ƴan Masar ba, farashin ya kasance dala 1500. Dole na fitar da mijina, amma har yanzu ba mu iya biya ba. Burina shi ne in ajiye kudi in dawo da mijina cikin danginmu.
Duk da haka, a safiyar wannan rana, na damu da na gano cewa sun kara wa Falasdinawa kudade, wanda hakan ya sa ba zan iya biyan dala 5,000 ba.
A razane na tafi cikin kuka, ina jin takaici da rashin. Ina fata, ina yi wa mijina addu’a Allah ya ba shi lafiya, ya kuma kara sa mu haɗu
Gangar cikina na cikin Masar amma ruhina na a Gaza. Tunanina na cike da batun mijina da kuma gidanmu da ke Gaza - Ina ta tunanin idan yana nan yadda yake sakamakon irin hare-haren da sojojin Isra'ila ke kaiwa.
Zuciyata na matuƙar son a tsagaita wuta, wanda lamari ne mai kamar wuya, domin jama'ar da suka mutu da waɗanda suka samu rauni da waɗanda suka ɓace.
Ina ta tunani kan yadda makomar Gaza za ta kasance da makomar iyalaina. A matsayina na ƴar jarida, na rubuta labarai da dama kan yaƙi, amma a halin yanzu labarin da nake son rubutawa shi ne "An tsagaita wuta a Gaza".