Daga Pauline Odhiambo
A lokacin da take shekara 15, a shekarar da yawancin mata sa'anninta suke tashen kwalliya da kyale-kyale, Yasmina El Habbal ta gane cewa wata rana sai ta dauki rikon da.
Wannan tunanin ya zo mata ne bayan wata ziyara da ta kai wani gidan marayu, inda ta kamu da son kananan yaran da ita da 'yan makarantarsu da suka je ziyarar jin-kai, da suka kai wa kyaututtukan kayan wasa da tufafi.
Ta ce, "Tun daga lokacin da na saka kafata a gidan marayun nan, na san cewa ina so na daukin rikon da. Na samu karfin rai kan hakan, sai kawai na ji ina jiran lokaci ne kawai ban damu da ta yaya zai faru ba".
Yasmina tana fatan yin aure da kuma burin haihuwar 'ya mace – inda har ta shirya sa mata suna, "Ghalia", wanda ke nufin "mai daraja" a harshen Larabci.
Ko da yake ta taba kewayawa ba don neman abin da take so ya kasance a kusa da ita ba, Yasmina za ta bar Ghalia dinta. Uwa da 'yar sun hadu, ba kamar yadda Yasmina take tunani ba lokacin da take yarinya, amma hakan ya faru ne a gidan marayu na Masar shekara 25 bayan haka.
Yarinya Ghalia, wacce take da kyawawan idanu masu ruwan kasa, nan take ta fara jin barci lokacin da Yasmina ta rike ta.
"Tana kuka lokacin da aka fara kawo ta, amma sai ta yi tsit yayin da aka miko min ita. Sai na cewa kaina, Eh! Ta san cewa ni mamarta ce," kamar yadda Yasmina ta shaida wa TRT Afrika. "Duk lokacin da na tuna abin da ya faru, na kan gode wa Allah. Allah na kaunata."
Daga nan ne labarin Yasmina da Ghalia ya fara kulluwa.
Kalubalen dauko yaro
Dauko yaro wanda ba kai ne ka haife shi ba, hakan na dora wa wanda ya dauko shi nauyin da doka ta dora a kan iyayensa na asali, ba abu ba ne da addinin Musulunci yake kwadaitar da yawan yinsa saboda kare tsatso.
Sai dai akwai tsarin kafala, wato wani tsari da mutum zai iya dauko yaro maraya — inda zai rika kula da cinsa da shansa da kuma addininsa.
Yasmina, wacce Musulma ce, tana tuna lokacin da ta yi aikin sa-kai na shekaru a gidan marayun da ta fara kai ziyara lokacin tana makaranta — a hankali sai ta zama wata tsayayyiya a rayuwar yaran.
"Ban ji dadi ba lokacin da na fahimci cewa iyaye mata da aka dauke su aiki ko masu aikin kula da yaran ana maye gurbinsu da wasu bayan kimanin wata uku," in ji ta. "Na ji tausayin yaran saboda na san tasirin samun tsayayye a rayuwar yaro."
Uwar goyo
Jim kadan bayan cika shekara 21, Yasmina ta samu aikinta na farko kuma sai ta fara daukar nauyin wasu yara mata biyu wadanda suke gidan marayu. Ta kulla alaka ta kut da kut da yaran, inda take kai musu ziyara akai-akai da kuma kula da bukatunsu bakin gwargwado.
"Na dauki nauyinsu tun suna wata 10 da haihuwa," kamar yadda Yasmina mai shekara 43 ta bayyana. "Ina gidan marayun lokacin da aka kawo su kuma yanzu duka su biyun sun kammala karatun digiri a jami'a. Daya daga cikinsu ta riga ma ta samu aikin da take kauna matuka."
Yasmina, wacce yanzu take aiki da Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a birnin Cairo a bangaren shirin ciyar da 'yan makaranta abinci, ta ce ta yi ayyuka da dama tun lokacin da take da shekara 20 da doriya, amma aikin da ta fi so shi ne wanda take hulda da yara.
A lokacin da take shekara 40, Yasmina ba ta yi aure ba – wannan ya sa ba za ta iya dauko yara ba.
"Da farko dokar ta amince ma'aurata ne kadai za su iya dauko yaro wadanda suka kai wasu shekaru, kuma suke zaune tare tsawon shekaru ba tare da samun haihuwa ba ko yiwuwar samun haihuwa," in ji ta.
"A hankali sai abubuwa suka fara sauyawa. An ba ma'aurata da suka wuce shekara 21 damar dauko yaro ko da kuwa suna da nasu yaran."
Sabbin dokoki
Dauko yaro a Masar yana zuwa da tsangwama saboda yara da yawa da suke neman wadanda za su dauke su, an yi watsi da su, ciki har da wadanda aka aure su ba ta hanyar aure ba. Yasmina tana fama da wannan kalubale hatta a cikin gidansu.
"Lokacin da na shaida wa mahaifina aniyata ta dauko yaro, nan take ya ce min a'a," in ji ta.
A karshe a watan Yunin shekarar 2020, lokacin da mahukunta suka amince wa matan da ba su da miji da suka wuce shekara 30 damar daukar yaro, wannan sauyin dokar ya kara wa Yasmina kwarin gwiwa kan bukatarta ta dauko yaro.
Gwamnatin kasar Masar tana fatan kara samun yawan iyayen da suke son su dauko yaro wanda hakan zai sa al'adar ta kara yaduwa da karin samun karbuwa a tsakanin mutane.
Amma farin cikin da Yasmina ta ji bayan rike yarinyar a hannunta bai dore ba, saboda annobar korona ta tsayar da al'amura.
"Komai ya tsaya, ciki har da aikin hukumomin da ke tafiyar da tsare-tsaren dauko yaro. Babu abin da zan iya yi," in ji Yasmina, wadda 'yar uwarta da aminiyarta kadai ta fada wa shirinta na dauko yaro.
"A karshe sai annobar ta zama min alheri saboda batun bayar da tazara ya sa cike takardun dauko yaron da sauran tanade-tanade an yi su ne ta intanet.
Bayan sake sanarwar, na latsa wani link kuma sai na cike wasu bayanai," in ji Yasmina, wacce ta aika da takardun shaidar samun kudin shigarta da gwajin ajin jininta da sauran abubuwa da ake bukata."Da zarar an kammala haka, an kwashe tsawon mako uku kafin a amince da bukatata."
Amma sai Yasmina ta bayyana a gaban wani kwamiti mai mambobi 17 wanda zai mata tambayoyi kan dacewarta a matsayin uwa.
"An yi ta tambayarta, 'Me ya sa kike son ki dauko yarinya? Ke mace ce da ba ta da miji: me ya sa kike son daukar wannan nauyi? Za ki iya yin aure a kowane lokaci. Me za ki yi kenan? Za ki dawo mana da yarinyar kenan? Yasmina ta ce bayan ganawar.
"Na fahimci cewa duka tambayoyinsu suna kan hanya saboda an samu akwai lokuta da mutane za su dauko yara, sai kuma su yi watsi da su daga baya."
Koma wa gida
Mako daya bayan an amince da bukatarta, Yasmina ta gana da jaririya 'yar mako uku mai suna Ghalia a wani gidan marayu da ke birnin Suez, mai nisan tafiyar sa'a biyu daga birnin Cairo.
"Wani yaro wanda shi ma aka dauko daga gidan marayun ya turo min hoton yarinyar, kuma sai ta ja hankalina," in ji Yasmina yayin ganawar farkon. A karshe ta yi nasarar dauko yarinya Ghalia wata biyu bayan haka.
"Yanzu Ghalia shekararta uku kuma za ta fara zuwa makaranta. Kowa na kaunarta, ciki har da mahaifina," in ji Yasmina.
Shawararta ga duk wanda yake so ya dauko yaro mai sauki ce: dangane da yiwuwar hakan da tunani.
"Dauko yaro ba abu ba ne mai sauki, haka zalika tarbiyyar yaro. Amma ina jin dadin kasancewata a matsayin uwa. Wasu lokuta sai na ji kamar Ghalia ce take min tarbiyya ba ni ce nake mata ba. Saboda tana so na kasance mace ta gari."