Zumar Grecom ta Nzarubara ta shiga yankunan wajen Goma da ma kwastomomi a Jamus, Beljiyom, da Amurka ta hanyar fitar da kayayyaki. /Hoto: Déborah Nzarubara

Daga Firmain Eric Mbadinga

Tuddan Masar na dauke da rirrika da dama, wasu na karo da wasu, wasu na bayyana rikitaccen al'amarin sararin duniya.

A 2015, masana tarihin zmaantakewar dan adam sun hako wasu abubuwa da aka samar da tabo masu shekaru 3,000, kuma suke kewaye da yana.

Abin da ya ba wa kowa mamaki shi ne halin da kayan da aka samu ke ciki - zuma ta gaskiya da ke rike da dandanonta da ingancinta duk da daukar shekaru da dama a kasa.

A yayin da wannan abu da aka gano yake baiwa mutane gama-gari mamaki, masu noman zuma ba su yi mamakin hakan ba.

Sun san cewa zuma na dauke da sinadarai masu daraja, ciki har da jurewa tsawon lokaci.

Wannan inganci ne ya zaburara da Deborah Nzarubara, mace 'yar kasar Kongo dafa yankin Goma mai fama da rikici, inda ta shiga noman gadan-gadan.

Kamfanin Grecom da Deborah ta samar a 2018, ya fadada kasuwancinsa, ya kara yawan ma'aikata, ya kara yawan kudadensa, tare da fadada rarraba kayayyakinsa.

Nzarubara ta samar da Kungiya Mai Zaman Kanta don horar da masu kiwon zuma, da dabaru masu kyau da ba sa bata muhalli wajen samar da zumar. /Hoto: Déborah Nzarubara

Ta hanyar tsarinta na gudanarwa da kokarin yau da kullum, Deborah ta sadaukar da kanta ga kawo sauyi a mummunar fahimtar da aka yi wa noman zuma tare da jama'arta, yayin da take kuma zamantar da sana'ar wadda har yanzu wasu suka dauka da wasa.

"Kasancewar wadda aka haifa da raina a kusan da Fiilin Shakatawa na Virunga, tun ina karama na dinga ganin masu kiwon zuma. Iyayena ma masu noman zumar ne, haka ma mijina.

"Wannan kusanci ya ba ni damar fahimtar wahalhalun da ke tattare da noman zumar a kasarmu. Na san cewa a wasu lokutan ana yin mummunan kallo ga masu kiwon zuma," Deborah ta fada wa TRT Afrika.

"Ana zargin wasu da maita saboda yadda suke da juriyar tunkarar zuma. Wasu na fuskantar kyara saboda ana cewa wannan sana'a ce ta wadanda ba za su iya zuwa karatu ba. Ta hanyar horar da kaina da shiga noman zuma, ina bukatar kawo sauyi a zukatan jama'a."

Deborah da ta yi karatu a Cibiyar Nazarin Cigaban Karkara a Goma tare da kammalawa a matsayin babbar masaniya, ta kirkiri wata kungiya mai zaman kanta a 2013 don taimakon masu noman zuma.

'Action Solidaire pour la Protection des Abeilles' na horar da masu noman zumar kan sabbin dabaru da ba za su gurbata muhalli a yayin gudanar da sana'ar tasu.

"Darussan da ake koyarwa sun yi tasiri sosai, ana bayar da dama ga masu noman zumar su bar tsaffin hanyoyin da ke ilata muhalli da samar da zumar, baya ga zama mai tausayawa kudan zumar," in ji Deborah.

Fadada ayyuka

Inganta hanyoyin gidanar da sana'ar cikin sauri sun sanya an samu daduwar indanji da yawan zumar, wanda ya sanya masu samar da ita neman masaya a sassa daban-daban.

Grecon na samar da zuma daban-daban irin su beeswax da propilis. /Hoto: Déborah Nzarubar

A 2018, Grecom ya samar da babban tsari d aya dace da muhalli da sayar da zumar da ake nomawa.

Masu noman zumar da aka horar sun samar da wajen shigar ta kwanda na zamani, sun samar da kayan hayaki da samar da kayan kariya masu kyau.

Tsari mai kyau na gyara zuba jarin kayayyaki da safararsu, da inganta wuraren aiki, sun samar da sakamako mai kyau.

Dabarun tallata kayan da ake samarwa da kunshe su a abu mai ban sha'awa na taimaka wa wajen samar da zumar, wadda da ma ta gaske ce da magungunanta a cikinta, kuma ta fi jan hankalin masu saye.

An yi watsi da tantamar farko da ake yi game da asalin zumar ta hanyar wayar da kan jama'a da Grecom ke yi.

Kuma yadda ma ake kunshe zumar ne ke kara jan hankalin jama'a.

"Dabarun sun yi nasara sosai. Muna sa ran yaddadabarun yadda kunshe zumarmu ne ya sanya take samun inganci haka.

"An samar da amintar jama'a a hankali. Tuntuni muka samu kwangila da manyan shaguna da kanana," in ji Deborah.

A yanzu Grecom na samar da zuma daban-daban irin su beeswax da propilis da ma zallar ta.

Daga asalinta a Goma, zumar Grecom ta fadadu zuwa masu amfani da ita a Kinsasha da Bukavu.

Ta kuma isa ga masu saya a Jamus, Beljiyo da ma Amurka ta hanyar safarar ta.

Sauya tunani

Nasarar kokarin Deborah ba iya masu noman zuma yake ba wa kudade ba har ma da daga martabarsu a cikin jama'a.

Nzarubara ta taimaka wajen kafa kungiyar masu noman zuma wanda ya samar mata yabo daga Bankin Duniya da Bankin Cogaban Afirka. /Hoto: Déborah Nzarubara

Manhajar NyukiTech na dauke da jerin masu noman zumar, tana taimaka wa wajen gudanar da aiki, goyon baya, da bayar da damarmakin horo a masana'antar.

Ana musayar bayanai game da hatsarin yanayi da dabarun kiwon zuma a manhajar, ana aika wa sakon kar ta kwana don ganin dukkan masu kiwon zuma a Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo sun tallafi juna a fannoni daban-daban.

Deborah da ke da yara hudu, ba ta yin rayuwar birgewa ko nuna ita wata ce. A yayin da take kula da iyalinta sama da komai, tana kuma alfahari da yadda take kawo sauyi ga abokananta wanda ke nganta noman zuma a kasarta.

Tun shekaru goma da fara wannan sana'a ta noman zuma, ta lura da cewa mata ciki har da ita kanta ba sa fuskantar kyama kamar a baya, kuma mutane a yanzu na jinjinawa masu noman zumar.

Tafiyar Deborah a sana'arta da sadaukarwarta ya janyo mata yabo daga cibiyoyin kudi, ciki har da Bankin Duniya da Bankin Cigaban Afirka.

A karkashin jagorancinta, Grecom ya samar da ayyuka da yawa, kafa kungiyar masu noman zuma, da tsara yadda za a samu cibiyar bincike da ta kware kan kudan zuma da kiwon su a matsayin wani bangare na tattalin arziki.

Juriya a yayin fuskantar tsangwama

Duk kokari da burin Deborah ya sha ruwa bayan da mako guda da tattaunawar ta da TRT Afrika, garin Goma da take rayuwa a ciki ya fada hannun mayakan M23 da kawayensu.

Kamar masu zama a garin da dama, an hana Deborah ruwan sha, lantarki da yanar gizo tsawon makonni.

An lalata wajen aikinta da kayan nomanta a lokacin da yaki ya barke da lokacin da aka fasa shaguna da kasuwanni ana sace kayayyaki.

Amma juriyar Deborah ta sanya ta ci gaba da tafiya duk da kalubalen.

Ta amince da kasarta da makomarta, haka ma garin Goma, inda take fatan za ta dawo da ayyukanta na inganta noman zuma a kasar.

TRT Afrika