Daga Sylvia Chebet
A wani yankin marasa galihu da ke Mathare, gabashin wajen Nairobi babban birnin Kenya, wasu yara masu tasowa da ke saka fararen kaya suka bayyana, suna wasa da takubba.
Su ne 'yan wasan karaskiya na kasa. Wajen wasansu na nan shimfide a kan hanya mai kula da ke unguwa mai yawan jama'a, wajen na da rufin kwano kuma kewaye da waya.
Faruq Mburu Wanyoike ne mai horar da su, yana yaba wasan karaskiya da ya kawo sauyi babba a rayuwarsa.
"Ina matukar godiya ga Ubangiji bisa dama da ya ba ni a karo na biyu," in ji shi yayin tattaunawa da TRT Afirka, inda yake bayyana yadda wasan karaskiya ya raba shi da aikata muggan laifuka, tare da dasa manufar rayuwa a zuciyarsa.
Shekaru goma kawai da suka wuce, Faruq ya yi fito na fito da mutuwa yayin da ake yin fashi da makami da rikici.
"Ba zan so su shiga irin wannan yanayi na rayuwa ba da nake ciki a baya," in ji Faruq, a yayin da yake shessheka yana share hawayen da ke zubo masa.
"Na dimautu saboda yadda suke zaune a unguwar da na girma. Suna fuskantar irin kalubalen da na fuskanta."
Labarai irin wannan
Wasu daga cikin matasa masu wasan karaskiyar sun fadi sirri ga mai horar da su game da yanayin da suka fada a rayuwa.
Faruq na tsoron irin wannan rayuwa za ta iya jefa su cikin aikata muggan laifuka. Koya musu karaskiya ne hanyar nuna kwarewarsu a fannin wasnanin, da kuma motsa jini da sauya halayyarsu.
Ko meye kalamin da ya fi yi wa matasan? "Kar ka bari muhallinka ya zama me bayyana waye kai."
Mafi yawan yara maza da mata da ke karkashin horarwar Faruq na hutun makaranta nda suke zuwa wasa kullum.
Tsalle-tsallensu na kullum na kayatar da masu wucewa ta kusa da filin wasan, kuma masu sayar da kaya na zagaye bakin hanyar.
Faruq ya ce "Karaskiya wasan masu hannu da shuni ne. Muna son karya wannan tsari mu mayar da shi wasan gama-gari, wasan unguwa da yankunan talakawa."
Kubuta daga laifi
Da yake waiwaye ga rayuwarsa ta yarinta a zamanin da 'yan daba ke rike da iko da mafi yawancin yankunan Mathare, Faruq ya tuno yadda fara shiga aikata laifi a rayuwarsa.
Rayuwar kawa d ayaran unguwa ke yi ce ta ja hankalin Faruq mai shekara tara.
Zai tambayi mahaifiyarsa ta ba shi dama ya yi wasa da yaran na wani dan lokaci. Ita kuma sai ta kyale shi, ba ta san wadanne irin abokai ne yaron nata ya hadu da su ba.
"Sai na je inda suke zaune, na zauna a wajen da suka zauna, na saurari abun da suke cewa," in ji Faruq yayin tuna zamanin baya.
Ba a dauki tsawon lokaci ba suka jefa shi cikin mummunar rayuwa.
"Za su dauki bindigogi, su gyara su, su kirga kudade a nan da can, sai na tambayi kaina shin mu 'yan sanda ne? in ji Faruq.
Duk da yana yaro karami, ya ji cewa lallai akwai dalilin da shi ma bai san shi da ya sanya shi kar ya bayyana wa kowa abun ya gani.
Lokacin da ya cika shekara 12, faruq ya kware wajen sarrafa bindigar amfani a ruwa, abun da ya tsaya ya koya a nutse.
Bayan wasu 'yan shekaru, Faruq ya koyi yadda ake sarrafa bindiga. Sai ya kusa zama abokin aikin bata-gari.
"Ni ne mafi karancin shekaru a cikin su, amma ban taba harbin kowa ba.... Zuciyata ta raya min hakan ba daidai ba ne."
A wannan gaba, ya bayyana karara gare shi cewa, akwai mummunan sakamakon ga aikata muggan laifuka, ana iya mutuwa ma.
"Daya bayan daya, aka harbe dukkan abokaina. Na gano cewa wannan wasa ne da za a iya gama shi ta hanya mummuna," in ji shi.
Darussan rayuwa
"Mummunan laifi ba ya taimako, yana illata mutum ne" abun da Faruq ke fada wa yaransa kenan a ko yaushe.
Sau biyu ana yi masa kwalkwal a rayuwarsa. Yana iya tunawa karara yadda wani dare suka bi wani dan kasuwa da ke dauke da kundin Kenya na Shilling miliyan uku, daidai da $30,000.
"Suka tare shi. "Amma abun mamaki sai muka ga ya tsaya da kansa ma... Mu ne ai za mu tsayar da shi."
Faruq bai gane me ke faruwa ba. Abokansa suka yi zumbur suna son su kwace kudin, ba su fahimci cewa shiri ba ne. "Daga nan sai ga 'yan sanda duk sun zagaye mu. Aka dana bindigu, aka bude wuta," Faruq ya shaida wa TRT Afirka.
Faruq ya ga yadda abokanansa biyu suka fadi kasa inda shi kuma suka arce don neman wajen tsira. Harsashi ya samu hakarkarinsa, wani kuma kafarsa. Ya fada wani kogi da ke kusa da wajen wanda yake dauke da damba.
"Na zauna a cikin ruwan na kamar awanni uku, ina tunani kan rayuwata a yayin da na ke jiran 'yan sandan su tafi," in ji Faruq. "Wannan ce ranar da na yanke hukuncin ba zan sake shiga aikata muggan laifuka ba."
Ba da jimawa ba, sai kaddara ta hada shi da Sakatare Janar na Kungiyar Wasannin Karaskiya ta Kenya, Stephen Okalo Kuya, a wata cibiyar rawa da motsa jiki.
Kuya ya zaci cewa Faruq na da jiki irin na masu wasanni, kuma in ko zai yarda ya fara wasan karaskiya. Matashin bai taba sanin wanne wasa ne wannan ba, kuma ya bukaci Kuya da ya nuna masa shi.
"Ina ganin takubba, sai na tuna yadda na ke kallon su a fina-finai. Sai na ji na kamu da son wasan," in ji Faruq.
Kuya ya ba shi horo na kusan shekara guda, kuma ya samu tallafin karatu a Afirka ta Kudu, inda ya samu kwarea kan koyar da wasan karaskiya tare da karbar shaidar kammala samun horon a 2021.
A 2022, ya je Alkahira, Masar don halartar gasa ta farko, kuma shi kadai ne dan kasar Kenya a gasar.
Daga baya, ya je Milan, Italiya, don halartar Gasar Karaskiya ta Duniya. Ya shirya wakiltar Kenya a Wasannin Neman Zuwa Gasar Olympic ta ta Aljeriya ta 2024.
Kundin bajinta
A wajen garin Matsare, Faruq na da yara 45 da yake horarwa.
Ya horar tare da samar da kwararru 15 a Kungiyar Karaskiya ta Tsavora wadanda a yanzu suke kungyar kasa.
Daliban Faruq sun shirya wakiltar Kenya shekara mai zuwa a babba da karamar gasar duniya da za a yi a Saudiyya da Moroko, abu da yake ba shi alfahari.
Ya ce "Ina son su zama mafi kyau ga kawunansu... A matsayin mai wasan motsa jiki, kana bukatar ka zama mai bin dokoki. Kana bukatar ka zama mai burin cimmawa. Kana bukatar ka samu jarumtaka.
Duk da kalubalen kudade, Faruk na da burin zama mai kawo sauyi.
Yana burin kai wasanni zuwa makarantu a kasar, matakin da ya kira da sunan "Litattafai da Takubba" --- kokarin da ya yi imani zai fitar da yara da matasa da dama daga ayyukan bata-gari.