Vitiligo: Yadda dan Kenya yake yaki da masu tsangwamar masu cutar mele

Vitiligo: Yadda dan Kenya yake yaki da masu tsangwamar masu cutar mele

Akwai akalla mutum miliyan 100 a duk fadin duniya da ke fama da cutar mele da ake kira Vitiligo.
Okal Andrew yana fara ganin alamomi a kan lebansa yayin da yake makarantar sakandare. Hoto: Okal     

Daga Paula Odek

A wannan bangaren duniyar da al'umma ke bai wa kyau muhimmanci, Andrew Clifford Okal a shirye yake ya zama wani tauraro da ya yarda da kansa wanda ba ya karaya.

Duk da cewa ya fuskanci kalubale da dama, shekaru 13 da ya yi yana fama da ciwon fata na Vitiligo bai hana shi jajircewa a rayuwa ba.

Maimaikon haka, ya tsaya tsayin daka wajen yaki da tsangwamar da ake yi wa mutanen da ke fama da ciwon fata da kuma kokarin sauya tunanin mutane.

Ciwon fata na Vitiligo wani yanayi ne da fata ke shiga sanadin rashin wani sinadari abin da ke jawowa fatar ta yi fari ko kuma jaja-jaja.

A wasu lokuta hakan yana jawo kumburi a ido ko a kunne. Ciwon Vitiligo yana farawa ne yayin da wasu kwayoyin halitta da ake kira melanocytes suka mutu ko kuma daina aiki.

Aikin kwayoyin halittar shi ne samar da sinadarin melanin — wato sanadrin da ke bai wa fata da gashi da idanu launi.

Cutar Vitiligo tana kama kowane jinsi ba babba ba karami, tana kama hatta fararen fata. Hoto: Others 

Cutar tana kama miliyoyin mutane a fadin duniya ciki har da 'yan Afirka kuma masu fama da cutar suna fuskantar tsangwama daga jama'a.

Alamomin farko

Tasowata a matsayin maraya a Kenya a karkashin kulawar kakannina, Okal ya rungumi rayuwa da kwarin gwiwa inda ya yi karatu cikin nasara kuma ya kasance mai zama da shaukin yin sabbin abubuwa.

Okal, wanda yanzu yake shekara 30, ya tuno karara yadda ya fara ganin alamomin cutar Vitiligo a kan lebansa yayin da yake makarantar sakandare a shekarar 2010.

Ya zaci morin jini ne sai dai karamar tawadar ba ta bace ba a kan lokaci kamar yadda ya zama.

Maimakon haka sai ta ci gaba da fadada kuma har ma ta shafi fuskarsa da hannunsa da kafafunsa, daga nan ne sai abin ya fara damunsa.

A shirye Andrew Okal yake don ya sauya tunanin mutane kan cutar Vitiligo. Hoto: Okal

‘‘Ba a haife ni da cutar Vitiligo ba. Amma lokacin da na shiga makarantar sakandare, sai labbana suka fara yin jaja-jaja," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"Abokaina suna cewa ina basaja ne wasu kuma suke danjan mota," kamar yadda Okal ya ce 'yan ajinsu suna tsokanarsa.

'Kyau da cutar Vitiligo'

Okal ya yanke shawarar ya karbi yadda ya koma da zuciya daya kuma bayyana kansa da "na musamman" kuma daga nan ne ya fara wayar da kan al'umma dangane da yanayin fata a duk inda ya samu kansa kuma ya ce masu fama da wannan matsalar ka da su karaya, kuma kada al'umma su rika tsangwamar masu ita.

Ya kirkiro wani kirari wato "Masu cutar Vitiligo Kyawawa ne," ya yi tsayuwar daka yayin da hakan ke jawo idon mutane sosai a kansa.

Ya mayar da hankali ne kan farin cikinsa maimakon yadda mutane suke kallonsa saboda ciwonsa.

Bayan tsangawar da kyamar da yake fuskanta a makaranta da kuma a kan titi, har ila yau Okal ya ce yana fuskantar wasu kalubale ciki har da na tsadar magani da yadda ake nuna masa wariya yayin da yake neman aiki bayan kammala babbar makaranta.

Okal Clifford Andrew ya ce ya fi mayar da hankali ne a kan farin cikinsa maimakon yadda mutane suke kallonsa. Hoto: Okal Andrew 

Sai dai daga baya ya samu aiki a matsayin malamin makaranta a birnin Nairobi.

Ko da yake wasu dalibai masu kwakwa suna yawan tambayarsa game da launin fatarsa kuma yana yi musu bayani abin cikin natsuwa kuma yawancinsu yanzu sun saba da ganin haka.

Kaucewa magana da mutane

‘‘Idan ban yi amfani da abin da ke bayar da kariya daga rana ba, fuskata tana konewa kuma tana koma wa jaja-jaja kuma ta kumbura," in ji shi.

Okal ya yi watsi da canfe-canfen mutane kan cutar Vitiligo inda yake cewa cutar ba ta yaduwa.

Cutar Vitiligo tana jawo sauyi a launin fata ne kawai kuma "ba ta jawo wani zafin ciwo ko rashin jin dadi," kamar yadda ya yi bayani. Ya ce wasu mutane ba sa musabaha da shi.

"Mutane suna ganin zan sa musu cutar Vitiligo idan na gaisa da su da hannu," kamar yadda Okal ya bayyana yana murmushi.

Ya ce wannan yana daya daga cikin abubuwan da mutane ba sa fahimta ba game da cutar kuma yana cikin abubuwan da ke jawo ake nuna masa wariya.

Okal ya yi kokarin bakın kokarinsa wajen ganin bayan tsangwamar da ake nuna masa saboda fatarsa. Hoto: Okal

Akwai akalla mutum miliyan 100 da ke fama da cutar fata ta Vitiligo a fadin duniya, kamar yadda Gidauniyar Bincike kan cutar Vitiligo wanda ke Amurka ta bayyana.

Wannan gidauniyar da wata irinta da ke Nijeriya sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ranar 25 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin Ranar Masu Cutar Vitiligo ta Duniya, gidauniyoyin biyu sun fara raya wannan rana tun shekarar 2011.

Masana sun ce kowa zai iya kamuwa da cutar Vitiligo, kuma a kowace shekara, sai dai yawancin mutane masu Vitiligo fari-farin fatar yana farawa ne kafin su shekara 20.

Abin da ke jawo cutar mele

"An fi samun cutar Vitiligo a mutanen da suke da wani da ya taba kamuwa da cutar a danginsu da taba kamuwa da wasu cutuka masu kama da ita," kamar yadda Ma'aikatar Kula da Lafiya ta Amurka, wato daya daga cikin manyan cibiyoyin binciken kiwon lafiya a duniya, ta bayyana.

Wasu daga cikin cutukan da ke iya jawo Vitiligo ko kara tabarbarewarta su ne: cutar Addison da cutar Pernicious da cutar Anemia da cutar Psoriasis da cutar Rheumatoid arthritis da ciwon siga nau'in farko da sauransu.

Babban alamar cutar Vitiligo shi ne rashin sinadarin da ke fitar da launin fata, abin da ke jawo wani fari-fari a fatar hannuwa da kafa da gwiwar hannu da matsematsi da kuma fuska.

Amma wannan fari-farin yana iya bayyana a ko ina a jiki ciki har da cikin baki da cikin hanci.

Miko Deo, wani dan Tanzaniya mai fama da ciwon fata na Vitiligo wanda yake kaunar buga wasan kwallon kwando da wasan takalmin taya. Hoto: Reuters 

Har ila yau gashi yana iya komawa fari cikin sauki a wuraren da fata ta rasa sinadarin da fitar da launi kamar a kai da gira da gashin fatar ido da gems da kuma gashin jiki.

Idan fari-farin da fata yake yi, ya bayyana a wani bangare daya a jiki ana kiran ciwon Vitiligo na bangare daya.

Akwai kuma wanda ba na bangare ba ne — wato wanda matsalar ta bayyana a sassan jiki — misali a kafa biyu da kuma giwar kafa biyu.

A lokuta kalilan, cutar Vitiligo tana shafar kusa duka sassan jiki. Wannan ce ake kira cutar Vitiligo ta duka sassan jiki.

Masana kimiyya sun yi amannar cewa cutar mele ta cikin jerin cutuka da ke samo asali daga garkuwar jiki tana yakan jiki (autoimmune disease).

A wannan yanayin, garkuwar jiki tana kai wa jiki hari kuma tana lalata kwayoyin halittar melanocytes maimakon kai hari kan baki abubuwa da suka shiga jiki wadanda za su iya jawo cuta.

Saukin samun magani

‘’Masana suna ci gaba da bincike kan ko samun mai cutar a cikin dangi da kwayoyin halittar gado suna taka wajen kamuwa da cutar Vitiligo.

A wasu lokuta — kamar yayin mai cutar ya shiga zafin rana da yayin da yake cikin damuwa ko kuma wasu sinadarai suka taba shi — wadannan za su iya jawo mele ko kuma jawo kara tabarbarewarsa," in ji Ma'aikatar Kula da Lafiya ta Amurka.

Okal Andrew ya yi amannar cewa cutar Vitiligo ba za ta zama mai cikas ba ga nasararsa a rayuwa ba. Hoto: Okal

Cutar Vitiligo ba ta da magani. Kodayake masana sun ce magani sun ce magungunan da ake shafawa a fata za su iya taimakawa wajen rage tabarbarewar cutar da kuma taimakawa wajen daidaita launin fatar.

Abin da ke ba da kariya daga hasken rana yana taimaka wajen kare fata.

Ko da yake tsangwama da nuna wariya sun da yawa daga cikin masu dauke da cutar mele ba sa jin kwarin gwiwar shiga mutane, mutane kamar Andrew Okal sun yi amannar cewa jajircewarsu za ta iya kawo sauyi wajen canja wadannan dabi'u na mutane.

"Mu mutane ne kamar ku, launin fatar ne kawai ya jawo wannan," in ji Okal, yana aika sako ga mutanen da ke nuna wariya ga masu dauke da cutar Vitiligo.

TRT Afrika