Daga Abdulwasiu Hassan
Akwai wata magana da Turawan mulkin mallaka na farkon ƙarni na 19 suke faɗa wadda suke cewa Afirka ta Yamma "Kabarin Farar Fata", don bayyana irin bala'in da suka ci karo da shi na annobar maleriya a yankin, lamarin da ya nuna ƙoƙarin cim ma burinsu na ɗibar albarkatun nahiyar da suke ikirarin cewa tana da hatsari ga rayuwarsu.
Ko da yake wannan tunanin ya canza a cikin shekarun 1850 bayan da aka ba da shawarar amfani da quinine a matsayin maganin cutar zazzabin cizon sauro, sai dai cutar mai kisa ba ta gushe ba har a yanzu kusan shekara 175.
Maleriya ta hallaka aƙalla mutum 194,000 a Nijeriya a shekarar 2021, a cewar rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).
An ƙiyasata cewa kusan kashi 97 cikin 100 na yawan al'ummar Afirka za su kasance cikin haɗarin kamuwa da cutar, wadda sauro ke yaɗa ta.
Habasha da Uganda su ne sauran ƙasashen da maleriya take yi wa ɓarna sosai a kowace shekara.
"A shekarar 2022, yankin yammacin Afirka ya fi fama da cutar zazzabin cizon sauro, inda kashi 94% na wadanda suka kamu da cutar, da kashi 95% na mace-mace a duniya suka kasance a can, wanda ke wakiltar wakiltar mutum miliyan 233 na waɗanda suka kamu da mutum 580,000 na waɗanda suka mutu, abin da ke nuni da samun raguwa kadan idan aka kwatanta da shekarar 2021," in ji WHO.
Yara sun fi kamuwa da maleriya, fiye da manya, saboda idan aka girma jiki yakan bujire mata. Bisa ƙididdigar da WHO ta fitar, kashi 80 cikin 100 na mace-macen da zazzabin cizon sauro ke haddasawa jarirai ne da kananan yara.
Bincike da yawa sun ambata cewa yara 'yan kasa da shekaru biyar a yankin kudu da hamadar Sahara sun fi kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro sau biyar fiye da wadanda suke da karfin tattalin arziki.
Garkuwa daga riga-kafi
A farkon shekarar 2024, Kamaru ta zama kasa ta farko da ta ƙara allurar riga-kafin zazzabin cizon sauro a cikin jadawalin riga-kafinta na yau da kullun.
Wannan ya biyo bayan shirin riga-kafin zazzabin cizon sauro na gwaji a Ghana da Kenya da Malawi tsakanin 2019 da 2023.
Kwanan nan Nijeriya ta sami allurai 846,200 na allurar riga-kafin cutar zazzabin na R21/Matrix-M a matsayin wani bangare na shirin fara allura miliyan daya. UNICEF ta kiyasta yawan abin da ake bukata ya kai miliyan 31.
A cikin ƙalubalen da ke tattare da yin allurar riga-kafin al'umma masu rauni, akwai ɗan fata - an ayyana Masar a ƙasar da ba ta da zazzabin cizon sauro yanzu.
WHO ta bayyana nasarar da aka samu a matsayin sakamakon kokarin kawo karshen wata cuta da ta addabi kasar tun a zamanin da.
"Malaria ta daɗe tun zamanin wayewar Masar kanta, amma cutar da ta addabi fir'aunoni a yanzu ta zama tarihin ƙasar ba makomarta ba," in ji babban daraktan WHO, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Don haka, ko akwai yiwuwar allurar riga-kafi za ta kawar da cutar ɗungurungun?
Duk da cewa nasarar da Masar ta samu ba karamin abu ba ne, hukumomi na ganin cewa ba tabbatar da cewa babu maleriya ne karshen labarin ba, domin a ko da yaushe akwai damar cutar ta sake bullowa.
An ambato mataimakin firaministan Masar Dr Khaled Abdel Ghaffar yana cewa "karbar takardar shaidar kawar da cutar zazzabin cizon sauro ba shi ne karshen wannan tafiya ba, illa mafarin shiga sabon babi."
"Yanzu dole ne mu yi aiki ba tare da gajiyawa da kuma taka-tsan-tsan don ci gaba da tabbatar da nasarar da muka samu ta hanyar kiyaye mafi girman ka'idoji na sa ido da ganewar asali, da magani da kuma ci gaba da mayar da martani mai inganci da sauri ga lamuran da aka shigo da su."
Matsalolin da ke gaba
Kwararru a fannin kiwon lafiya sun yi imanin cewa akwai bukatar a kara yin aiki don dakatar da mace-mace sanadin zazzabin cizon sauro da kuma nauyin tattalin arzikin cutar, gami da rage yawan aiki.
Shugabannin kasashe da gwamnatoci a taron Majalisar Dinkin Duniya na baya-bayan nan sun yi gargadin cewa idan ba a shirya karin kudade don yaki da zazzabin cizon sauro ba, mutane 300,000 za su iya mutuwa sakamakon cutar.
Haɗin gwiwar RBM don kawo ƙarshen cutar zazzabin cizon sauro, wani dandalin duniya don yaƙi da wannan annoba, ya yi kashedin cewa "duniya za ta iya ganin ƙarin masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro miliyan 112 da ƙarin mutuwar mutane 280,700 a cikin shekaru uku, tare da yaɗuwar cutar a duk faɗin nahiyar Afirka".
"Hujjar ta fito ƙarara cewa akwai gagarumin hadarin kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro idan ba a ƙara samun kudade ba sannan kuma wuraren da suka fi fama da ita ba sa iya kai muhimman ayyukan riga-kafin cutar zazzabin cizon sauro," in ji Dr Michael Adekunle Charles, shugaban kungiyar RBM a hadin gwiwar kawo karshen maleriya.
“Ba kamar cutar kanjamau da tarin fuka ba, zazzabin cizon sauro ya ta’allaka ne a kasashe masu karamin karfi, musamman a fadin Afirka, wadannan kasashe ba su da karfin da za su iya yaki da cutar, kowa a duk inda yake zaune, yana da hakkin ya samu lafiya. Maleriya tana wahalar da mutane a cikin ƙasashe masu karamin karfi wajen jin daɗin yancinsu na kiwon lafiya. "
Fiye da tallafin kudi
Dokta Agbor Neji Ebuta, likita ne da ke Abuja, ya yi imanin kawar da zazzabin cizon sauro na bukatar hadin kai da hadin gwiwa daga masu ruwa da tsaki wadanda suka wuce tallafin kudi.
"Abin da muke bukata shi ne jajircewa, kokarin hadin gwiwa da ya hada da rarraba gidajen sauro da aka saka wa maganin kwari, da matakan sa ido da aka tsara don gano sabbin masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro cikin sauri, da kuma magani," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Ministan lafiya da walwalar jama'a na Nijeriya, Muhammad Ali Pate, ya ce kasar na shirin "inganta dukkan kayan aikin da ake da su" na irin wannan shiri.
"Dabarunmu sun hada da samar da gidajen sauron da riga-kafin cutar sankarau na lokaci-lokaci, maganin rigakafi na lokaci-lokaci, fadada kula da cutar, da sanya wadannan sabbin kayan aiki kamar alluran rigakafi. Har ila yau, muna da niyyar daidaita wadannan kokarin yadda ya dace da bukatun sassa daban-daban na kasar."
Ga miliyoyin mutane a duk faɗin Afirka, fatan cewa wata rana nahiyar za ta kasance ba ta da zazzabin cizon sauro, mafarki ne da ya dace a bi.