Hukumar da ke sa ido kan wutar lantarki a Nijeriya NERC ta bayar da umarni kan a rage yawan lantarkin da ake bai wa ƙasashen waje domin ƙara yawan wutar da ake samu a cikin gida.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce sashen da ke samar da wutar lantarkin ya jawo wahalhalu ga ƴan Nijeriya sakamakon an fi bayar da muhimmanci ga wutar lantarkin da ake bai wa ƙasashen waje fiye da kwastamomin cikin gida.
NERC ɗin ta ce za ta ƙayyade kan cewa kaso shida cikin 100 na wutar lantarkin da ake samarwa kaɗai za a rinƙa bayarwa ga ƙasashen waje waɗanda suka haɗa da Nijar da da Benin da Togo a watanni shida masu zuwa, wanda hakan zai fara daga 1 ga watan Mayu.
Kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya na da yarjejeniya da wasu kasashen Afirka da ke makwabtaka ita don ba su lantarki, inda ƙasar ke samun kuɗaɗen shiga ta ɓangaren domin tallafa wa tattalin arziƙinta.
Sai dai duk da haka, ba ko da yaushe ƙasashen ke biyan kuɗaɗen wutar da suka sha a kan lokaci ba.
Ana yawan samun katsewar wutar lantarki a Najeriya saboda ƙarancin wutar lantarki amma abin ya kara kamari a 'yan kwanakin nan.
Haka kuma a yan kwanakin nan ne kamfanonin da ke rarraba lantarkin suka ƙara kuɗin wuta ga kwastamomi waɗanda ya kamata su rinƙa samun wuta a kullum ko sama da awa 20 a rana, sai dai duk da haka ba su samun isashiyar wutar.
Haka kuma baya ga yarjejeniya da Nijeriyar ke da ita ta wutar lantarki da ƙasashe irin Niger da Togo da Benin, kamfanonin samar da lantarki na ƙasar na da yarjejeniya da manyan kamfanoni da ma’aikatun gwamnatin ƙasar waɗanda suke samun fifiko wurin samun wuta fiye da sauran kwastamomi.
Hakan ne ma ya sa masu sharhi ke ganin akwai yiwuwar nan gaba irin wannan ƙayyade wutar ya shafi kamfanonin da ma’aikatu.