Hukumomin Mali sun sanar da rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kasar Rasha ta gina masana'antar sarrafa zinare a Bamako, babban birnin kasar.
Kasashen biyu sun sa hannu kan wasu yarjejeniyoyi da dama tare da tabbatar da ci gaban hulda da ke tsakaninsu, ciki har da gina masana'antar sarrafa zinare mafi girma a yammacin Afirka wacce za ta iya samar da tan 200 na zinare a duk shekara.
Yarjejeniyar za ta yi aiki ne tsawon shekaru hudu, a cewar Ministan Tattalin Arziki da Kudi na kasar Mali Alousseni Sanou.
Aikin zai ba da dama "kan duk wani abu da ya shafi sarrafa zinare, da ma aiwatar da ayyukan shige da ficensa da kuma biyan haraji," in ji Ministan yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na kasa ORTM a ranar Talata.
A watan Agusta, Mali ta amince da wani sabon kundin tsarin ma'adinai wanda ya bai wa kasar damar daukar kashi 30 cikin 100 a sabbin ayyukan ma'adinai da kuma kara samun kudaden-shiga daga masana'antar mai muhimmanci.
Habaka dangantakar Rasha da Afirka
Kasar na daya daga cikin kasashen da suka fi samar da zinari a Afirka, inda ta samar da tan 72.2 a shekarar 2022, wato kashi 66.2 kenan da masana'antun ke samarwa da kuma karin kashi 8.4 cikin 100 a cewar hukumar kididdiga ta kasar Mali.
Zinare na samar da kusan kashi daya cikin hudu na albarkatun kasafin kudin Mali, inda ya zama daya daga cikin kasashen da ke samar da zinari a nahiyar.
A yanzu haka, ana fitar da akasarin zinaren kasar Mali ne zuwa kasashen Afirka ta Kudu da Switzerland da kuma Australia.
Dangantaka tsakanin Mali da Rasha ta kara karfi a 'yan shekarun nan, musamman bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 2021 da kuma janyewar sojojin Faransa daga Operation Barkhane a shekarar 2022.
A shekarun baya-bayan nan dai kasar Rasha na kara habaka alakarta da kasashen Afirka a fannin tattalin arziki da tsaro a kokarin da take yi wajen kara karfinta a nahiyar.