Shugaban Rasha Vladimir Putin ke neman yin amfani da taron na St Petersburg don inganta alakarsa da kasashen Afirka / Photo: Reuters

Rasha ta yafe wa Somaliya wani bangare na bashin dala miliyan 684 da take bin ta a wata yarjejeniya da aka cimma a wani kwarya-kwaryan taro da aka yi a wani bangare na babban taron Rasha da Kasashen Afirka a birnin St Petersburg, kamar yadda jami'an Somaliyan suka fada.

Somaliya, wacce take kokarin farfadowa daga gomman shekarun da ta shafe tana fama da yakin basasa, tana neman samun sauki daga tulin bashin da ake bin ta a karkashin Shirin Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF da kuma Bankin Duniya na yafe wa kasashe matalauta basussukansu.

"Wannan matakin zai taka babbar rawa wajen kammala matakin yafe basussukan kasar," a cewar Ministan Kudi na Somaliya Bihi Egeh, a wani sako da ya wallafa a shafin Facebook na ma'aikatarsa kan batun yarjejeniyar da Rasha.

Yarjejeniyar wacce aka sanya wa hannu a ranar Laraba tsakanin Egeh da mataimakin ministan kudi na Rasha Timur Maksimov, ta shafi batun bashin Paris Club, kamar yadda Mataimakin Firaministan Somaliya Salah Ahmed Jama ya gaya wa kamfanin dillancin labarai na Rasha, RIA Novosti.

Tsarin yadda biyan zai kasance

Jama ya kara da cewa, a karkashin yarjejeniyar, an yafe wani bangare na bashin yayin da sauran kuma za a tsara yadda za a dinga biya a hankali a hankali.

Yarjejeniyar da aka cimma da Somaliyan na zuwa ne a yayin da Shugaban Rasha Vladimir Putin ke neman yin amfani da taron na St Petersburg don inganta alakarsa da kasashen Afirka, tare da dakushe kokarin Kasashen Yamma na mayar da Moscow saniyar ware wajen yin tasiri, saboda kutsenta a Ukraine.

Putin ya shaida wa shugabannin Afirka a ranar Alhamis cewa zai ba su kyautar dubban ton-ton na hatsi nan da watanni masu zuwa, duk da takunkuman da Kasashen Yammasuka sanya, wadanda ya ce suna takura wa Rashan wajen fitar da hatsi da takinta.

Idan Somaliya ta ci gaba da samun nasara a sauye-sauyen, to za ta iya kai wa ga nasarar samun yafiyar basussukanta nan da karshen 2023, inda hakan zai sa bashin da ake bin ta ya ragu zuwa kusan dala miliyan 550 daga dala biliyan 5.2 ake bin ta a jumlace, kamar yadda IMF ya fada a watan Oktoban bara.

Rasha kadai tana bin Somaliya kusan dala miliyan 695 a 2019, a cewar Asusun Lamuni na Duniya.

Reuters