Daga Brian Okoth
Kudin kasar Tunisiya na Dinar shi ne mafi karfi a cikin kudaden kasashen Afirka, sai kuma na Dinar din Libiya sannan Dirham na Moroko.
Wani nazari da TRT Afrika ta yi kan yanayin musayar kudaden kasashen Afirka a kan dala a ranar Talata 25 ga watan Yulin 2023, ya nuna cewa Cedi na Ghana da Pula na Botswana su ne kudade biyar da suke kan gaba wajen karfi a nahiyar.
A wannan ranar dai, sauyin dala daya idan aka kwatanta da Dinar na Tunisiya ya kama ne a kan 3.04, yayin da dala daya ya kama Dirham din Libiya 4.77, sai Dirham din Moroko 9.79. Dala daya kuma ta kasance Cedi din Ghana 11.28.
An tattara alkaluman ne daga wani shafi da ke bin diddigin sha'anin kudi na intanet na xe.com da kuma shafin mujallar Forbes. Alkaluman kan sauya ne a kullum in da yake danganta da bangarorin da suke tasiri ga tattalin arzikin kasa.
Amma ba lallai ne a samu wani gagarumin sauyi lokaci guda ba, sai dai idan an samu wasu gagaruman ci gaba a kasa.
Kudin Rupee na kasar Seychelles ya kama (14.09 idan aka kwatanta da dala daya), Nakfa na Eritrea (15.00), Dalar Namibian (17.56), Rand din Afirka ta Kudu (17.59) da kuma Lilangeni na Eswatini (17.62) su ne sauran kudade da suka cika jerin na 10 a mafiya daraja a Afirka.
Abin da ya sa ake kwatancen da dala
TRT Afrika ta yi amfani da dala a matsayin hanyar kwatanta darajar kudaden saboda da ita ake amfani da hukumance.
Dalar Amurka ita ce kudin na farko da aka fi tu'ammali da shi a harkokin kasuwanci da tattalin arzikin duniya.
Ita ce ke da kashi 85 cikin 100 na yawan hada-hadar kasuwanci da ake yi a duniya.
Kudin Lesotho na Loti shi ne yake kan mataki na 11 a Afirka inda dala daya take daidai da Loti 17.97. Kudin Kwacha na Zambiya ne na 12, dala daya tana daidai da 19.33.
Fan din Masar 30.90 ya zama dala daya, yayin da Ouguiya na Mauritaniya 37.95 yake daidai da dala daya, sai Rupee na Mauritiniya Rupee 45.59 a dala daya.
Kudin Birr na Ethiopia ne yake kan matsayin na 16 a nahiyar inda ake musayar dala daya a kan 55.09. Dalasi na Gambiya ke bin bayansa a kan sauyin 59.60 kan dala daya, Metical Mozambican kuma a kan (63.25).
Escudo na Cape Verde ya tashi a kan (99.85) duk dala daya. Fan din Sudan ta Kudu kuma a kan 130.26 duk dala, inda ya zama na 20 a mafi karfi a Afirka.
Kudade marasa karfi
Kudin kasar Sao Tome and Principe ya fi rashin daraja a nahiyar Afirka, in da dala daya ke daidai da kudin Dobra na Sao Tome 22,823.99. Sao Tome karamar kasa ce da yawan mutanenta ba su wuce 220,000 ba.
Kudin Saliyo shi ne na biyu mafi rauni inda duk dala daya ke tashi a kan Leone 19,750. Sai kuma Franc na Guinean Franc da yake (8,604.43), Malagasy Ariary na Madagascar Ariary ya kai 4,510.69 sai kuma Shilling na Uganda da yake (3,651.68).
Sauran kasashen da suka kasance cikin jerin goman da kudadensu ba su da daraja a nahiyar sun hada da Franc na Burundi (2,831.30), Franc na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo (2,559.00) da Shilling na Tanzaniya (2,448.30) da Franc na Rwanda (1,175.09) da kuma Kwacha na Malawi (1,053.73).
Kasar Kenya da ke gabashin Afirka ce ta zo ta 22 a jerin, in da dala daya take daidai da kudinta na Shilling 142.15.
Faduwar darajar Shilling ya jawo ta da hakarkari sosai a Kenya, inda masu zanga-zanga suka zargi gwamnati da rashin tsinana abin arziki wajen kawo tsare-tsaren da za su karfafa kudin kasar.
Naira ta Nijeriya ce ta 43 a jerin kasashen Afirka inda ake sauya dala daya a kan naira 793.32.
Sai dai duk da wannan abu, har yanzu Nijeriya ce kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka, saboda ma'aunin tattalin arzikinta na GDP ya kai dala biliyan 477, in da ta wuce Masar da Afirka ta Kudu.
Ma'aunan gane darajar kudi
Abubuwa da yawa ne suke fayyace karfi da darajar kudi, ciki har da yawan bukatar da ake da ita a kasuwannin musayar kudaden kasashen waje, da yawan kudin ruwan da babban banki ke sanyawa da hauhawar farashi da kuma karuwar tattalin arzikin cikin gida na kasa.
Kazalika yawan kasuwancin da kasa ke yi da yanayin dorewar dimokuradiyyarta ma kan taka muhimmiyar rawa a wannan fanni.
Mujallar kasuwanci ta Amurka Forbes, ta ce gwamnati mai karfi da take da karfaffan tsarin mulki da tarihin samar da tsare-tsaren tattalin arziki masu karfi tana taimaka wa wajen jan hankalin masu zuba jari, lamarin da kan kara wa kudin kasar karfi da daraja.
Kudi mafi karfi, duk da cewa yana saka farashin kayan da ake shigar wa cikin kasa ya yi kasa, a hannu guda kuma yana saka farashin kayayyakin da ake fitarwa ya yi sama, lamarin da ke yi wa gasar da ake a kasuwancin kasar illa.
Kudi mara karfi a hannu guda kuma, kan sa tsadar farashin kayan da ake fitarwa daga kasa, don haka sai a samu hauhawar farashi a cikin gida, in ji Forbes.
Ga dai jerin kudaden kasashen Afirka daga kan wanda ya fi daraja zuwa kasa, idan aka kwatanta da dalar Amurka daya a kasuwancin ranar 25 ga watan Yulin 2023"
1. Dinaren Tunisiya: 3.04
2. Dinaren Libya: 4.77
3. Dirham na Moroko: 9.79
4. Cedi na Ghana: 11.28
5. Pula na Botswana: 13.06
6. Rupee na Seychelles: 14.09
7. Nakfa na Eritrea: 15.00
8. Dalar Namibian: 17.56
9. Rand na Afirka ta Kudu: 17.59
10. Lilangeni na Eswatini: 17.62
11. Loti na Lesotho: 17.97
12. Kwacha na Zambiya: 19.33
13. Fan din Masar: 30.90
14. Ouguiya na Mauritaniya: 37.95
15. Rupee na Mauritiya: 45.59
16. Birr na Ethiopia: 55.09
17. Dalasi na Gambiya: 59.60
18. Metical na Mozambic 63.25
19. Escudo na Cape Verde: 99.85
20. Fan din Sudan ta Kudu: 130.26
21. Dinaren Aljeriya: 135.09
22. Shilling na Kenya: 142.15
23. Franc na Djibouti: 178.09
24. Dalar Liberiya: 184.75
25. Dalar Zimbabwe: 361.90
26. Franc na Comoro: 445.25
27. Shilling din Somaliya: 570.77
28. Gabon (Central African Franc): 594.08
29. CFA (Sefa) ta Kamaru (Central African Franc): 594.08
30. CFA (Sefa) ta Jamhuriyar Tsakiyar Afirka
31. CFA (Sefa) ta Kamaru ta Chadi: 594.08
32. CFA (Sefa) ta Kamaru ta Congo: 594.08
33. CFA (Sefa) ta Kamaru ta Equatorial Guinea: 594.08
34. Sefar Afrika ta Yamma, West African Franc na Jamhuriyar Benin: 594.42
35. Sefar Cote D'ivoire: 594.42
36. Sefar Guinea-Bissau: 594.42
37. Sefar Senegal: 594.42
38. Sefar Niger: 594.42
39. Sefar Burkina Faso: 594.42
40. Sefar Mali: 594.42
41. Sefar Togo: 594.42
42. Fan din Sudan: 601.50
43. Nairar Nijeriya: 793.32
44. Kwanza na Angola: 827.50
45. Kwacha na Malawia: 1,053.73
46. Franc na Rwandan: 1,175.09
47. Shilling na Tanzaniya: 2,448.30
48. Franc na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo: 2,559.00
49. Franc na Burundi: 2,831.30
50. Shilling na Uganda: 3,651.68
51. Malagasy Ariary na Madagascar: 4,510.69
52. Franc na Guinea: 8,604.43
53. Leone na Saliyo: 19,750.00
54. Dobra na Sao Tome and Principe: 22,823.99