Sanarwar ta zargi kamfani Air France da yin gaban kansa wajen daina jigila zuwa kasar ba tare da ya sanar da hukumomi da kwastomominsa ba./Hoto: Reuters

Gwamnatin mulkin sojin Mali ranar Laraba ta ce dakatarwar da ta yi wa kamfanin jiragen saman Air France za ta ci gaba da aiki har sai an kammala nazari kan batun ba shi umarnin shiga kasar.

Ta bayyana haka ne kwana guda bayan Air France ya sanar da cewa zai ci gaba da zirga-zirga zuwa kasar ta Mali a ranar Juma'a mai zuwa, bayan an dakatar da shi a watan Agusta sakamakon hatsaniyar da ta barke tsakanin Nijar da Faransa bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

Wata sanarwa da Ma'aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Mali ta fitar ta ce hukumar kula da harkokin sufurin jiragen sama ta kasar “tana ci gaba da yin nazari kan bukatar Air France ta neman ci gaba da jigila zuwa kasar.”

Sai dai ta kara da cewa “kawo yanzu an haramta jigilar jiragen saman Faransa sai bayan an kammala bincike.”

Sanarwar ta zargi kamfani Air France da yin gaban kansa wajen daina jigila zuwa kasar ba tare da ya sanar da hukumomi da kwastomominsa ba.

Gwamnatin sojin ta jaddada matsayinta na "ci gaba da kare martabar kasar Mali."

Air France yana zuwa Mali sau bakwai a duk mako sannan ya je Burkina Faso sau biyar kafin a dakatar da shi ranar 7 ga watan Agusta bayan sojojin Nijar sun rufe sararin samaniyar kasarsu.

Ranar Talata, Air France ya bayyana cewa zai ci gaba da jigila zuwa Bamako babban birnin Mali daga Paris inda kowace Talata da Juma'a da kuma Lahadi zai rika zuwa kasar kai-tsaye ba tare da ya da zango a ko'ina ba ta hanyar amfani da jirgin kasar Portugal EuroAtlantic Airways.

TRT Afrika