Saudiyya ta sanar da kara wa’adin rage yawan albarkatun man da take fitarwa da ganga miliyan daya kowacce rana, a wani yunkuri na hana farashi karyewa.
Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya (SPA) ya ruwaito majiyar ma’aikatar makamashi na cewa matakin rage yawan man da ya fara aiki a watan Yuli, zai ci gaba har a watan Agusta “Za kuma a iya kara wa’adin”.
“Majiyar ta tabbatar da cewa an dauki matakin kara wa’adin ne saboda a karfafa matakan da kasashen OPEC+ suka dauka da nufin daidaita kasuwar man fetur”, in ji SPA.
Wannan mataki ya sanya adadin man da Saudiyya za ta ci gaba da fitarwa zai kasance ganga miliyan tara kowacce rana.
Akwai yiwuwar kara wa’adin
Ministan Makamashi na Saudiyya Yarima Abdulaziz bin Salman bayan wata ganawa da kasashe masu fitar da albarkatun mai suka yi, ya bayyana cewa akwai yiwuwar kara wannan wa’adi.
Matakin ya biyo bayan taron da kasashen OPEC+ suka gudanar a watan Afrilu inda suka amince da rage yawan man da suke fitarwa, kuma Saudiyya ta amince da rage yawan nata da ganga miliyan daya kowacce rana.
Kasashen da ke fitar da man na fuskantar barazanar karyewar farashinsa da kuma rashin tabbas din kasuwar man saboda rikicin da Rasha ke yi da Yukren.
Saudiyya na son amfani d akudaden man fetur din ta don cika burinta na manufar fadada tattalin arzikinta da daina dogaro kan albarkatun mai.
Rage yawan man da Rasha ke fitarwa
Manazarta sun bayyana cewa masarautar na bukatar a bar farashin mai kan dala 80 kowacce ganga ta yadda za ta iya daukar nauyin kasafin kudinta.
A ranar Litinin din na Rasha ta sanar da rage yawan man da take fitarwa da ganga dubu 500,000 a kowacce rana a watan Agusta, a wani yunkuri na ganin kasuwar man ta daidaita.
Sanarwar da mataimakin firaministan rasha mai kula da harkokin makamashi Alexander Novak ya fitar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan mayar da martanin Rasha ga takunkuman da kasashen yamma suka saka mata a wannan shekarar.
Tun bayan fara rikicin Yukren a watan Fabrairu, Rasha ta juya akalar fitar da mai zuwa Turai inda ta karkara ga Indiya da China.