Kamfanin man fetur a Nijeriya NNPC ya karyata rade-radin karin farashin kudin fetur a fadin kasar.
NNPC ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X wanda a baa ake kira Twitter bayan wasu rahotanin da ke yawo a shafukan sada zumunta cewa yana wasu sabbin shirye-shirye na karin farashin fetur da a yanzu haka ake sayarwa a kan Naira 617 zuwa Naira 720 ko 750 kan kowace lita.
''Ba mu da niyyar kara farashin man fetur kamar yadda ake yayatawa,” a cewar sawarwar NNPC a shafisa na X.
Ana rade-radin ne bayan wasu alamu daga ‘yan kasuwar man da ke nuna cewa farashin fetur zai tashi zuwa tsakanin Naira 680 zuwa Naira 720 kan ko wace lita a makonni masu zuwa idan har farashin dala ya ci gaba karuwa a kasuwanin bayan- fage, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce daga kungiyar kwadago ta kasar.
Kamfanin na NNPC dai ya bukaci 'yan Nijeriya su yi watsi da duk rahotanni da ke yawo a shafukan sada zumunta kan batun.
A halin yanzu rahotanni sun yi nuni da cewa farashin man fetur a kasar yana tsakanin Naira 570 zuwa Naira 600 kan kowace lita tun bayan cire tallafin mai da aka yi a karshen watan Mayu na 2023 a Nijeriya.