Ma'aikatan katafaren kamfanin fasaha na Koriya ta Kudu, Samsung sun soma yajin aikin gama-gari na kwana uku kan rashin biyansu albashi da alawus- alawus, a cewar shugaban kungiyar wanda ke wakiltar dubban ma'aikatan kamfanin, yana mai gargadin cewa matakin na iya yin tasiri wajen ci gaba da samar da sabbin fasahohi da sauran na'urori da kamfanin ke ƙerawa.
A ranar Litinin ne dandazon ma'aikatan suka taru a gaban harabar kamfanin a yankin birnin Hwaseong da Gyeonggi sanye da rigunan ruwa yayin da suke ɗauke da alluna suna yekuwar ''yaƙi tare cikin haɗin kai.''
Kamfanin Samsung dai na kan gaba wajen ƙera na'urori da fasahohin zamani a duniya kana yana da kaso mai yawa na manyan na'urorin da ake amfani da su a duniya.
Tun a watan Janairun da ya gabata ne mahukuntan kamfanin suka yi ta kwan gaba kwan baya da kungiyar ma'aikatan kan wata yarjejeniya inda bangarorin biyu suka gaza cimma matsaya na ƙin amincewa da ƙarin albashin kashi 5.1 da kamfanin ya gabatar.
''An soma yajin aikin ne a yau Litinin,'' in ji Son Woo-mok, shugaban kungiyar kamfanin fasahohin Samsung na ƙasa.
Ya ƙara da cewa "Yajin aikin na gama-gari na yau somin taɓi ne."
“Idan muka tuna dalilin da ya sa muka zo nan, ina mai ƙarfafa mana gwiwa cewa kar mu zo wurin aiki har sai ranar 10 ga watan Yuli, kuma ka da a amsa duk wani kira na kasuwanci,” kamar yadda Woo-mok ya shaida wa taron zanga-zangar ma’aikatan.
Kungiyar ta ce kimanin ma'aikatan kamfanin 5,200 ne suka bi sahun gudanar da zanga-zangar.
''Shin har yanzu ba sa tunanin cewa matakin hakan zai shafi ayyukansu?" a cewar mataimakin shugaban kungiyar, Lee Hyun- kuk.
'Matakin ƙarshe'
Ƙungiyar ma'aikatan wacce ke da mambobi sama da mutum 30,000 ta sanar da soma yajin aikin ne na kwanaki uku a makon jiya biyo bayan gaza samun matsaya kan yarjejeniyar biyan haƙƙokin ma'aikata da kamfanin, inda ta ce wannan mataki ne na karshe.
Matakin dai ya biyo bayan zanga-zangar kwana ɗaya da aka gudanar a watan Yuni, lamarin da ke zama irinsa na farko da aka taba ɗauka kan kamfanin, wanda ya kwashe tsawon shekaru da dama ba tare da ganin irin wannan haɗin kai ba.
''Yanzu muna cikin tsaka mai wuya,'' in ji ƙungiyar a wani sako da ta aika wa mambobinta a makon da ya gabata, inda ta bukaci su ba da goyon bayansu wajen gudanar da yajin aikin.
"Wannan yajin aikin shi ne mataki na karshe da za mu iya ɗauka," in ji shi, yana mai cewa ma'aikatan kamfanin na bukatar su hada kai.''
"Na ji dadi ƙwarai da gaske," in ji wani ɗan ƙungiyar kuma daya daga cikin masu zanga-zangar, yana mai cewa, "Mun kafa tarihi."
Ma'aikatan sun yi watsi da tayin ƙarin albashi na kashi 5.1 cikin 100 a watan Maris, inda a baya ƙungiyar ta bayyana bukatunta da suka hada da inganta lokutan hutun shekara-shekara da kuma karin kudaden alawus-alawus na ma'aikata.
Kamfanin na Samsung dai ya ƙi yarda ya ce komai kan wannan batu.
''Yayin da aka soma yajin aiki na kwana uku kacal, daga cikin mambobin da suka halarci zanga-zangar har da ma'aikatan da ke aiki a fannin ƙera na'urori,'' in ji Farfesa Kim Dae-jong na Jami'ar Sejong.
"Duba da cewa ƙungiyar na iya ɗaukar ƙarin wasu matakai na gudanar da yajin aiki idan har aka gaza samun mafita, kuma hakan na iya haifar da gagarumin haɗari ga kamfanin na Samsung a kokarin da yake yi wajen fafatawa a fagen kasuwancin fasahar zamani,'' in ji shi.