Kungiyoyin kwadagon sun toshe hanyoyin shiga filin jiragen saman Legas da ke kudancin Nijeriya, suna neman a kyautata  yanayin aikinsu tare da inganta albashinsu/Hoto TRT Afrika Hausa

Ma’aikatan sun hana motoci shiga filin jiragen sama na Mohammed Murtala da ke birnin Legas.

Mutane sun rika takawa a kafa sakamakon rashin ababen hawa/Hoto: TRT Afrika Hausa

Zanga-zangar, wadda gamayyar kungiyoyin kwadago na fannin sufurin sama ta gudanar, wani bangare ne na yajin aikin kwana biyu da suke yi.

Matafiya da ke son hawa jirage sun yi korafi kann yadda  ma'aikatan suka toshe hanyoyin da motoci ke bi zuwa filin jiragen/Hoto: TRT Afrika Hausa

Ma’aikatan sun tare kofar shiga filin jiragen saman da ke unguwar Ikeja, lamarin da ya sa matafiya suka yi ta takawa zuwa filin jiragen saman don motoci ba za su iya shiga ba.

Duk da cewa jami'an tsaron kasar sun je wurin, ma'aikatan sun ce ba za a fasa yajin aikin na kwana biyun ba/Hoto: TRT Afrika Hausa
TRT Afrika da abokan hulda