Masu zanga-zangar na neman gwamnan Babban Bankin kasar Ghana Dr Ernest Addison da mataimakansa su yi murabus da gaggawa. Hoto: Reuters

Daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a ranar Talata ta neman gwamnan Babban Bankin kasar Ghana Dr Ernest Addison da mataimakansa su yi murabus da gaggawa.

Wasu mambobin majalisar dokokin kasar na jam’iyyun adawa ne suka jagoranci zanga-zangar wacce aka yi ta sakamakon ɓatan kuɗaɗe har dala 513,000 a shekarar 2022, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Turkiyya Anadolu ya rawaito.

Masu zanga-zanga sun yi ta ihu suna cewa “A yanzu Babban Bankin Ghana ya talauce,” inda suka ce hakan ya samo asali ne saboda rashin iya tattali da ɓarna ta shugabannin bankin.

Kazalika batun shirin kashe dala miliyan 250 wajen gyara sabuwar hedikwatar babban bankin ya sake tunzura mutane, inda suke ganin hakan a matsayin rashin sanin ya kamata ganin halin matsin tattalin arziki da ƙasar ke ciki.

A yayin da masu zanga-zanga suka durfafi hedikwatar bankin don gabatar da ƙorafinsu ne aka sanar musu da cewa jami’an bankin na wata ganawa da Asusun Ba da Lamuni na Duniya, IMF.

Shugaban marasa rinjaye Cassiel Ato Forson ya sha alwashin cewa “Za mu sake dawowa.”

Ghana na fama da hauhawar farashi da tsadar rayuwa da ƙaruwar basussukan da ake bin ta.

Gwamnatin kasar ta sanya wasu matakai kamar ƙara haraji don samun ƙarin kuɗaɗen shiga da za su taimaka wajen magance matsalolin tattalin arzikin.

Ko a watan da ya gabata ma sai da matasa suka yi wata zanga-zanga ta kwana uku inda suka soki jami’an gwamnati, ciki har da Shugaba Nana Akufo-Addo, kan yadda ya gaza shawo kan matsalar tattalin arziki da ke "ta ƙaruwa" tun hawansa mulki a shakerar 2016.

Kazalika suna fushi kan alkawuran da aka "gaza cikawa" wadanda daga farko aka yi matuƙar saka rai da su.

AA