Wayoyin zamani kirar Samsung da Apple sune su ke kan gaba wajen siye a duniya a cewar sabon binciken./Photo: Reuters 

Kasuwar sayar da wayoyin zamani na ci gaba da fuskantar koma baya a duniya musamman a zangon nan mai ƙarewa cikin shekarar 2023, sakamakon irin taka tsantsan da mutane ke yi wajen saye, a cewar wani rahoto na binciken kasuwanni 'Tracker Counterpoint', ya fitar a ranar Litinin.

A bisa ƙididdigar kamfanin bincike na Counterpoint Services, an samu ragin kaso takwas cikin 100 a kasuwannin wayoyi, kuma wannan yanayin ya nuna faduwar darajar wayoyi sau tara cikin shekara daya idan aka kwatanta da sauran shekaru.

Koma bayan da aka samu a kasuwar ya biyo bayan ''rashin iya biyan buƙatun al'umma da kawo yanzu ke ci gaba da tangal-tangal,'' in ji kamfanin a cikin binciken da ya gudanar.

Sai dai alamu sun nuna cewa kasuwar watan Satumba da aka yi tare da fitowar sabuwar wayar iPhone 15 na kamfanin Apple na iya farfaɗo da faɗuwar darajar wayoyin a nan gaba, cewar binciken.

Kamfanin Samsung na kan gaba

"An yi hasashen kasuwar za ta yi ƙasa sosai a shekarar 2023 da matsayi mafi ƙaranci cikin shekaru goma musamman saboda irin sauyin tsarin maye gurbin fasahar na'urorin zamani da aka samu a kasuwannin wayoyin da suka ci gaba," in ji Counterpoint.

Katafaren kamfanin ƙirƙirar fasahohin zamani na ƙasar Koriya ta Kudu Samsung, na kan gaba wajen jagorantar kasuwannin wayoyin zamani da tazarar kaso biyar, sannan yana da kaso 20 cikin 100 a zangon nan mai ƙarewa a kasuwar.

A ɗaya ɓangaren kuma kamfanin Apple na matsayi na biyu da kaso 16 cikin 100 a kasuwar, bayan fitowar sabon samfurin wayar iPhone 15 wanda ya samu karɓuwa kawo yanzu.

TRT Afrika