Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da ƙasar Saudiyya domin kafa tsarin hadin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a fannin mai da kuma iskar gas.
Ana sa ran yarjejeniyar za ta taimaka wajen haɓaka dangantaka tsakanin kasashen biyu ta hanyar musayar bayanai da fasahohi da za su inganta hanyoyin cin moriyar juna.
Gwamnatin Nijeriya, wacce ta samu wakilcin karamin Ministan Albarkatun Man Fetur na kasar Sanata Heineken Lokpobiri, tare da gwamnatin Saudiyya karkashin jagorancin Ministan Makamashinta Yarima Abdulaziz bin Salman, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a yayin babban taron kasar da kasashen Afirka kan tattalin arziki da ke gudana a birnin Riyadh.
Tun da fari a wata sanarwa da Ministan ya fitar ranar Alhamis ya ce yarjejeniyar za ta kawo ci gaba sosai wajen ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu tare da inganta hanyoyin da za a ci moriyar juna.
“Fa'ida ta farko da ake sa rai daga wannan yarjejeniya mai muhimmanci ita ce sauƙaƙa musayar fasaha,'' in ji sanarwar.
“Duba da ci gaban Saudiya a fannin fasahar haƙo mai da iskar gas, Nijeriya za ta samu ci gaba sosai daga musayar ilimi a wannan fannin da kuma ƙara yawan albarkatun man kasar,'' a cewar Ministan.
Karanta wani labarin mai alaƙa: Saudiyya za ta ƙulla yarjejeniyar dala miliyan 500 da ƙasashen Afirka
Yarima Abdulaziz bin Salman, wanda ya sanya hannu a madadin Masarautar Saudiyya, ya bayyana kyakkyawan fata game da tasirin da yarjejeniyar haɗin gwiwar za ta haifar wajen inganta fannin makamashin ƙasashen biyu.
Kazalika Yariman ya sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi da ƙasashen Afirka ciki har da Nijeriya da Senegal da Chadi da kuma Habasha don haɗin kai a abubuwan da suka shafi makamashi.