Wani sabon rahoto da Hukumar Kididdiga ta Nijeriya (NBS) ta fitar, ya yi nuni da cewa kayyakin amfanin gona da ƙasar ta fitar zuwa wasu kasashe ya ƙaru da kashi 123 cikin 100 idan aka kwatanta da darajar kayayyakin da aka fitar a watanni huɗun karshe na shekarar 2023 (₦463.97bn).
Kazalika rahoton ya bayyana cewa an samu karin kashi 270 cikin 100 idan aka kwatanta da darajar kayayyakin a watanni huɗun farko na shekarar 2023 (₦ 279.64 biliyan).
A cewar rahoton na NBS kan ‘Kididdigar Kayayyaki da ake fitarwa zuwa kasashen waje, a watanni hudun farko na 2024 yankin Asiya ne aka fi fitar da mafi yawan amfanin noman Nijeriya a kan darajar ya kai Naira biliyan 572 sai kuma Turai da darajar kayayyakin ya kai Naira biliyan 366.
Rahoton ya kuma yi nuni da cewa an fi fitar da iri na ridi 'sesamun' a darajar da ya kai Naira biliyan 247.75 zuwa kasashen waje, da iri na ‘Superior quality Cocoa beans' wato manyan waken koko da ya kai Naira biliyan 231 sai kuma matsaikaitan waken koko da ya kai Naira biliyan 140.
Wani bincike da aka gudanar ya yi nuni da cewa an fitar da irin 'yayan ridi' da jimullar darajarsu ya kai Naira biliyan 83.29 da biliyan 58.04 zuwa kasashen China da Japan, yayin da darajar manyan iri na wake da aka fitar ya kai Naira 112 da kuma Naira biliyan 48 zuwa kasashen Netherlands da kuma Malaysia kowannensu.
Kayayyakin da aka shigo da su Nijeriya
A daya bangaren kuma, jimullar kayayyakin amfanin noma da aka shigo da su Nijeriya a watannin farko na shekarar 2024 ya kai Naira biliyan 920 ko kuma kashi 7.28 cikin 100.
ƙarin adadin ya kai kashi 29.45 idan aka kwatanta da darajar da aka samu a watanni huɗun karshe na 2023 (₦711bn) da kuma kashi 95 cikin 100 idan aka kwatanta da na watannin farko na 2023 (₦471bn).
Manyan kayayyakin noma da aka shigo da su Nijeriya a watannin farko na shekarar 2024 sun hada da alkama daga kasar Kanada da ya kai na Naira biliyan 130 sai kuma kasar Lithuania da ya kai Naira biliyan 99.
A watannin farko na shekarar 2024, kasar China ita ce ke kan gaba a cikin manyan abokan cinikayyar Nijeriya a bangaren shigo da kayayyaki, sai Indiya da Amurka da Belgium da kuma Netherlands.
Kayayyakin da aka fi shigowa da su sun hada man fetur na kananan Motoci da Man iskar Gas da Alkama da rake da kamfanonin sarafa sugari suke amfani da kuma sinadaren hydrocarbons da dai sauransu.