TotalEnergies ya karyata zarge-zargen da ake yi masa kan sakaci da kisan kai, yana mai cewa hakan  "ba daidai ba ne.  / Hoto: Reuters      

Wasu daga cikin mutanen da suka tsira da kuma ‘yan uwan wadanda harin ‘yan ta'adda ya rutsa da su a shekarar 2021 a kasar Mozambique, sun maka kamfanin iskar gas naTotalEnergies a kotu, bisa sakaci da kuma kisan kai, suna masu cewa kamfanin ya gaza wajen samar da tsaro ga ƴan kwangilar da ya dauka aiki.

TotalEnergies ya yi watsi da zarge-zargen, yana mai cewa hakan "ba daidai ba ne."

A watan Maris na shekarar 2021 ne wasu ƴan ta'adda suka kai hari tashar jiragen ruwa da ke birnin Palma inda suka kashe fararen hula da dama a yankunan kusa da inda ake gudanar da ayyukan samar da albarkatun iskar gas LNG mallakin kamfanin TotalEnergies a Mozambique.

Wadanda suka shigar da ƙarar- daga ciki akwai mutum uku da suka tsira da kuma 'yan uwan hudu daga cikin wadanda suka mutu a harin kwanton ɓauna da aka kai musu - sun yi zargin cewa kamfanin TotalEnergies ya gaza sanar da 'yan kwangilar hadarin yiwuwar kai hare-hare wurin, sannan ya gaza wajen samar musu ingantaccen tsaro.

A karar da aka shigar an yi zargin cewa wani jirgi mai saukar ungulu da aka tura ya kwashe mutanen da suka musu mafaka a wani Otel bai zo ya dauke su ba saboda rashin mai a cikin jirgin, kuma kamfanin TotalEnergies ya ƙi amincewa da bukatar samar da man saboda rashin son hada wata alaƙa da wani kamfani mai zaman kansa.

Kwanton ɓauna kan wasu ayarin motoci

Wasu masu aikin kwangilar sun yi kokarin tserewa daga otal din da ayarin motoci, inda aka yi musu kwanton ɓauna, kuma aka kashe da dama daga cikinsu, in ji masu shigar da ƙara.

"Ba ƙamarin abu ba ne a tuhumi wani kamfani tare da gurfanar da shi kan laifin kisan gilla kai tsaye ... an samu sakaci mai yawa da suka ba da gudummawa ga yanayin asarar rayuka da aka samu da dama," a cewar Henri Thulliez, lauyan da ke wakiltar. masu ƙarar.

"It is not alleged that TotalEnergies directly caused the deaths of victims but that the company did not act in accordance with the expected diligence standards of a professional in its responsibilities," lawyers for the plaintiffs said in a statement.

“Ba wai ana zargin cewa kamfanin TotalEnergies ne ya yi sanadiyar mutuwar wadanda abin ya shafa kai tsaye ba ne, amma kamfanin bai dauki matakan da suka dace ba musamman wajen samar da tsaro,'' a cewar sanarwar da lauyoyin masu ƙarar suka fitar.

A nasa ɓangaren, TotalEnergies ya musanta zargin, yana mai cewa yana da tsarin tsaro kuma ta aiwatar da shi a lokacin.

'An kwashe 'yan kwangilar'

"A lokacin harin da aka kai birnin Palma, da kuma bayanan da muke samu, an kwashe dukkan ma'aikatan LNG na Mozambique da 'yan kwangilar da ke aiki a wajen,'' a cewar kamfanin na TotalEnergies.

Kamfanin ya ce tsarin tsaron da aka ware wa 'yan kwagillar rukunin LNG da ke Mozambique shi ne samar musu matsugunai da kuma kwashe su da jiragen ruwa.

A yanzu haka dai kamfanin ya ce an samu saukin matsalar tsaro a yankin, kuma yana kan kammala shirye-shiryen sake fara aikin kafin karshen wannan shekara.

TRT Afrika