Ma'aikatar man fetur ta kasar Masar ta kaddamar da sabon shirin hako mai ranar Litinin a wani mataki na gudanar da bincike a wasu wurare 23 da aka gano shi.
An sanya ranar 25 ga watan Fabrairu na shekara mai zuwa a matsayin wa'adin karshen na aikin binciken.
Aikin ya hada yankuna 10 da ke hamadar Yamma ta Masar, biyu a yankin hamadar gabas sai bakwai a gabar tekun Suez da kuma hudu a yankin tekun Bahar Maliya, a cewar Ma'aikatar
Masar wacce ke da mafi yawan al'umma a yankin kasashen Larabawa, na neman mayar da kanta a matsayin cibiyar makamashi ta yankunan.
A watan da ya gabata ne ma'aikatar albarkatun man fetur ta kasar ta sanar da gano wani sabon wuraren hako mai a yankin Geisum da Tawila West Concession a mashigin tekun Suez.
Adadin Mai da ake samu
Kamfanin Cheiron na kasar Masar ne ya gano sabbin wuraren a aikin binciken rijiyar GNN-11 wanda a yanzu yake samar da gangan mai sama da 2,500 a rana, a cewar Ma'aikatar.
Ma’aikatar ta ce rijiyar ita ce ta hudu da aka kammala aikin hako ta sannan ana kan aikin hako wasu rijiyoyi uku da ke cikin jerin shirin binciken da za a yi a yanzu, in ji Ma'aikatar.
Jimillar mai da ake fitarwa daga rijiyar da ke Arewacin Geisum, ya kai kusan ganga 23,000 a kowace rana, a cewar Ma'aikatar.
Yawan makamashin da Masar ke fitarwa dai yana dada karuwa a 'yan shekarun da suka gabata.
Kasar ta fitar da kyubik Mita biliyan 8.9 (bcm) na iskar gas (LNG) a shekarar 2021 da kuma 4.7 bcm a watanni biyar na farkon shekarar 2022, a cewar wasu bayanai da Refinitiv Eikon ya tattaro.