“Muna da burin zuba jari, musamman a fannin muhimman ma’adanai,” kamar yadda Mr Scholz ya shaida wa Tinubu a Abuja. Hoto: State House

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz said ya ce kasarsa na son saka jari a fannin iskar gas da ma’adanai masu muhimmanci sosai na Nijeriya, kasar da ta fi kowacce arzikin fitar da man fetur a Afirka.

Mr Scholz ya fadi hakan ne a ranar Lahadi a yayin wani taron manema labarai da yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wata ziyarar kwana biyu da yake yi a yankin Kudu da Hamadar Sahara ta Afirka.

Wannan ne karo na uku da Mr Scholz ke ziyartar yankin a cikin shekara biyu, a yayin da rikici a wani wajen yake nuna karuwar muhimmancin yankin da ke da arzikin fetur, lamarin da Jamus ba ta da wani tasiri sosai a kai.

“Muna da burin zuba jari, musamman a fannin muhimman ma’adanai,” kamar yadda Mr Scholz ya shaida wa Tinubu a Abuja, babban birnin Nijeriyar.

A kan batun gas kuwa, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa shugaban na Jamus ya yi maraba da kokarin Nijeriya na fadada tsarin yawan samar da iskar gas dinta.

“Idan har muka yi nasara, idan har muka samu dama mafi kyau ta fitar da iskar gas … to zai zama ya rage ga kamfanonin Jamus kuma su yi kasuwancin a ƙashin kansu,” a cewar Scholz.

A nasa jawabin, Shugaban Nijeriya Tinubu cewa ya yi “ya yi wata tattaunawa mai zurfi” a kan batun iskar gas tare da ƙara wa ‘yan kasuwan Jamus ƙwarin gwiwar saka jari a fannin gas a Nijeriya.

Kazalika Nijeriya na son jawo hankalin masu zuba jari a fannin ma’adananta, wanda ya dade ba ya samun ci gaba, kuma yana taimakawa ma’aunin tattalin arzikin kasar da kashi 1%.

Mr Scholz wanda bai fayyace komai duka ba, ya ce kamfanonin Jamus suna kuma da niyyar gina layin dogo na jirgin kasa a Nijeriya.

A yanzu haka kamfanonin China ne suka yi bake-bake a fannin, inda suka samu manyan kwangilolin fadada layukan dogo a ƙƙsar, wacce ta fi kowacce ƙarfin tattalin arziki a Afirka.

Scholz ya kuma gana da shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, yana mai cewa dole ne ƙasarsa ta yi aiki da ƙungiyar “don hana juyin mulki zama ruwan dare” bayan waɗanda aka yi a Nijar da Gabon.

Reuters