Sassan kasar Ghana da dama ne yake cikin duhu saboda karancin iskar gas. Hoto: Reuters

Sassan kasar Ghana da dama ne yake cikin duhu saboda karancin iskar gas da ake amfani da ita wajen samar da wutar lantarki a fadin kasar.

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Ghana (GRIDCo) ya ce matsalar ta jawo gibin wutar da ta kai “MegaWatt 550 a lokacin da aka fi bukatarta” a tashar wuta ta Tema wacce ke kusa da babban birnin kasar Accra, kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Alhamis.

Ko da yake sanarwar ba ta bayyana dalilin da ya jawo karancin iskar gas din ba, ko kuma lokacin da za a kwashe kafin warware matsalar ba, amma kamfanin ya nemi gafarar jama’a.

An fara fuskantar matsalar wutar ne a yammacin ranar Alhamis a bangare guda kuma da ma Ghana tana fuskantar matsin tattalin arziki wanda aka dade ba a ga irinsa ba.

Wani nazari da aka fitar a watan Yuni ya ce adadin wutar lantarkin da kasar take samarwa ya yi “kadan kuma kasar ta kama hanyar fada wa matsalar wutar lantarki”.

Har ila yau a watan Yulin bana kamfanonin samar da wutar lantarki masu zaman kansu a kasar sun yi barazanar dakatar da aikace-aikacensu saboda bashin da suke bin Kamfanin Wutar Lantarki na Ghana.

TRT Afrika