Shugaban kamfanin TotalEnergies da ministan mai na Iraki suka saka hannu a yarjejeniyar. Hoto/Reuters

Iraki da babban kamfanin makamashin kasar Faransa TotalEnergies sun saka hannu kan kan yarjejeniyar da aka dade ana jira ta dala biliyan 17.

Ana sa ran yarjejeniyar za ta habaka fetur din da ake samarwa a kasar da kuma habaka karfin da kasar take da shi na samar da wuta da ayyukan fetur da gas da makamashi masu sabunta kansu guda hudu.

Tun da farko an saka hannu kan yarjejeniyar a 2021, inda aka soma zuba jari da dala biliyan 10 a kudancin Iraki sai dai an samu jinkiri sakamakon rashin jituwa tsakanin ‘yan siyasar Iraki kan batun yanayin yarjejeniyar.

Shugaban TotalEnergies Patrick Pouyanne ya saka hannu kan yarjejeniya da ministan fetur na Iraki, Hayan Abdel-Ghani a wani taro a Bagadaza a ranar Litinin, inda Pouyanne ya ce rana ce ta “tarihi”.

An karkare yarjejeniyar a watan Afrilu, a lokacin da Iraki ta amince da daukar karamin kaso wanda bai kai wanda ta nema a baya ba na kashi 30 cikin 100, inda TotalEnergies ya dauki kaso 45 sai kuma kamfanin QatarEnergy ya dauki sauran kaso 25.

Shirin na makamashi mai suna Gas Growth Integrated Project na da burin habaka wutar lantarkin kasar, da kuma farfado da iskar gas din da ke kone a rijiyoyin mai uku domin tura su ga tashoshin lantarkin.

Kamfanin TotalEnergies ya ce zai samar da tashar wutar lantarki mai amfani da hasken rana da za ta samar da GW 1 ga tashar lantarki ta Basra, inda kuma ya bukaci kamfanin lantarki na Saudiyya ACWA da ya shiga shirin.

TRT Afrika